← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 286

Sashe 106

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune yake gidin iccen mangoron dake kofan gidan a zahiri zaka dauka dabbobin dake killace a wuri daya yake kallo a lokacin don fuskanshi dake kallon dabbobin dake kiwo. Saidai a can kasan zuciyar shi tunanen halin da rayuwan shi ke ciki yakeyi idan bayi karya ba yau kwanan shi biyar ke nan a garin tsohon wanda kuma a kullun ana dan cigiyartawa koda Allah zaisa a samu wanda yasan waye mahaifin nasa a kasan. Saidai sunyi abune a dunkule don basu sanar a zamanance ba ko su cigiyarta ta hanyar daya dace subi na zamani koda ace sukai cigiya wurin uban kasan da haka zai iya taimaka masu har su kawo ga mutumin da suke nema din. Bakon malam musa kana jin dadin zama kai kadai baka sha,awan zuwa majalissane kayi hira ko baka da sha,awan hakane muyi sabo dakai sai zama kai kadai. Murmushi yaiwa saurin dake kaiwa zaune gefen shi saman dan iccen dashi Ahmed din yake zaune a kai yace ko naje majalissan ku ban san komai da zakuyi magana a kai ba yanzu zamana a nan ni kadai shine alherina don banji bangani daga abin ki. Kumafa kayi gaskiya don zaman majjalissa bai bar yaro ba baibar tsoho ba balle matar aure ko makaho duk wanda ya gitta sai an aza mashi ayyah a kai kafin yakai inda zai tafi din. Kaga ke nan kana muna wayau daka kebe nan kai kadai kana nazarin ka duk da dai wani lokacin zama a cikin mutanen yana da dadi don mutum na samun abin karuwa sosai. Dan bayaro kaine a nan kuma yau tare da bakon malam musa wani farin saurayi mai zubin fulanin asali ya fada yana karasaowa wurin su. Shima wuri ya samu ya zauna suna gaisawa kafin yace wai bako kai mutumin inane naji hausan ka daban da namu sosai yana kallon idon Ahmed din dake kallon su. Ni mutumin zamfarane wajajen sokoto hodi jam kace ka fito danisa kai bako aradu niko kano ban taba sani ba balle wanan garin sokoto ina dai jin sunan garin sosai a redio da waya kuma. Ashe Malam musa ba kusa ya fito ba dama harda yan uwa a wanan garin mai nisa haka gaskiya kayi tafiya sosai kafin kazo nan na farkon ya fada. Tafiyan kwana biyu da wuni ya kawoni nan garin ku kaga kuwa ai ba wani nisa mai yawa ga tafiyan ke nan Ahmed din ya fada cikkn zolaya don koshi da yayi tafiyan duk da tafiyan tana da muhinmanci a gareshi saida yayi nadaman yin hakan a zuciyarshi. Musanman yadda ya baro gida bai sanarwa kowa inda ya dosa ba wanda yasan hakan ba karamin tayarwa Dije da hankali hakan zaiyi ba. Amma shi hakan ya kama dole gareshi sai yayi wanan tafiyan don ya tserar da kanshi daga samun mutuncin shi da asali da aka fara kira mashi baida shi. Idan ya tsaya daka ta Dije da yan uwa ba zai taba samun hakan ba don sun tsaya akan dole shi mahaifin nasane zai kawo kanshi garesu idan har ya damu da danshi. Alhalin gaba dayan su kaf sun janye sun saka masu ido a yanzu ba wani wanda ke daukan kwandalanshi ya taimaka masu dashi duk da sunsan suna bukatan taimako a lokacin. Kowa yaja diyanshi a jiki sun waresu a gefe suna nasu lamari a tsakaninsu bayan shi malam ladan a baya lokacin da yake raye ya taimakawa yan uwa da abinda yake dan samu a aljihunshi lokacin. Yanzun ko kasa ya rufe ido tun mutuwanshi suka sakasu a gaba da wani surfan cewa ai gonan malam ladan din akwai kudin mshaifiyarsu ciki data kwashi adashe lokacin ta kara mai ya sayi gonan dashi. Dole aka saka gonan cikin na gadon su suka dawo kuma sukace ai sun tuna cewa gidan nan ma dasu Dije din da jikanta suke ciki yanzu da kudin tsohuwan su aka sayi filin har yai ginan. Wanan ne hukuma basu yarda da dashi ba kuma don angane suna son su wullakanta ahalin mamacinne kawai a duniya suke wanan kirkire kirkiren a yanzu din. Tun wanan case din suka dauki tsangwama suka sakawa Dije da ahalinta haka yasa karshe danta namiji daya tilo ya bar garin yai kaura ya koma garin ibadan da zama. Saidai kuma ko can din ma ba wani sana,an kirki yakeyi ba ana dai zaune hakanane sunan ba a garin ana wurin neman kudi don bai iya yiwa kanshi maganin dubu goma balle wanin shi. Haka yasa yakan dade bai leko gida ba don koda yazo din ma karshe idan zai koma na mota ma wuya yake masa yasa yanzuma ya daina zuwa ga baki daya garin. Su kuma diya matan na dije ita mahaifiyar Ahmed din tayi aure tabi mijinta kasan Niger state inda yake noma har zaman ya mayar dasu can na dindindin a yanzu sai can ba a rasa ba ta kan dan lekosu nan zamfara din. Haka ita kuma kanwarta a wani kauyen zamfara ne da ake kira silami take