Sashe 163
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
har ta tabo jinnu suke wahalal da ita a yanzu don malam yace ta nuna rashin imani a garesu ne. Ai kaji irinta lokaci daya yarinyar nan ta canza halaiyarta dana santa dasu a baya wanan yawon ciranin bai kara Rashida da komai ba wallahi shiko ba abinda ya tsaya mashi a rai sai tunanen yadda inna din ta nunawa uwargarke a ranan. Sai wanan abin ya tsaya mashi sosai a rai daya je basu abinci ya duka yana gyara mata wuri yana fadin uwargarke nasan inna ta bata maki rai kin kuma rama amma don ni da yan uwana ki barta hakan kamar da wasa yai maganan gami da kurciya lokacin tunda yaji ance dabbobi suna jin maganan mutane.. Abu kamar wasa saiga ina ta mike wasai washegari kamar ba ita ba lafiya ya samu tana ta faman kwasan barci kamar tasha maganin barci yana mata amfani a jiki. Alh ban fahinci wanan sabon halaiyar daka tsiro dasu a yanzu ba matar ta fada cikin kunan rai a cikin harshen fulatanci. Yana a yadda yake zaune zakace badashi take wanan maganan ba lokacin yadda baiko motsa ba ganin hakan ya kara bata haushe ta tako zuwa gaban shi ta tsaya tana kara maimaita abinda ta fada da farko. Sai lokacin ya dago ya kalleta da tun kan ya bude baki yai magana ta hango zallah tsana da masifa a indon shi abinda bata taba hangowa ba ke nan a zaman su. Don tana da tabbacin cewa duk yadda ta juyashiba nan yake tsayawa ba mussu gareta amma a yan kwanakin nan abubuwa sai kara bata mamaki yakeyi na sabon halaiyan shi. A ranan sai ya koma mata dangasken shi data sani ba Alh ta ba da take juyawa gabantane ya yanke ta fadi sosai tasan akwai matsala babba dake shirin faruwa da rayuwanta nan gaba. Ke ki fita daga dakin nan tunkan rayuwan ki yakai ga baci ya fada cikin kakausan harshe gareta dole tanaji tana gani ta juya zuwa part din ta cike da fargaba a zuciyanta. Kallo takaici ya bita dashi har lokacin data rufo kofan ya sauke idon shi ga kallon rakiyan dayai mata din na takaici. A yanzu yake nadama da dana sanin tare da tambayan kanshi na hada iri da wa yan nan mutane marasa kirki a yadda yasan su a baya a yanzu ga zuria sun shiga tsakanin su dasu haka. Ashine tambayan da yake yawan yiwa kansa lokaci lokaci a yan kwanakin nan gashi ya kula duk wani dan uwa nasa na jini a yanzu bai tare dasu sai yan tsiraru haka daga cikinsu din duk halin hjy Yabi ya koresu gareshi. Kai ya mayar baya saman makarin kujera yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali ya dan runtse idanunshi a hankali yayin dayake dan kada kafanshi a hankali. A haka barcin ya dan daukeshi yana wanan tunanen ya kwana biyu da wanan mafalkin sai gashi yayi a dan barcin daya daukeshi din lokacin. Yaron nan daine mai kama da yasir dinshi duk da bayan shi yake yawan gani lokaci lokaci amma kamaninshi da danshi yasir yana da yawa ko a hakan da bayan shi yake gani kawai. Zubur ya dan zabura yana waige waige a falon ta ina zaiga wanan matashin daya shigo mai yanzu yana maganan akan hakkin shi wani haki nasa zai basane haka wai ? Hannu ya yakai a fuska ya shafo kafin ya tsayar da hannun zuwa goshin shi yana dan murza kadan kadan tare da tunane a zuciyan shi. Inda tunanen nasa ya tsaya cak ga abokanshi na kurciya dake gida zaune a yanzun cikin halin irin na rufin asirin bawa duk da yaci ace ya taimakesu a yanzu amma ya kasa hakan a garesu. A hankali ya bude ido kafin ya mayar ya rufesu a hankali yana mai jin wani irin zafi a ziciyanshi don ya kasa gane dalilun haka a gareshi bayan yasan irin gudunmawa da suka