← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 273 OF 286

Sashe 273

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ina son komawa wurinsu ummah na kai masu abincin dare a asibitin. Wanka nayi na fito na samu har lokacin yana dakin shi bai fito ba sai yaran dake manne da dije don sun saba da ita sosai binshi nayi in lekashi na sameshi yayi wanka ya saka jallabiya ya koma ya kwanta rigingine saman gado yana tunane. Jin shigowana yasa ya dago ya kalleni nace aina dauka barci kakeyi bayan la,asar din nan yace No ina nan dai ina tunanen duniya wai zancen inna da Asma yace kwarai kuwa. To ai kallo daya zakaiwa Asmau yanzu kasan cewa ta canza ga yadda muka barta a baya sosai don na hango tsaban rashin kunya yanzu a idanunta sosai yasa har na fara tunanen anya barinta da Dije ba matsala bane kuwa ? Ashe kin fahinci abinda nakewa ke nan nima tunanen da nakeyi ke nan don ba zan barta da ita a gidan nan ba su kashe min ita idan kuma nace zan barta a nan karshe zakiga duk sun kwaso sun dawo nan din sun tare min a gida. Zahra ba zan boye maki ba tun farko na tsani wanan yarinyar mara mutunci da rashin ta ido don bata da kunya ko kadan shiyasa nake daure masu lokacin kina ganin laifina kan hakan. Ba laifin ka nake gani ance idan hannu ya rube baka yakeshi don sun zama hakan ai ba zaka iya rabasu da kai ba ni kuma tsakanina daku gyarane a tsakanin ku ba batawa ba. Zan bata zabi biyu kafin a gama gyarawa Dije tsohon part din mu ta zauna ciki ita da Aisha kafinta gama karatun itama tayi aure idan taki ko daya sai dai ta koma gidan ubanta ta zauna. Idan kayi tsauri da yawa kuma zakayi laifi a wurin inna gaskiya don haka ka bisu a sannu ba irin su inna ake bi a sannu ba zahra don ma ina haka din da itace yasa abubuwan suke dan min sauki. Don da ban daure fuskana a kansu abinda yafi haka yawa ta mace zuwana na karshe a wurin su da nayiwa mijinta noman doya saida muka gama wahala an fara cire amfanin gona. Rana daya haka kawai na dawo gidan na samu yana bala,i waina koma gida shiya gaji da ciyar da dan daba nasa ba har makwabta a lokacin saida suka shigo suna bashi hakkuri amma haka mutumin nan ya rufe ido yayi min tonon asiri nida ita a garin mutane. Wani ya fada mai awurin cewa wani kasan yaron nan shine karfin aikinka bana don baka taba noma irin haka ba yace ai Allah ne ya bashi bani ba haka mutanen nan suka harharda min abin arziki. Allah ya taimakeni kuma can mutum na dan aiyukansa yana samun kudi ina da dan kudin motana a aljihuna shina kulla washe gari na kamo hanya ni kadai na dawo gida tun lokacin ban kara komawa wurin su ba har suka dawo nan din. Don me ni kuma a yanzu zan rike masa yaransa ba dole dani dasu don haka zan takawa kowa burki a tsanake zanyi komai kafin na bar kasan nan insha Allahu. Ai don inna kayi komai badon shi ba haka kuma su din kannen kane kun hada nono dasu basu da wani wanda yafika yanzu a duniyan nan koda kuwa baka dashi ba zasu wuce zancenka ba don kaine dai nasu da zasuyi tunkaho dakai a fadin garin kaf don ka hada uwa dasu. Shiru yayi zuwa lokacin idanunsa sun kade sunyi jawurin Amir ya shigo yana kuka hakan yasashi tashi ya fita don ya tambayi meya sameshi ya shigo da kuka lokacin na samu daman gyara masa dakinsa har bandakin na wanko na gyaro ko ina na dakin na fito. Mamace zaune gaban mai magani tana hawaye tana fadin gaba daya yarana sin lalace min ban gane kansu ba mazan sun barkace haka matan masu aure duk nike dauke da laluransu yanzu. Daga mai auren dangiya sai mai auren barawo don har gidan kaso an kaishi kan rikici dole hankalina ya tashi da wanan bala,in da aka sako min an barkata min kan dakina lokaci guda haka. Yau kuma sai inga diyar abokiyar zamana tazo min da suran da nake mafalkin inga yayana sun kai itace ta zama tauraruwan gidan mu har tana iya daukan nauyin kowa a gidan yanzu. Ki duba kiga yadda musa ya koma min dukiyan da mahaifinsu ya danka mai ya salwantar dashi ya koma yana rokon dari dari biyu don yasha sigari sai ta kara fashewa da kuka. Hjy maimuna ki saurareni da kyau idan kin mantane in tuna maki tun farko na fada maki ki barta da yarta don wanan matar bata kallon kowa da sheri idan muyi mata a lokacin zai iya dawowa kanki. Kikace abi ko wani hanyane a dai kuntata mata yanzu sakamakon ki kike girba hanya dayace shine ki gyara zuciyar ki da kowa kamar yadda har yanzu gata nan da zuciya daya take zaune dake da yayan ki. Ban taba ganin takai ki ko danki wurin wani boka ko malam don ai maku sheri ba idan kuma baki yarda da zancena ba zaki iya zuwa gaba kiji. Saidai idan kawai meshi yana son cin kudin ki to zai iya ce maki wani abu akasin hakan don kawai ya bambari kudi a hannun ku yanzu amma amsa dayace sherin kine yake bin ki a yanzu hjy. A karshe ta bata wai abinda za a bawa yaran na tsari dana samun daukaka duk da abinda aka fada mata bata yarda da hakan ba saida ta karbo kayansu ta shigo mota suka dawo gida tana masu bayanin yadda zasuyi amfani dashi.
Chapter 273 · 0% Book details