← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 286

Sashe 223

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau wace rana don haka tayi mamakin ganin mijin nata a dakin dakanshi ya shigo wanda ba zatace ga iya watannin da suka dauka bataga hakan ba tun bayan faruwan abubuwa da dama a garesu. Har ta fara tunanen ko yaran nata harsun gana da mahaifin nasune a lokacin don haka ta fara tunanen kalan wullakacin da zata yanka masa tunda ya dawo hannunta a yanzu din. Dago kan da tayine ta kalleshi yasa shi gyara tsayi yana fadin dama nazo in fada maki cewa zan yi tafiya a yau din nan ta gagawa sai zuwa jibi zan dawo. Kallon mamaki ta dago kanta tanayi kafin tace dashi tafiya haka ga yaran nan duka a gari ba zaka samu lokacin zama dasu ba ? Yara ya tambaya cikin mamaki tare da dorawa da fadin wasu yaran wai kike nufi har kike magana akansu kada nayi tafiya gasu ? Wasu yara ka tambaya kadana wasu diyane da sukafi yasir da salima da kannensu ina da mana ko kin manta da ina da wani da kafin yasir din yazo duniya don haka ki rika sakashi cikin jam,in ki idan kin tashi magana daga yau din nan. Baki ta bude da zuman fadin wani da kuma sai ta tuno ai a baya ance yana da da amma ai sun share babin wanan dan nasa tuni acikin rayuwanshi ko ? Ko hakan daya fada yanzu yana nufin boyayyar maganan dan ya dawo mashi a zuciyarshine yanzu wai inko hakane zama bai ganta ba ashe da magana kuwa sabo gareta nan gaba. Juyowa yayi ya katse mata dan guntun tunanenta da fadin tare da hjy murja zamuyi tafiyan don haka ke kadaice a gidan tare da yaranki sai yan aiki ke nan yana fada ya fice a dakin ya barta cikin bacin rai a lokacin. Tunane ba zai kaita ba don haka ta mike da sauri zuwa dakin danta ta tasheshi ga dakin sai tsamin giya yakeyi da taban dayasha ya dirkawa cikinshi kafin ya kwanta. A ciki tashin hankali take kwala masa kira kan ya tashi da kyar ta samu ya falka kuma falkawan bai kara mata komai ba don yana cikin maye a lokacin. Dakin salima ta nufa itacema ta samu suka fita tare saidai suna zuwa motanshi ta karshe tana fita get din gidan hakan yasa takaici ya kara kumesu a lokacin. Haka suka koma ciki zugun zugun dasu ga takaicin miji gana danta dake damun zuciyan ta sai sha biyu yunwa ya sauko dashi ya fito yana hamma a lokacin buko digon kunya a idanunshi. Wurin abinci ya nufa kai tsaye ya fara budewa baiga abinda ke masa ba don kunun gyada suka dama sai kuma irish da kwai da aka soyo sune aje a kan dinning table din. Kwai da dankalin ya jawo ya zuba ya somaci saida ya fara koshi ya dago kai ya kalli inda suke zaune sun zuba mashi ido suna kallon shi cikin takaici. Kafin ya cire hannu ya kallesu ya ware hannayen nasa ya nuna alaman tambaya zuwa garesu din kan irin kallon da suke mai a lokaci. Yasir dama haka ka koma ban sani ba ashe shine dalilin dayasa Alh ya karawa gidansa security har da yansanda a yanzu don yasan ya haifi dan iska. Bai taba cewa zaiyi tafiya tare da murja ba amma yau tare yace zasuyi tafiyan sai yanzu nagano ko don saboda menene ya tafi da ita tafiya yau din nan har yar aikinta bai bari a cikin gidan nan ba ashe saboda kaine. Fuska ya dago ya kalli mahaifiyan cikin mamaki yace saboda dani zaiyi tafiya da ita why sabodani haka zai kasance nace zan mata wani abune ko me ? Ko baka furta cewa zakayi ba nasan Alh ya rigada yasan kome kakeyi acan France shiyasa ya dauki wanan matakan yanzu haka. Idan ko har hakane zuwanka turai dana zabama ya zama min dana sani haka wanan zuwan nakama bai mun rana ba wallahi a yanzu. Na kiraku don kuzo ku zauna da mahaifinku amma kai badala kawai kasaka a gabanka shiyasa yayi min habaicin cewa dagani sai diyanane a gidan nan yanzu saiko yan aikin mu dake gidan kafin ya tafi. Ke nan haka na nufin akwai wani mugun aiki daya san kana aikatawa a can ke nan yanzu yasa da zai tafi ya kwashe iyalansa da yake so ya barni daku a gidan. Kai ya jijoga ya taso zuwa inda uwar take tsaye saida ya dan zagayata kafin yace gaskiya tsohon nan yanada wayau sosai da yayi dabaran hakan shima ya dauka kashe ta zanyi idan ya barta nan kome ? Gargadi kawai zan mata idan nataji ba sai nayi mata fewwwww ya nuna hanunshi a saman wuyan shi yana lumshe idanuwanshi lokaci guda. Dama haka ka koma yasir Alh ya sani bai sanar dani ba hakan ko wanan yasa Alh yake kina daku yanzu ko kuma dai shima a yanzu yai nazarin hakan gareka ? Kasan wanan abin kunyam da kake shirin shuka muna mu fulani abin kunyana