← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 286

Sashe 66

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

na bita dakinta bayan sallah magariba na sameta zaune a kasa saman sallaya ta hade jikinta da gado tana jan tasbaha a hannun ta. Sallama nayi na shiga ta dago kai ta kalleni gaida ita nayi ina zama nace wai ummah anyi wani abune dazun da ku fitan. Don tun dawowan ku naga yanayin ki ba dadi haka na kura mata ido ina son jin amsan da zata bani lokacin don na gama fahintar cewa akwai matsala. Maamah na fada maki kada ki fada tarkon soyayya a yanzu kada ki biyewa su Aisha don ba daya kike dasu ba yanzu gashi zancen yaron nan da ake ganin ku tare har yakai gaban Alh ko . Wani yaro ummah na tambaya cikin rudewa dama kuma fahintar cewa bakin cikin da ummah ke ciki ashe ta dalilina ne hakan ya faru. Kasa na sauko inda take don dama a saman godo na zauna sai gani na zube kasa gaban ummah sallaman da akayine yasa batace dani komai ba nima din ban samu fadin komai ga ummah din ba. Ummah ta mike ta fito zuwa falo wasu makwabtan mune da take abin arziki dasu suka shigo lokacin gaida ita da Sallah. Sun dade tare hakan yasa na koma dakina na kwanta jiki a mace don abinda ummah ta fada min na shiga tashin hankali. Abinka ga wauta irin nawa wai Ahmed din nayi niyar kira in fada mai ko zan samu shawara a wurin shi don sam ban yarda in magana gidan mu da Hannatu kawata ba. Saidana danna kiran nakuma ga rashin dacewa hakan na kashe saidai kiran ya shiga sai gashi ya kirani dole na dauka yake fadin zarah yau lafiya kuwa naga flashing din ki a wayana ? Sorry bakai naje kira ba saina danna sunan ka na samu kaina da fadin hakan gareshi murmushi naji yayi kafin tace duk dadin naman sallah da kike cine yakai ki ga hakan ina mama ina kannen mu. Duk suna lafiya na fada a kasalance lokacin yace a gaida min su saina kawo masu goron sallah su da sauri na tare shi da fadin no ka barshi don Allah. Cikin mamakin jin hakan yace lafiya kuwa kikace min hakan ina mungama wanan maganan dake ko raina abinda zan basu kikayi ? No ba hakana bane akwai abinda yasa nace hakan kasan Abban mu na gari ba fita mukeyi ba koda kazo din koda nazo ai ba tsayawa zanyi ba don ina son zuwa in gaida mama da sallah . Na sake fadin don Allah kayi hakkuri kada kazo don yanzu haka case akeyi da ummah din mu saboda wani abu so kada kazo gidan mu don Allah. Abinda ya fada ya daure min kai don cewa yayi saboda nine ko zarah an fadawa mahaifin ku kina kulani dama nasan da wana ranan yana tafe komai dadewa. Amma tunda kince kada nazo din na fasa zuwa ni kaina nasan baki cancanci mu,amula da mutum irin naba mara galihu da asali na kwarai. Kiyi hakkuri shiga rayuwan ku yaja maku matsala har ummah da bata taba sanina ba na jawo mata matsala a rayuwan ta nace ba yadda kake zato bane kawai dai an samu wanda ya fadawa Abba zancen kane na karya. Murmushi naji yayi yana fadin nasan za ai hakan zasu dauka soyayya muke dake zarah har shakuwa ya shiga tsakanina dake hakan. Abinda na guda ke nan garemu tun farko nake ta kaucewa hakan kada azo a yiwa mu,amulana dake wani fahinta na daban gashi kaddara ya riga fata har an samu wanda ya tsegunta hakan. Ko kudinshi ya kare a lokacin ko kuma dai shidin ya kashe naji wayan ya katse lokaci guda duba wayan nayi na aje ina gyara kwanciya don lokacin gaba daya jikina ya mutu sosai da maganganunshi da mukayi ga na ummah kuma da ban san me zata fada ba a kan hakan. Tun ina dakon ummah ta sallami bakin nata har barci ya daukeni ban sani ba a haka har gari ya waye bamu samu zama da ummah din ba kan case din. Saidai na kasa sukuni da sakewa a gidan don haka