← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 242 OF 286

Sashe 242

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu kamar wasa sai ga magana ya tabbata gaskiya mashin ko kasa ko sama ba a ganshi ba kuwa nan inna tayi ta babatunta a cikin gida tagaji dai ta kyale dole tunda babu dai yadda za,ayi. A cikin hakan kuma Ahmed din ya shiga Abujan daya yace din don yin wasu takardu a can a gidan iyayyen wani abokinshi ya sauka wanda suke karatu tare a zaria. Ya kaishi wurin iyayyenshi su gaisa duk da karatune ya hadasu amma ya girmi Ahmed din a shekaru gaskiya suna dai abotane kawai irin na karatu ana tare. Suna gaban iyayyen nasa shi abokin yace to mummy kinga dan school din namu da nake fada maku dan zamfara wanda nace maku karami dashi yana da mata . Amma ni kunce wai nayi karami da neman budurwa yanzu balle aure kai Ahmed din ya dukar kasa don kunyan abinda abokin nasa ya fada game dashi a gaban iyayyen nasa. Salati mahaifiyar nasa ta saka yayin da mahaifin shi ya danyi murmushi yace ka kalleshi mana ka kalli kanka ai kasan ya fika natsuwa da sanin ya kamata. Wanan zai iya rike ko mata hudune yanzu don yana da natsuwa ba sai an fada ba ai don wanan shiyasa fa don ace min hakan nake koyi da halinsa yanzu momi bakiga na canza ba sosai kuma sallah baya wuceni ko yaushe yanzu. Kai tafi can don Allah ka rabamu da shirmensa ka kaishi daki ya huta yaci abinci ka zaunar dashi kana masa shirme a nan ai kaga irin rashin hankalin naka zakace wai ai maka aure yanzu. Ka diba yadda ya zauna a kasa da zai gaidamu kakofa ba a tsakiyan mu kake zaune ba yanzu hakama ko gidan matar kaje neman aure zaka haye kujeran ubanta ka zauna. Duk aka kwashe da dariya harshi a falin suka mike zuwa cikin yaga taro na mutunci da karramawa a wurinsu nan yayi kwanakinshi da taimakon abokim nasa ya samu ya kammala abinda yazo yi abujan sukai sallah jumma,a a Central mosque. Bayan sun fito daga sallah yake cewa abokin nasa akwai wanda zan gani a nan dama bayan sallah bari na kira naji ko ya samu zuwa a lokacin ne kuma wayanshi ta dauki kara ya ciro daga aljihunsa yana dubawa tare da fadin gashima ya kirani. Sallama yayi bayan ya dauka yake fadin gamu a mosque din aka amsa mai da fadin amma zaka bari mu gaisa ai ko mahaifin nasa ya fada jin hakane ya dan shake murya yana fadin. Ina wuni gani nan ta kofan ya juya ya tambayi abokin ya fada masa shima ya fada mai yace muna saurine yau nake son in koma gida. Kana nufin har kayi abinda ya kawoka garin ke nan yace eh tun rana monday na shigo yau kuma zan koma ok gamu zamuzo wurin ya fada yana kashe wayan. Mutumin garinkune ko abokin nasa ya tambayeshi saida ya danyi murmushin yake yace mahaifina ne yana kawar da kansa gefe daya. Da sauri yayi mai wani irin kallon mamaki yace mahaifinka fa kace dama mahaifinka yana garin nan ne baka taba fada min ba kafin ya rufe baki Abban ya tsaya a gaban mu. Ba sai ka tambaya koshi waye ba gareni saboda yawan kaman mu dashi don sak shi na kwaso a wurin kama shiyasa mutane suke musun cewa wai innace ta haifenshi don basu da kama da ita a ko ina. Kai ya daga sau daya ya kalleshi ya dukar da nasa da sauri yayin da yakai kasa kuma yana masa gausuwan da hausawa sukewa iyayyen su na girmamawa a garesu. Ganin hakan yasa abokin nasa shima ya kai kasa da sauri kamar yadda shima din yaga yayi suna gaida mahaifin nasu. Ku tashi yace dasu yayin daya kai hannuwanshi saman kafadan Ahmed din yana tayar dashi yace yanzu baba karami ka kyauta ke nan kana cikin garin nan amma bakazo gidana ba sai yau da zaka tafine zan ganka ? Duk da nasan baka son taimakona a yanzu amma ya dace ace munga juna dakai tun zuwanka garin nan ko badon niba ai zakazo don yan uwaka ko uwayeka nagida. Wani iri Ahmed din yaji ya sonar da kansa kasa saidai yayi alkawari a ransa cewa duk yadda mahaifin nasa yake kokarin nuna masa ba komai a fili bazai yarda ya afka gidan mahaifin nasa ba a yanzu sai nan gaba kamar yadda shi ya daukarwa kanshi alkawarin hakan. A nan yaja hannun dan nashi suka dan fara takawa a hankali yayin da kowa na wurin yake kallon ikon Allah don ba sai a tambaya ba ko dansane ko kuma wani dan uwansa saboda kamarsu da yai yawa na jini. Mamakin shi wanan mai kama da Alhajin wayeshi wasu keyi inka don har yafi danshi yin kama dashi sosai saboda shi yasir ya dan debo mahaifiyarshi ga tsayi don baikai uban nasu tsawo ba . Inka debe bala driver a wurin danshi Alh ya fada ma komai game da dan nasa lokacin da suka bishi zuwa zamfara shikuma bai fadawa kowa komaiba kan