Sashe 226
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAMBARAKE garine dake cikin Benin republic dake makwabtaka da kasan Nigeria kamar sauran kasashen da sukeda iyaka da kasan ta Nigeria. Mutanen cikinsa bakakene yayyen kasan faransa don sune suka yayesu a zaman amsan incin kai daga mulkin mallaka da turawa sukaiwa kakanin mu na bakkaken fata irin mulki na bauta da rasa incin kai. Akasarin mazauna wanan kasan Dandawane babu addini a tare dasu sai bauta irinna arnanci da ake kira da kafirci a sannu wayen kai har addini yazo ya ziyarcesu yanzun kasan nada mabiya addinin musulunci dana kirstanci sai da yawansu da har yanzu suke bautawa abin bautansu. Allah yayisu mutanene karfafa ga baki ga tsayi irin kiran samudawa mazansu da matansu yana da wuya ka samu wanda baida tsawo a cikinsu gaskiya. Sun dogarane da noma da kiwo sai sana,oin da akasan malam bakar fata dashi irin su kira rini farauta da sauransu . Zaman su makwabta da Nigeria yasa a yanzu idan kaje kasan zaka samu mutanen mu na nan Nigeria a can suna sana,an neman kudi don gaskiya akwai albarkan kasa a tare dasu sosai hakan yasa wasu ke ketarawa daga nan zuwa can su kama yan sana,oinsu na hannu. Ko addinin na wa yan nan mutanen gashi nan dai ga kamarsane suna muna musulmaine su ko kirtancin don al,ada yaci gaban komai a garesu har yanzun basu yarda dabi,unsu ba a kasan. Amma haka wasu mutanen mu suke shige suyi sana,a a tare dasu don a yanzu kowa ya fahinci dan uwan junane kasa daine ba daya ba dasu. Akwai hatsari sosai shiga irin wa yan nan wajajen amma neman na kai yanzu yasa mutanen mu basu tsoron kutsawa irin kasashen nan matuka zasu samu abinda sukaje nema a wajensu din. Darene sosai ko wanen su yana saye da rigan sanyi ga hula sun kafa don yanayin dajin da suke shiga din don zuwa cin kasuwan da akace shigan safe zasuyiwa kasuwan. Gashi kuma an labarta masu cewa hatsinsu yana da sauki sosai kuma ana samu ba sai ya katse ba don haka suka shigo wanan kasar su gwada sa,ansu. Wasu barci suke wasu kuma sabbin zuwa irin su Amadi sai bin surkukin dajin sukeyi da kallon tsoro tare da tunane kala kala a zukatansu. A garin akwai Irin su shimkafa masara dawa shine dalilin yin wanan tafiyan na Amadi tare da abokan nansa da suka kwadaita mashi zuwa wanan garin neman hatsin irin wanda suke sayarwa. Alhamdullahi sun isa lafiya sunje sun samu kamar yadda labarin yazo masu hadi da kari kuma sun gane cewa zaka iya daukan mai a nan Nigeria kaiwa mutanen shima akwai samu a cikinsa sosai saida hakan akwai wahala. Wanda yai masu jagora zuwa garin suke bi a baya yayin da yake kara nausawa cikin kasuwan zuwa dasu wurin abokan cinikinsa . Duk sammakonsu sun samu kasuwa ta faraci a lokacin don haka wuri ya fara cika sosai da mutane wanda yayo masu jagora yana ta ja masu kunne akan su kulla da kudinsu dai don akwai bariyi sosai a kasuwan. Amadi bai yarda an barshi a baya ko gefe ya tsakiya cikin tawagansu har suka kai wajen ga kayan gona nan ko wani irin launi an baza a wajen gwanin burgewa. Cinikin gaba daya aka fara yi suji kudin buhuhunan yayin da suka shagala da sauraron bayanin da mutumin keyi ake fassara masu haka kawai ba zato yaji anja bayan riganshi . Cikin azama ya juyo a zatonshi barawone yake lalubenshi sai yaga wani tsoho a cikin shigar kamala na mutunci tsaye a bayan nasa yana mashi murmushi. Nan take hankalin kowa ya dawo garesu sai kawai wanan tsohon ya zube kasa ya daga hannu kamar wanda yakewa wani basarake ko babban mutum gaisuwa ya fara jera mai kirari a cikin yaresu. Ido kowa ya zuba masu yana kallonsu shi Amadin bai gusa ba haka shima dai bai dago daga yadda yaken ba sai faman jerawa mutumin kirari yakeyi. Dama wanan din dan sarkin fulanine kuke tafe dashi wanan mutumin mai masu fassaran yare yake tambayan cikin mamaki. Wanan din gaskiya ban tsamanin hakan don dai a sanina shidin kamar ba dan kowa bane fa da sauri wanan din yace a, a kada kace hakan saidai idan kaine baka sani ba gaskiya . Amma abinda Alh ke fadi ya nuna alaman sarauta da kudi ga yaron shi kuma din kansa wani babbane nan gaba haka kawai basuyi aune ba sai suka fara ganin jinsin wasu kabila na kasuwan suna kawo mai gaisuwa lokaci guda. Tsohon na farko ya dago kai yanawa Amadi din wasu gwalancin cikin yarensu shidai ido kawai ya zuba masu yana binsu da kallo ya dauka hakan sallon wani yaudarane a gareshi suka fito mai dashi sai kokarin dafe madaurin kudin shi yakeyi lokacin. Wai ku taimaka yaje gidansa kafin ya tafi akwai maganan da yake son yi dashi don Allah wani ya fada masu a cikin yaren hausa da sukeji don mutane kamar ko ina idan