Sashe 245
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun wanan tafiyan uwar garke bata dawo gidan ba ta bata amma ina jin Ahmed kafin ya tafi yana fadin nasan uwargarke sarai zata dawo garemu komai dadewa don haka Dije ki kwantar da hankalinki don Allah. Nakanyi mamaki haka tayaya akuya ta bata tsowon haka kuma ace ta dawo wanan kan ai karyane shirmensa kawai yake fadi don ta kwantar da hankalinta saboda tsohuwar ta damu ainun akan batar akuyan har yar rama tayi. Bani kadai ba ko innan shi da kannensa idan yace zata dawo mukan masu dariyane mu nuna ai ta tafi ke nan don ba wanda zaibar akuya kamar wanan idan ya gani. Har dai lokacin tafiyan master yayi wanan akuyan bata dawo ba muma sai zancenta ya fita a kanmu saidai idan mun tuna mukanyi hiranta wani lokaci. Mai karatu na bar maki zance baya akan yadda muka kwashe da mama da yaranta a gidan mu don na kwana biyu banje gida ba saboda bin umurnin ummah da nakeyi da tace bata son yawan zuwa gida gareni. Bamu hadu dasu irin haka ba sai wata rana da muka hade a family house din mu da akai rasuwa wata diyar baba harun ta rasu a wurin haihuwa sai akai sa,a koda naje gaisuwa suma alokacin sukazo nan muka hadu dasu. Bayan mun gaisa ne na shiga da mutane na dawo dakin hjy inda suke muka gaisa na danyi wa kaina mazauni daga gefen su zakace ba asalin mu daya dasu ba yadda suke jan kamshi a lokacin. Suna ta hiran su kamar ba mutuwa akayi ba a gidan akazo gaisuwa ba waike har yanzu dai shiru bamu ga gaskiya ba Rukkaiya ta fada tana kallona nace gaskiyar me kuma Rukky ? Mijim ki mana da akace ya samu aiki a kasan waje kuma mahaifinshi mashahurin mai kudine Abuja duk ashe zukece don aji dadin bakine tunda ba alaman komai ga zahiri. Na rasa meyasa mutane basu kunyan karya ko in kayi karya ka zamawa oho ji yadda aka zauna aka shirya karya a lokacin babu ko kunya ba tsoron Allah sai kace kowa dolone da zai yarda Aishace ta fadi hakan. Kai yaran nan da shirme kuke kun taba jin an canzawa tuwo suna ta yaya mai hankali zai yarda da wanan karyan idan an fadi hakan ba an dauka mutane zasu raja,a suce gaskiyane a fara masu wani sabon kallo babba ma yayi karya ina ga yara mamata fada. Fadin hakan da mama tayi yasa na gane abinda suke nufi watau ummah sunyi karya ke nan a kan mu don su gyara master a wurin mutane don kawai a dauka gaskiyace yana da asali. Wai wa ake zancene haka hjy tsohuwa ta tsoma baki a lokacin sai Rukkaiya tace a,a mijin Zahra dai da akace wai ya samu aiki kasan waje nake tambaya munji shiru har yanzu bai tafi ba ? Ke nifa ba wanan karya ya dameni ba sai cewa da akayi wai dan shararen mai kudineshi magana ba ko kunyar fada sai yanzune ake neman uban lakaka mashi daga sama kuma don gyaran zance. Ai bansan lokacin dana bude baki nabawa mama amsan hakan data fada ba saboda bacin rai tana kokari tace ummah ce munafuka tayi wanan babatun don ta gyara surukin ta yasa idona ya rufe nace dasu. Saukin abin dai duk garin nan kowa yasan Ahmed yana da ubansa dama shidin ba shege bane da ubansa nisa ne ya rabasu yake nan don haka babu abin mamaki don ace yau ga uban nasa yazo gareshi. Ra,ayine kawai irin na Ahmed yake zaune a nan saboda kakansa amma idan karyane lokaci shi zai nuna kansa karya kuma ai ba kaina aka fara ba don wasu sunyi fiye da hakan bai zama komai ba har yau kuma suna zaune a cikin gari ba wanda yai masu maganan rashin bin mijin da akace zasuyi idan anyi aure zuwa wani gari. Ina wuta su sakani su hudun har hjy sukayo kaina lokaci guda nan gidan makokin ya koma gidan fada wuri ya kicime ni kadai su da makaraban su a lokacin. Kai kai kai wanan abin kunya har ina ko wani haduwa sai ku takali boyar Allah nan ita tana lamarinta bata sakaku ba amma ku kun sakata da laluranta gaban ta. Shekaran Jiyan nan fa mijinta yazo ya sallami Alh cewa zai wuce kasan waje amma zai bar zahra garin nan har ta karasa karatun ta idan ta gama zasu koma Abuja gidan mahaifinshi gaba dayan su shine yazo ya fadawa Alh. Inko haka ba gaskiya bane zaizo har wurin Alh ya fada mashi haka a matsayin shi na