hakan. Malam Ahmed kayi hakkuri ka jaye tafiyan ka a yau din nan muje gidana kaga iyalaina suma su ganka koda kuwa ba zaka kwana a wurina ba idan kayi min ko hakan ne ya datar dani a zuciyana. Abinda Alh ke fadi ke nan ga dan nasa lokacin dayaja hannun nasa suka kebe daga sauran mutanen dake wajen don ganawa da dan nasa dayazo garin ba tare da saninsa ba. Alkawari na dauka sai wanan asirin na gidan ka a kaina ya karye zan taka kafana zuwa gidan ka Abba idan yau baba musa ya kirani ya fada min cewa naje gareku insha Allahu zan dauka iyalina muzo mu ganku. Kada kayi amfani da fadan mutum watau camfi ban faye yarda da abinda mutum dan uwana zai fada min ba duk da nasan asiri gaskiyane don anyi min akan rabon samunka naje da kafata har garin mahaifiyar ka na zauna har mukai aure da ita aka sameka. Amma duk da hakan ban yarda da cewa wani yai min ba na dai dauka cewa rabon kane kawai yasa nabar gida na bar gatana da kowa nawa zuwa wanan garin don haka ka cire fadan mutum dan uwanka a zuciyar ka. Zan shigo saidai ba yau ba Abba ya fada a dan sanyayye kafin mahaifin yai magana yace dama dalilin haduwan mu yau shine don in tambayeka don Allah ko kasan buba Bande dala ? Ko hardo Dala Banden a baya can wani irin kallon mamaki mahaifin nasa yai masa don koshi a yanzu ba zai iya bada labarin wanan mutumin ba saidai yasan dan uwansa ne na jini daya bata tun suna yara suma. Kaiko baba a ina kasan Dala Bande mutumin daya bata ko ya mutu tun muna yara kwarai kuwa na sanshi amma ba sosai ba don shine wanda rabin dukiyan mahaifiyata take hannunsa. Amma tun bayan rasuwan mahaifiyata muka daina jin labarinsa kwata kwata mutanen garin muma cewa sukayi ya mutu a lokacin baya raye. Bai mutu ba Abba yana da rai saidai baya cikin kasan nan yanzu yana wani gari a can cikin benin republic zaune shi da iyalinsa ya fada min duk ranan da muka hadu in maka wanan tambayan kuma in fada ma inda yake zaune. Ya kumace na isar mai da gaisuwana a gareka in a fadama komai na nan yadda yake saidai zuwa gembo ne abu mai wuya gareshi don magajiya ce silar komai. Babana Dala bande fa kace ka hadu dashi har ya baka wanan sakon yace kwarai kuwa Abba shine ma dalilin dayasa na tsaya na ganka a yanzu don in sanar dakai sakonshi don nayi alkawarin hakan gareshi. Hulan kanshi yaga ya cire yana fitara dashi yabi mahaifin nasa da kallo mamakin hakan kafin ya dubi lokaci agogon hannunshi yace Abba ni zan koma don motan dare zanbi na koma yau din. Kai ya dago da idanuwanshi da sukai ja lokaci guda yace zaka koma amma kuma ba yau din da kace ba a matsayina na mahaifinka na bada umurnin hakan gareka. Zanso mu zauna dakai yau da dare ka fada min komai game da Dala nasan in har dalane ko wani ne yake son yimuna wasa da hankali a matsayin sunan Dala din don ba karamin labarin daya taba min zuciya bane ka kawo min game da wanan mutumin da aka dade ana nemansa an rasashi. Saboda haka ka koma masaukin ka ba zan matsa maka sai kazo gidana ba tunda baka tashi hakan ba amma ni zanzo har masaukin naka da yamma in sameka idan na taso daga office. Yana fadin hakan yaiwa security dinsa hannu a take suka shirya da sauri suka shiga mota shima ya shiga nan suka barshi tsaye yana kallonsu. Nabil ne ya dafashi har lokacin a cikin mamakinsa yake yace wai dama mutumina kai dan wanan mashahurin mutumin ne ko garin ku dayane kawai dashi. Amma kuma zanfi gaskata idan kace min shi din mahaifinkane don yawan kaman da kukeyi dashi gaskiya ban taba sanin cewa kai din kana da halaka da mai kudi irin haka ba a cikin garin nan. Muje gida kawai in dauki kayana ka kaini tasha ya fada Nabil din ya kalleshi yace muje sun fara hanya yaji yace alama ya nuna akwai takon saka a tsakaninka da mahaifinka ko ? Bai bashi amsa ba sai hannu daya dora a gefen glass din motan yana kallo titi saidai a can kasan zuciyarshi yana tunanen me yasa mahaifin nasa ya gigice game da zancen wanan hardo din Dala. Sama sama yaci abincin kafin ya mike da zuman su tafi koshi don mahaifiyar Nabil dince data matsa akan sai yaci abinci zai tafi Nabil din yace bari a kira momi kuyi sallama. Duk yana ganin nawan da Nabil din ke masa don yasha alwashin bai kara kwana a garin duk da karfe hudu har ya buga gashi biyar akace mota yana tashi zuwa zamfara na yamma. Shigowan mahaifin Nabil dine da sauri ya dakatar dasu yace badai tafiya zakayi ba Ahmed yace baba na gama cika komai yanzu nake son in tafi nagode da irin dawainiyar da kukai mani. Dakata Ahmed ina yabon kirki da hali irin na dattako
Chapter 242 · 0% Book details