aure itama ba wani halin da zata iya tallafawa wanin ta don mijinta tallakane tilis. Wanan yasa suke zaune tsiya tsiya ita da dan jikanta a cikin rubaben gidan su da malam ladan ya mutu ya barsu a cikinshi. Saidai saboda gidan don rashin samun gyaran da baiyi lokaci lokaci saidai dan facin da Amadin ke yawan yiwa gidan tun yana karami har tasowa yanzu din daya girma don hali bai kai ba yasa suke zaune a cikinsa. Ko karatun boko da yayi Allah dai ya nufa sai yayi da taimakon Allah dana jama,a ya samu yakai secondary nan ma da kyar ya samu Allah ya rufa mai asiri gwanati na biyan kudi haka ma daya dauko karatun zuwa jami,a. Yasha korafi da ayi mugani na yan uwan kakan shi dana Dije din kowa ya dare ya zuba mai idanu shine ya hadu da madam na neman dan aiki yace zai iya da wanan taimakon ya samu har ya hada karatun shi na jami,a yanzu. Wai amma dai kai bako dama kasan ta kan shanuwa sosai ko dan naji iyayyen mu na maganan cewa duk yadda akayi kai din ka fito daga gidan manyan fulanine da suka san kansu da kuma sanin dabarun kiwo. A,a haaa nikan ai baffa shewa yayi yaron manya ne da ganinshi wata kila wani dangantaka ne ya hadashi da malam musa har yazo nan ya zauna dashi ? Dan uwan mahaifiyanane shi amsan da Ahmed yabawa samarin biyu ke nan da yake ganin sunzo don bugun cikin shine su san wani abu a game dashi dama. Haka kan don gaskiya baka da kama dashi don naji suna fadin dakai dan kasan nan ne sai suce kai jinin wurichedine don sune dabi,unsu yake irin naka sak naji baffana ya fada. Gaban Ahmed ne ya fadi don jin abinda dan bayaron ya fada amma saiya dake bai nuna komai a fuska ba sun dauki lokaci a tare dashi da suka fito sallah la,asarne suka rabu kowa ya kama gaban shi daga can din. Mamaki nayi kwarai lokacin da hjy karima ta kira layin wana tana sheda min cewa na fito na tari mutanen garin mu gasu nan sunzo daga zamfara din mu. Har na gama kimtsawa na fita zuwa inda suke ban gama mamajin hakan ba wanda ba wani abu nakewa mamaki ba sai yadda akayi wasu yan zamfara zasuzowa hjy karima buki tundaga can. Don naga ai buki idan bana mama ba basu zakewa haka har su kwaso jiki su zo idan buki ya sami ummah katsina koda sunce zasuzo karshe bamu ganin kowa har muje mu dawo saidai suba da excuse din karya suce shine ya hanasu zuwa. Daga karshe kuma muka gane saboda mamace don kada suyi laifi a wurinta dan abinda suke samu a daina basu yasa basu zuwa wani sha,ani na ummah din. Sallama nayi nasa kai dakin dasu na fara arba suna zaune a kasa sun baje sai abinci sukeci gashi an loda masu abincin a gabansu sai kwasa sukeyi kamar masu yunwa a ciki. Sai hakan ya bani kunya amma haka na daure na karaso ina fara,a a fuskana ina fadin gwaggo ashe kuna hanya sannuku da zuwa. Suka juyo tare da fara,a suna fadin a,a maamahce an zama mutanen kano ashe kina nan tare da maman ku amarya ? Eh daga Abuja danaje hutu mukazo nan din tare dasu au ashe dama kina can wajensu Abujane nace eh tunda akai hutu nake can ai ya hanya ya mutanen gida nayi saurin kawar da zancen a lokacin. Kowa lafiya kalau ummah kima jiya muna tare gidan ya mamman nake fada mata zancen zuwan mu saidai lokacin ba a gama tsayar da maganan ba don na daukama da wata cikin su zamuzo ashe ba wanda zaizo a cikinsu. Aiko za a zo ita kan hjy salma dake da yara kanana bata samun zuwa don makaranta gwaggo Ai ta fada tana kai loman abinci a bakinta. Hakane gaskiya yanzu ita bata faye zuwa wuri ba don yaranta ita dai yar mulkin daine kuma kunsan bata zuwa koda alama . Mommy ce ta fito take fadin yauwa Zahra kin fito nace kizo gasu gwaggon ku sun iso ku gaisa dasu dan dariyan yake na sake a fuskana nace. Wallafa ashe suma suna hanya ga tafiyan da dan nisa sai naji gwaggo shafa tace ai ma tafiyan kamar girshi yazo muna don masu son zuwa suna da yawa motar da yaya ya bayar kuma iyakan mu zata dauka. Ke nan ma ashe da babban mota Abba ya basu dasunfi nan yawa ke nan da basuzo su biyar ba sai ashirin tunda wurin kwadaine don suna ganin wurin samune nan. Duk a zuciyana nake wanan zancen ni kadai dan dama ance diya mace tasan zafin uwarta fiye da da namiji wani lokaci don haka ke nan ina jin zafin yadda dangin Abba kewa mahaifiyar mu nima. Badon komai ba sai don kawai suna ganin cewa ita ummah bazata iya masu wani hanya har su samu komai daga mijinsu ba ma,ana dan uwansu. Ina nan dai zaune dasu a dakin idan suna son wani abu zan tashi naje na dauko masu duk da mimmy ta kama kanta tana can tana sha,anin bukinta su
Chapter 106 · 0% Book details