Sashe 254
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dije ce ke zaune saman kujera mai zaman mutum daya sai ni kuma da nake zaune din na ishishire kafata don inji dadin zama a lokacin ga diyan icce tatacce a hannuna ina sha a hankali. Amma yanzu ina ganin kin rage shaka abin naki ko dijece ke min wanan tambayan don sai mu zauna ba hira don ni din ba gwana bace a wurin hira hakana muna dai dan tabawa wani lokaci. Duk da dije din ma bawai tana shiga mutane bane sosai kuma wai tayi irin tsufan nan na sosai bane don innace yarta ta fari shi kuma Ahmed jikanta na farko so batayi irin tsufan gigicewa din nan ba a yanzu. Illa kafa dake damun ta da rashin gata yasata dan mokade a yanzu kuma da take cikin hutu ta dan fara dawowa hayacinta don tana dan murmurewa saboda abincin da take samu yanzu duk da wani bata iya cinsa sosai tunda bata saba dashi ba. Haka yasa nake dagewa ina dan sarafa shinkafa irin namu na gida da muka saba dashi don ita na neme hanyan tuka tuwo a can ba ita kadai ba harshi yana ci sosai sai shimkafa da miya da nakan muna ban damu da nayi abincin su na can ba. Don haka a fannin dije kan nagama kamota sosai don na saye zuciyar dijen fiye da tsamanin ki mai karatu tun a gida na kafa gwaunatina a zuciyanta uwa uba kuma zuwan mu wanan kasan yanzu. Saura inna da wasu yan uwa nasa dake min kallon mai wayau a cikin su don su a daukansu wayau kawai nakewa Ahmed a zaman mu dashi tunda suna ganin ni idona ya bude ko. Basu san zaman miji da mata ba sai Allah a tsakaninsu sai kuma hakkuru duk yadda zance in masa ma wayau Ahmed ya darani in dai dabaran karban kudine a hannunsa abinda basu gane ba ke nan su. Don shi ya bude idone da neman kudinshi na zufan shi don haka zaiyi wuya a iya karban kudi haka hannunshi wasan dadi shine su kuma basu gane ba suke kallon nice mai hanawa. Kallonta nayi ina murmushi kafin nace da ita gaskiya yanzu na rage tun bayan zuwan mu nan amma dai ai ina dan shakawa akai akai don dama ance sai cikina ya tsufa sosai zan daina. Waya fada maki hakan ta tambayeni cikin kureni da idanu tana son ji na danyi murmushi nace a nadai fada maki haka sukace dani tace ni nasan ba banza ba kan wanan abin dole mutanen kankine ke sakaki hakan don wanan abin karfi gareshi sosai. Ni dai ina ganin mutanen ku dayane da mijinki don shima tun yana yaro haka yake mu,amula da tumfafiya nakan rasa inda yake debowa kona kwashe na zubar gobema zai samo ya aje min a daki. Ke har wanan ganyen nasa dake fadowa kasa da kansa Amadi daukowa yake ya kawo min daki idan na zubar kuma ya kama jinini ke nan na zubar masa da abu ranan har yajin cin abinci yake min don wanan abin. Shiyasa a karshe nama daina zubarwa yadda ya kawo haka nake tara masa kayansa a gefe sai ya gaji shida kansa yake zubarwa sai gashi a karshe iccen ma ya fito a cikin gidan mu karewa ke nan. Kullun fada yake zakiga ya duka yana tsince duk wani abu dayaga an zubar a wurin iccen yanzu kuma gakike da naki saddabarun tumfafiyan . Allah yasa dai kardan cikin naki ya gado ku din dan gado yafi nagada riko haka nake kallon wanan lamarin tafe maku. Dije kina nufin abinda ke cikina zai iya hakan shima tace waya san gaibu yar nan Allah dai ya sauwaka amma ni lamarin mijinki kan nasan komai tsarawan ubangijine a kansa gaskiya. Shiyasa ban faye yarda zuciyana ta amincewa wai mabiya ke gareshi ba yadda mutane ke fadi kansa don rashin mu,amulanshi da mutane. Don kinga yadda yake din nan fari ga kyau sai dora mai aljannace ta aure shi don da har ina jin tsoron hakan amma tunda ya aureki har kuka zauna lafiya yanzu har ga ciki . Hankalina ya kwanta sosai wallahi amma a lokacin da naga har shekara biyu da yan kai baki da komai gaskiya ban fada bane amma hankalina ba a kwance yake ba gaskiya. Shiru nayi ina nazarin maganan ta kafin can ince wai yau me zamucine a gidan dije ta juyo tana fadin ni yar gata ai yau inda tasone ta gida zamu tuna muci shimkafa da mai da yaji. Lokacin na tuna da akwai yaji ai danazo dashi wanda ummah ta bani idan na haihu wai nayi amfani dashi ni yaji bai dameni ba amma don kawai kada na aje na saka a cikkn kayan tafiyana gashi kuma zai mun amfani yanzu. Waken su bai kai namu dadi ba a baki amma nasan idan na hadashi itin namu hadin zaiyi dadi don haka na mike kawai na shiga kitchen na dora muna girki. Shimkafa da waken na dafa sai ganyen kabejin dana yanka na soya mai da albasa da kamshin