bashi a rayuwansu a baya suna yara dashi. Yanzu meye abinyi ya tambayi kanshi a take zuciyarshi ta bashi amsa a wurin da ya nemi dan Jauro donshi gaba daya cikin su yafisu natsuwa da sanyin hali ga sanin ya kamata. Bai karasa tunanen shiba yaji jauro din yana masa sallama a cikin waya jin haka yasa ya katse tunanen shi ya amsa masa sallaman shima. Ikon Allah yau dan gaskene da kansa haka ya kirani ko batan layi kayine ya fadamai cikin zolaya dan murmushim manya ya sake tare da fadin ba bata nayi ba kaidin dai na kira muyi zumunci. Murmushin ya mayar mashi shima tare da fadin aikuwa nagode gamuma tare da jabbo yanzu haka a kofan gidanshi jauro ya fada . Wani iri yaji a ranshi kafin yace dasu kai haba dai kuce ni kadai kuka ware dama ina Alamu yanzu yabar nan zuwa asibiti shima duban yakumbomsu da aka kwantar jiya. Idonshi arufe yace jam balafiyane haka har asibiti yace eh wallahi kasan tsufa da yan ciwarwatan zamanin nan na yanzu da ba a rasaba. Badai kuna lafiya da iyalin naka ba nan duka ko kuna kasan wajenne yanzu don baku zama a cikin kasan nan sosai ku ? A,a muna nan duk lafiya suke to madallah Allah abin godiya nagode nagode Allah ya bar zumunci amin tunda ka tuna damu har munji lafiyanka a yau. Don ko jiyan nan saida Alamu yai maganan ka nace tunda mukaji shiru lafiya kuke don shiru ke nuna lafiyan mutum. Tau lafiyan dai amma ba lau ba don wani abu ke damuna ya kuma daure min kai sosai a yanzu jauro shine naga ba wanda ya kamata in nema yaban shawara illa kai sai gashima kana kusa da Jabbo ashe. Jam jam dangaske meye wanan abin wanda yai zafi haka ya daurema kai kuwa ku manyan kasa daku sai yai masa murmushi irin nasu. Wayance ta dauke ya barsu suna faman fadin hello hello don sunzaci cewa shiru yai masu yana jinsu sai daga baya suka gane cewa wayance ta katse ashe. Shigowan yarinyarshi yasa ya kashe wayan yana saurarenta don zancen data zo mai dashi lokacin wanda tambayanshi takeyi Dad mekayiwa mommy take kuka ? Don yaran tashin falone kai tsaye suke zance da iyayyen nasu saboda gata daso dayai masu yawa a rayuwa sun tashi basu da kwabo ko kadan. Balle su san basuyi daidai ba gashi uwar kamar itace uba a gidan duk komai na rayuwan gidan itace ke gudanar dashi . Don hakane sukafi ganin kimarta da uban nasu sosai yanzunma data samu uwar a daki ta gama waya da yarta ta tambayeta meya sameta shine tace daddysune. Bata tsaya jin meyafaru ba kawai ta juya ta fita zuwa wurin daddyn nasu ta tambayi ba,asi taji abinda yaiwa mommy din nasu. Itama kamar uwar ya barta da mamajinshi ranan don ya koma mata tankar wani zaki agabanta yadda ya daka mata tsawan da saidata kadu ta koma tana mashi kallon mamaki lokaci guda. Don cewa da tayi dashi bayan ta fado mai falon a hasale yana zaune yana waya lokacin da abokan nasa. Tace dashi da daddy mekaiwa mommy mu na samu tana kuka akan ka kuma ban saba ganin hakan gareta ba sai yau ? Ya dago kai cikin mamaki tare da kashe wayan yace you are very stupid Ni,ima you are more than stupid da zakizo kina min wanan tambayan haka ba respect a tare dake ? Yadsa yake maganan yasa ta kaduwa don gaba daya ya canzawa sanin ta a ranan ya koma irin mahaifin da take gani a cikin film ko a wasu gidajen . Kofa ya nuna mata da yatsa alaman ta fita mashi daga falon tayi saurin juyawa zata bar falon yace dakata daga yau karki sake shigo min falo haka kai tsaye babu sallama understand ? Ta gyada mashi kai alaman taji ta juya ta fita zuwa part din uwan nasu hankalinta tashe tana tafiya kamar tababa a lokacin.