na zauna dakina ina jiran tsamani har barci ya daukeni can cikin barcin nake jin muryan ummah na kiran sunana na bude idanuna. Tana tsaye a kaina take fadin kinsan kuwa karfe nawa yanzun baki je kin gaida mutane har Abba ku yakai ga tambayan ki yanzu . Jin hakan yasa na sauko a gurguje saman gadon ban daki na shiga na watsa ruwa na fito na shirya ba wani kwalliya nayi ba sai idan nadawo zan zauna in gyara kaina. Part din mama na fara zuwa su Aishane a falo suna breakfast na gaidasu da kwana ta hanyar fadin ina kwana ku nasan da wuya su amsa min da dadin rai don haka na hada da fadin mama fa? Tana ciki kwance Rukkaiya ta bani amsa nace idan ta tashi na shigo na fice zuwa part din mommy amaryan Abba don wanan zuwan ta gyara part din ta daga kano masu hada wuri sukazo kwana biyu suna aikin gyaran wurin nata . Nasan ranan da sukazo ummah ta turamu muje mu gaida ita da zuwa kashe gari kuma sallah kowa yana hidimar shi ban samu zuwa ba can saida ta shigo gida ummah da sallah muka gaisa a part din mu da ita. Sai yanzun da zan shiga saida nayi sallama nasa kai na shiga ban sameta ba sai wanan matar da sukazo tare da naji tana kira da Altine. Nagaida ita na fito ina fadin in ta fito a fada mata cewa nazo tana ciki na fita na nufi part din Abban mu yana zaune saman daning yana karyawa lokacin nayi sallama na shiga. Bayan nakai wurin shi nakai gurfane kasa ina gaidashi da kwana ya amsa min yadda ya saba amsawa saidai ba wani wasan ko zancen daya biyo bayan haka din. Na danyi jim na dago zan fice har nayi tako biyu naji ya ambaci sunana na amsa na dawo na tsunguna gaban shi ina fadin na,am Abba . Bai dago ba na dan lokaci sai can ya dago yana fadin wani yarone ke zuwa wurin ki maamah kuma shi din dan gidan waye a garin nan ina kuma kika hadu dashi ? Cikin mamaki na dubi Abban din kafin nace yake zuwa wurina Abba ni ba wanda ya taba zuwa wurina wallahi Abba. Murmushin takaici naga ya baiya a fuskanshi lokaci guda kafin yace kinsan banson karya kuma maimuna ba zatayi maki karya ba tunda tace da idonta ta ganki dashi gidan nan ? Ahmed ne Abba kuma ba wani abu bane ya kawoshi lokacin sai takardun shi dayazo amsa a lokacin wurin shi kawai na sani. Shi din dan gidan waye a garin nan kuma wani sana,a yakeyi dashi da mahaifin shi wani mataki yake ga karatun shi yanzu ? Duk wanan tambayab Abbane ya jero min su lokaci guda na kara dago kai a gigice ina fadin Abba bansan komai ba kanshi abinda na sani shine kawai yana koya muna karatu mu goma idan muna free wanan kadai na sani game dashi. Kallon mamaki Abba yai min wanda ke nuna rashin yarda dani lokacin ya kalloni da kyau yana fadin ki turo min shi kafin na koma cikin satin nan. A tsorace na dago kaina nace wallahi Abba ba abinda kake tunane bane a tsakanina dashi tashi ki ban wuri ki tabbarar da kin turo min shi kafin na koma idan ba haka ba zamu saka kafan wando dake gidan nan ki tashi ki ban wuri.. Na mika da kuka zan fita muka hade da hjy karima wace ke shigowa tana fadin a maamah ance kinzo gaidani ina wanka sai kuma tayi shiru ta bini da kallo. Me kuma ya farune ta riko hannuna tana tambayana na kasa budan baki in bata amsa sai sautin kukan dana kara a lokacin. Kallon Abba din tayi tana fadin Alh meya sameta ne take kuka haka wani abu ya farune kuma da ita kodai wancan maganan ne kake har yanzu din ? Bai bata amsa ba sai kallon shi da takeyi saketa ra fice min daga falona sakariya kawai mara hankali ya fada daga inda yake zaune. Jin hakan yasa ta sakeni tana fadin jeki part din ku zanzo in sameki can muyi magana ta fada tana bina da kallo na fice daga falon na barsu da Abba.
Chapter 66 · 0% Book details