sunga abin mamaki harsun kewaye suna kallon ikon Allah . Kai haba dai ina haka zai yuyu haka kawai bamu san mutum ba kuce ya bishi ya bishi zuwa ina iyakarmu cikin kasuwan nan saiko bakin motar mu in kaga mun daga nan wani babban mutum daga cikin su Amadi din ya fada. Haba don Allah wanan Alh gambarine fa sananen mai kudi kuma basarake a cikin kasan nan ba wanan kasuwan ba duk wani kasuwa mai tashe a kasan nan asandashi sananen mutum ne shi sosai . In bakai mamaki ba kusan kayan wajen nan nasa ne kafa wallahi don haka ba zai taba masa wani abuba gaskiya kawai dai akwai abinda ya sanine a game dashi. Alh Bala ku bari kawai zan bishi inji ko me yake son fada min dole akwai wani abu don bai fadi karya ba ainihin tsotson mahaifina basarake ne a can kasansu don haka wani abin yake son sanar dani. Kai Amadi wanan wani sabon zance kake son sanar damu kada kwadayin duniya ya kaika ka jawowa kanka wahala ba ruwan mu hatsi mukazo saya shi zamu saya mu koma. Kafin ya karasa fadin maganan shi baiyi aune ba sai ganin Amadin ya daga wanan tsohon yayi ya kuma tsaya suna gwalanci dashi duk suka zuba masu idanu suna kallon su. Zan bishi yace ba zamu dade ba yanzu zamu dawo kafin a gama lodin kayan mu idan an shirya suka amsa mashi tunda ikon Allah suke kallo a lokacin. Wanan dattijon ya fito wani mutum yazo ya kaishi ga wanan mai masu jagora yake fadin zai tafi da wanan don ya dinga masa bayanin inda bai fahinceshi ba suka dan amsa da to kawai. Nan suka fara kus kus dinshi shidai yabi bayan mutumin suka tafi tafiyan daya kawo karshen komai ya kuma walwalewa Amadin kai lokaci guda. Da farko ya dauka kusane zasu tafi saida yaga anyi tafiya mai nisa ya fara dana sanin biyo wanan mutumin da bai sani ba bai kuma san mai ceton shi ba a lokacin bayan Allah. Gidane irin nasu ginan na kasan komai da laka akayishi da duwatsu har shefen sumintin ginan nasu fari kal da alaman farar kasane akai amfani dashi ga ginan. Saidai alama ya nuna cewa ginan gidan yanayin shi na babban mutum ne don yadda aka bambantashi da sauran ginan kauyen duk komai kallo yake kamar a mafalki lokacin. Kauyen ya tuna mashi zuwanshi kasan mambila don yaren fulatancin daya samu sunayi a nan ba wancan yare ba da suka baro a cikin kasuwa ba. Da hannu ya yafuto wani yazo a cikin dan sarsarfa irinta girmawawa yai masa yare sai ya juya yabi wani hanya yana sauri ya tafi. Manyan tabarmin saka na kaba irin na gargajiya daya sani a da yaga an fito dasu ana shimfidawa a wani innuwan iccen daya samu wuri ya baje ya sake rassa sai innu da duhu har yana ba mutum tsoro. Suka nufi wajen suka zauna yara nata kawo filo da tim tim sai binsu da kallo yake yana mamaki ya kalli wanan mutumin da sukazo tare yace ka fadawa bakon yayi hakkuri da yanayin mu na nan din. Gashi kuma har wa yau ba yaren mu yake ji bashi da badon hakan ba dayasha bayani yau a bakina amma a gurguje ka fada mai muna mashi sannu da zuwa. Ya saki jikinshi nan din gidane garshi idan ya sani ka kuma fads mai komai a gurguje zamuyishi yanzu don ba lokaci garemu zan bashi magani yasha a nan ko zai yarda yasha din ? Nan wanan mutumin ya juyo yayiwa Amadi din bayanin duk abinda tsohon ya fada yayi dan murmushi yana gyara zama tare da kada kai. Tsohon basaraken nan ya kara tare numfashin mutumin a cikin yaren kasan yana fadin ka gaiya masa nace shi din jinin gidan Hardo Amadune kuma jika ga hardo Bukar na garin Chedi Garba ko ? Don haka ya saki jiki babu cutarwa a tsakanin mu dashi zan taimaka mashi kan abinda baisan dashi bane a jikinshi dake biye dashi tun yana yaro karami . Ko ya yarda da nasan shiko waye a yanzu sai mutumin ya kara masa bayani kamar yadda ya fada mai yace ya yarda yayin da wata zuciya ke fadin haka kawai zaka amince masa ba tare da sanin koshi waye ba gareka. Bayani tsab yadda zai fahinta kuma wanan tsohon duk yaiwa mutumin ya gamsu da hakan din haka ya yarda a zuciyarshi koma meye zai karba yayi kamar yadda ya hango gaskiya a cikin idon mutumin lokaci guda. Kaidin sun sani magajin chedine yasa suka daure duk wani hanya naka da zaisa ka hasaka a san da kai da badon naka mabiyan nagadon gida ba da komai ya gama faruwa dakai a yanzu. Amma ka godewa Allah da taimakon wasu abubuwan sunki tafiya a yadda sukeson suje masu saidai abu daya shine wanda aka bizzine a wani tsohon rijiyan da yanzu har anshafeshi . Shi wanan abin kuwa nake son na baka makarin shi a yanzu da zaran yabi jikin ka zaka iya tunkaran duk sauran matsalolin naka ba tare da wani abu ya sameka kaba. Nasan kasan da hakan don an sanar dakai komai a baya kan hakan Allah ya taimaka fararen mabiya ke