Sashe 107
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kuma suna zaune kamar wasu yan kauye dole na koma saini ke kula dasu a lokacin. Ina nan zaune wurin su duk da hankalina yana kan waya amma ina sauraren hiran da sukeyi jefi jefi wanda gulman mama sukeyi kan cewa wai mama ta nuna bakin ciki da zuwan su a fili. Naji gwaggo shafa tace ai ba zamubi ta nata bamu don dan dan uwanmu mukazo ai ba don wani abu ba shi ya nuna yana son azo ayiwa matarshi kara a nan. Duk ina jinsu suna dan hiransu jefi jefi kawata maryam dana samu a nan yar yar mommy da muke kwana dakin tsohuwar a tarece ta biyoni. Kwance ta sameni a daidai kan gwaggo shafa saidaini ina saman digon kujera a kwance da wayata a hannuna ina duba. Take fadin au nan kike kinga yan garin ku yau kin manta damu ki tashi muje mu shirya za a tafi wurin kauyawa da andawo za a fara shirin dinner kuma . Kafin nayi magana gwaggo Ai tace keko taga uwayenta ai dole ta dawo wurin mu ta zaunamana wa take dashi nan wanda yafimu ai zamanta yayi rana garemu nan tunda ita karima bamu ganta ba tun dazun . Suna can sun tafi gidan da za akai amaryan ne amma zasu dawo yanzu ai tunda zasu wurin wasan suma maryam ta fada. Mikewa nayi na fara fita bayan nacewasu gwaggo su shirya muje can mu hadu da mommy din a wurin sukaji dadin hakan suma nan na barsu sun fara shiri. Wanka na fara shiga nayi na fito na samu maryam tana shiri take fadin wai wanan ne za a saka a wurin ni sam bai mun ba wallahi. Ai kinsan anko ba sai ra,ayinka ba abune na kowa don haka ko bai maka ba saikayi hakkuri ka saka a jikinka kawai hakane ta fada balle kinsan duk wanan kayan ai mommy kice ta zabosu can Abuja . Kinsan ita tanada wani ra,ayi na daban dake hadasu da yan uwa halan ku baku gama sanin halinta bane a gidan ku ? Don itafa mama karima idan ta zauna a wuri dolene a bita ko kuma ta hada mutanen fada ko tasa dole ku tsani juna a tsakanin ku . Bari kawai basai na fada maku halinta ba kuda kanku zaku sani nan gaba don duk wanda yayi kokarin nuna cewa ya fita nan take zata tsaneshi. A yanzu duk amfani takeyi daku hakan dole tana da wani manufa akan ku da takeson ta aiwatar nan gaba don haka take kwanta maku a yanzu. Shigowan dayan kawarmu dakin yasa tayi shiru ga abinda take fadi din a lokacin don kada wanan din taji me muke fadi a lokacin. Niko da tasan halinda zancen ta ya sakani a lokacin da bata fada min wanan zancen ba gaskiya don gaba daya hjy karima ta fice min a rayuwana harma na koma tsoronta ko a lokacin. Haka muka shirya da kyar na samu motan daya daukemu tare dasu gwaggo zuwa inda ake kauyawa din har mukaje muka dawo nice ke fama dasu lokacin. Sai dare mommy ta dawo lokacin har an fara shiri wai zuwa wajen dinner da za,ayi a ranan saidai banda niyar hakan don na fadawa su maryam cewa ba zanje bani saboda dare . Don haka tunda naga su gwaggo sunci abinci sun kwanta a inda muka gyara masu nida maryam na dawo na kwanta abina a dakin tsohuwar nan. Bayan mommy ta dawone ta samu sun kwanta take fada don me zasu kwanta a falon ni ina ina dana barsu a nan kwance gwaggo shaface tace aiko tayi kokarinta damu. Don ko nan din ma itace ta gyara muna muka kwanta to ai sai ku tashi muje wurin dinner ta fada da sunso suki amma kuma suka shirya suka tafi. Basu dawo ba sai karfe daya da wani abu na dare kowa ya samu wuri ya kwanta maryam ma bansan dawowanta gidan ba lokacin don na dade da tin barci ko ni.