shi ya karade easthed din namu har saida makwabta suka shigo tambaya me muka dafa haka ke kamshi ? A lokacin na hada muna a tire don in munci tare da dije din nafi cin abinci sosai in koshi ido matar ta sauke ga abincin tana binshi da kallo na nuna mata. Ta dan debi cibi daya dan kadan takai bakinta tana wani taunawa a yangance sai naga ta kara turmuza cibi wanan karon da yawa ta dibo takai bakinta. Munci sosai muna hira yayin da shima ya dawo ya zauna yaci yana ta saka min albarka ni dai ina murmushi kawai don jin dadin yadda suka yaba da girkina din basu ba gashi har makwabta mutum uku suka karba na koya masu yadda akeyinsa kuma. Ko wani rana likita yace mu koma muna zuwa a ranan su dubani haka kuma sun tabbatar min abin cikin cikina lafiya kalau yake kwance kuma yana samun abincin da yake gina jiki. Har watan haihuwana ya kama lokacin na gama fita a zahra na don nauyin cikin da yai min yawa sosai amma haka master ke ban kwarin gwiwa akan cikin yai min kyau sosai na daure na dinga ciki akoda yaushe don Allah har na haifa mai sha biyu. Na kan kalleshi ince oh don na tsofe da sauri kaiko lokacin kaji dadin dauko yar yarinya kuna sheke ayan ku ina kallo yakan yi murmushi kawai bai ban amsa saidai yayi dariya ya fita. Har ranan mukai haka gaban dije budan bakinta sai cewa tayi aiko daya zamo butulun duniya duk wanan harcin da kike masa yace zai dauko wata ya juya maki baya don ya kara aure. Auren me zan kara kuma dije ku din nan ku biyu ku isheni a rayuwata don baku rageni da komai ba da har zanji wani sha,awan kara aure nan gaba kuma. Kai dai kada kayi alkawarin hakan don maza baku da tabbas nan zakazo kana muna dadin bakin ku na maza kana fadin dije kibata hakkuri ta barni in kara. Baki na turo ina fadin ni ina ruwana ni zanfiso ma ka kara yanzu basai lokacin dana fara ragwabewa ba lokacin da karfina ya kare in dinga ganin takaici a idona. Duk yadda kika koma nan gaba haka nake son abina haka kuma zan zauna dake a cikin kauna don kin wadatar dani da komai a rayuwata. Namiji ke nan na fada ina mikewa saboda fitsarin dake damuna a lokacin na barsu a wurin sai dai a zuciyana tunane nakeyi duk wanan cika bakin na yanzu ne dubama da tun bamu kai ko ina ba amma inna na burin taga ya kara aure. Don hakane ban matsawa rayuwata cewa ba zai kara min kishiya ba don ko banza na taso a gidan mu naga uwata da kishiya don haka nima kuma matar musulmice kuma ba haushe ba zan debe raina ga kara kishiya ba nan gaba ko kusa. Ga yan arewan mu dasun rike dan canji sunji aljihunsu da nauyi ba abinda ke zuwa masu farko sai karin iyali sai a manta da duk kokarin na gida idan ma ba a dace ba keta gida kinkai zuciya nisa ba. Kece a karshe zaki koma abokiyar gaba ga mijin da amaryansa don zasu koma su hade maki kai sai diyan kine zasusan damuwanki da bukatanki saboda kin zama tamoji. Watan haihuwana ya kama kullun mahaifinsa na kira ya tambayi lafiyata dana dije don itama tana ganin likita a nan din tun zuwan mu master ya kaita asibiti ana dubata. Har Allah ya saukeni lafiya na samu baby girl fara sol da ita tun a asibitin mukayi posting din haihuwan wai ashe duk wanan abin mama da yaranta basu san cewa ina da ciki ba kuma ummah bata fadamasu ba. Ta yayama zata fada masu mutanen dako sunana basuso a kira a gabansu tun bayan tafiyana tsanar mama ya karu a kaina. Aishace ta fara gani tana duban status taga na saka Alhamdullahi Allah ya saukeni lafiya ga baby ku kuyi mata addua inganttace saboda Allah. What ta fada da karfi hannu na rawa tayi zooming ta kara kallon photo da kyau ga nurse din turawa a kaina su biyu suna dariya daga gefena. Zahra zahra ta fada sau biyu kafin ta danna kira layin mama tana dauka tace mama wai dama zahra ciki garetane har ta haihu bamu sani ba ? Zahra wace zahra ke nan zahran mu mana mama zahra dai ta gidan mu yanzun naga tayi posting a waya ta haihu kuma a asiniti na ganta tare da nurse balle nace karyane. Zahra ta haihu fa kikace dama cikine da zahran tunkan ta bar kasan nan ashe au kema mama baki sani ba ashe ? Wallahi ban taba jin hakan ba ko a bakin Alh kuwa in kuma ya sani bai fada min ba sun munafunceni ke nan shida salma suna daukata muguwa ko me ? Mama ki dai binciki Abba ko ya sani wata kila shima bai sani ba fa kai amma salma takai makiran mace har zahra tayi ciki ta haihu bamu ji ba . Lalai wanan matar a barta wurin zurfin ciki da bakin hali zanko nuna mata