da fade a wajen mu don ba wanda zaiba mai irin halin ka mata yasir. Ina tufafin da nake aika maka dasu ko wani lokaci ta fada tana kallon idon dan nata kafin ya amsa saida ya juya yace sayarwa nakeyi a can kuma suna sonsa sosai wlh don guy din ya iya dinki sosai. Zubewa tayi a wurin ta rike hannun kujera ta dora kanta akai ta fara rera wani irin kuka gwanin ban tsusayi ganin hakan yasa salima mikewa tana dakawa wan nata tsawa akan ya fita daga falon ga baki daya. Ya juyo yana mata wani irin kallo kafin yace idan taji naki nawa mai saukin saurara ne a kunnuwanta yanzu amma zan fita din sai mun hadu kisan nasan komai akanki. Friday ne yasa ban dadeba na dawo gida don ranan da safe kawai nake lacture kodana dawo na samu ya dora muna abinci yana dafa shinkafa. Naji dadin hakan don haka na canza kayan jikina na fara aikin miyan da zan dora muna din don kada in makara dan dabi,anshine sai ya dawo daga sallah jumma,a yake cin abincinsa na rana a ranan jumma,a. Don haka na karasa aikina a tsanake na gyara wuri na dauki nasu Dije nakai masu part din su babu kowa a tsakar gidan don haka na shige dakin Dije din kai tsaye ba tare da wani ya ganni ba. Bandade da shiga ba naji muryan inna tana fadin Asmau kizo ki leko muna yarinyar can yau me take dafawa haka kamshi duk ya gaure gidan da tashin da alama wani abin dadin ne suke girkawa yanzu tana iya gamawa ta boyeshi a daki su cinye su kadai. Daga dakin Dije na amsa masu ina fadin Asmau ki dawo ga naku nan na kawo maku nan na dauka ba kowa a dakin ne na aje a nan dakin Dije bakomai bane miyar kan shanune daya sayo jiya na dafa yau. Duk abinda na girka ban taba boyewa a daki ban ba wani a gidan nan idan ba idomie da nakan dan sulala da dare ba inci koshi dasu Aisha mukecinsa don ban iya cinye guda daya ni. shiru naji inna din tayi Asmau kuma bata shigo ba don haka na duka na dauka na nufi dakin nasu dashi na shiga ina fadin ga abincin inna tayi shiru bata ban amsa ba tana kokarin shimfida dadumar sallah a lokacin. Na fito ban koma dakin dije ba na nufi part dina kai tsaye cike da bakin ciki da bacin rai na irin abubuwan da ina ke mun a gidan nan. Gara na bar mata gida zaifi don kada tazovta illantani nan gaba don kiyayyan nata gareni yayi yawa tunda harda kazafin abinci take iya min duk da tasan kome na dafa saina diban masu ita da yaranta bayan wanda zan sakaqa dije din kuma subi suci. In kin debe indomei danakan dafa wani lokacin da dare idan baya gari koshi tare da yaranta mukeci din bana iya cinye idomie daya idan na dafa. Haka kuma Allah ya gani Ahmed yana da kokari wurin fitar da hakkin iyayye akan shi don haka zai sayo masu abin miya bai sawo min ba saidai inya dawo ya ban hakkuri cewa baida kudine yaga ni ina da saura da banyi amfani dashi ba. Haka dangin sabulu da omo da man shafawa zai saya masu kusan sau biyu saigana uku zai sayo dani duk wanan bai taba damuna in tambayeshi meyasa hakan ? Amma duk wanan baiwa inna ba sai takai da yimin shedan rowa wai harda fadin zan iya boye abinci sai kawai naji abincin ya fita min a raina lokaci guda. Koda ya dawo ina kwance inda na idar da sallah ya shigo yana fadin wallahi kin kyauta ina Allah Allah na dawo na samu kin gama girki dama taso muci yunwa nake ji sosai yau. Kaci kawai nace dashi ba tare dana dago kaina kalleshi ba kincine ko ya fada yana kaiwa zaune tare da jawo kulan abincin gaban shi banci ba bandai cine na fada a sanyaye. Sai ya dago kai ya kalleni bazakici ba kuma bakici komai ba nace kaci kawai idan na tashi zanci ai ya zuba ya soma ci har yayi rabi naga ya mike ya fita daga dakin din yace ina zuwa. Kitchen ya shiga ya duba babu komai har na wanke tukunya na kife sai gashi ya dawo wanan karon ba wasa a fuskanshi yace ki taso kibar wayan nan kizo muci abinci zahra. Kaci in na tashi zan dafa indomie naci na bashi amsa ga abinci zakije cin indomie kuma nace eh shinake so naci na kara gyara kwanciyana ina game. Naji ya gama ya fita ashe wurin Dije ya nufa yana tambaya zahra tayi fada da wanine bayan fitana sai dije din tace dashi matarka tana da abokin fadane a gidan nan bayan uwarku dake zubar da girmanta gareta. Ai tayi arziki baka dauko mata mai ido bude ba kayi dace da Allah ya baka matar kirki da ko tana sonka kana sonta halin uwarku zaisa ta bargidan nan. Ko kuma a dunga shigowa kullun ana rabasu fada a tsakanin nan ta kwashe komai ta fada mai yayi shiru kafin yaja tsuki ya fita
Chapter 223 · 0% Book details