ubanta da yake dauka tunda shine madauri aurenta ku rika magana kuna taunawa don Allah wanan matar baba Ado din In kin tuna ta ranan data basu amsa asibiti itake wanan jawabin. Aikin banza ya tafi din mu gani mana don an fadi shi zaisa mu yarda sau nawa ake irin karyan nan karya dai aiba kan mu bane farau na kara fadawa mama aiko su Aisha suka taso min kamar zasu cinyeni danya saida su gwaggo suka fita dani ina kuka don takaici. Um,humm ke meyasa zaki biye masu ku zubar da hali ummah ta fada dana gama mayar mata da yadda akayi in su basu san me sukeyi ba kema baki sani ba ke nan. Kuda kukaje wurin gaisuwa zaku tsaya kuna zubar da hali a bainar jama,a ana maku dariyan ga marasa hadin kai da wauta don Allah niki rufa min baki ta fada tana kawar da kai. Nima dai kuka nake saboda abin ya bata min rai sosai a lokacin yasa nake kukan bacin rai haka gaban mahaifiyata din sai kuma can naji tace cikin murya mai taushi. Ke mahmaah baki ganesu bane har yanzu dan hassadansu su a fili yake ala dole dai kada mu kai inda suka kai har ace zamu fisu wanan kuma yana hannun Allah ba mutum ba. Uba dai basu isa su sake mai ubaba shi din dai wanda basu son ya zama uban nasa shine dai uban nasa haka kuma daukaka yana hannun Allah ke kinsan da a hannun mutum yake daba haka ba. Kwarai kuwa tani dake aje kayan abinci ta fada basu da hankaline na a matsayin mahaukaciya nake daukan hjy yanzu a gidan nan inba hauka ba wanan maganan abin fitarwane har duniya tasan manufarki akan yar kishiyarki wanan ai gazawa ne da abin kunya kice na fada watarana sai kinji wani can yana saka mata magana kan hakan. Nifa ba wanan ba wai ace hjy tsohuwa duk zance ya taso sai ta nuna min kamar ni barece ba jikanta nake ba dariya naga ummah tayi lokaci guda dana fadi hakan. Ke barece mana tunda mahaifiyar ki barece a cikin su ai haka hjy take kowa garin nan ya sani tashi don Allah ki shiga ki gyara fuskan ki kada su dawo su sameki haka su dauka sunyu galaba akankine sake jiki ki nuna bai dameki ba tani ta fada. Yau sai gashi master yaje yayi masu sallama har dakin mama yake ya sallameta ya bata dubu hamsin ya fito abinda ya gigita mama ke nan wanan kudin daya bata din don haka ta rude tana maganganu bayan fitanshi gashi anyi sa,a duk yaran nata suna gidan a lokacin. Master ya tafi ya barni gusau tare da iyayyenshi duk da a lokacin ba walwala amma ba laifi don ya bar muna abincin da zai kaimu tsawon wani lokaci. Ga kuma karamin ciki a jikina dake wahal dani wanda duk bamu san ciki bane a lokacin mun dai dauka mutanenane suke damuna ashe cikine a jikina Allah ya kawoshi lokacin ba a sani ba. Ina faman laulayi ga kuma jerabawan da nakeyi Allah ya taimaka har na gama ciwo yakici yaki karewa ba barci sai hamma da hawaye kawai nake aikin yi. A wani asuba da ciwo ya isheni ne na dauko wanan maganin daya kawo min na shaka a hancina na kuma shafa a jikina ko ina sannan na samu sauki har dan barci ya zo min a lokacin. A nan nayi mafalki da akuyan nan uwar garke tana fada min wai haba dai godiya kin dauki jinjiri mai karfi kuma ki zauna kina sakaci haka bayan kinsan kina da makiya ta ko ina. Zakuje asibiti yau kada ki yarda kiyi allura haka kuma innan ku zata kawo maki magani a yau din kada ki yarda kisha maganin nan ki daitayin wanan hayakin kina fasa kwan tumfafiya kina shaka sai kin kai wata takwasa ki daina hakan Allah ya raba lafiya ta bace a cikin wani irin haske dana gani. Zubur na falka tare da mikewa lokaci guda ina dan waige waige a dakin ranan kuma dagani sai Aisha muka kwana don Asmau tace gaskiya bata iyawa ita. Hakan yasa na mike cikin karfin hali na nufi bandaki na kewaya duk nayi zuba don haka na watsawa jikina ruwa na hado da alwala na fito. Har aka kira sallah ina zaune a inda na samu nayi nafila a cikin karfin hali na dan jingina kaina a saman gadona don in samu sa ida aka kira sallah asuba nayi na kwanta a wurin. Kwalon tumfafiyan da tace na samu na dinga mafalki dashi yana min yawo a sama zubur na sake mikewa dije zaune a kaina take min sannu ganin na falka tace mijinki ya bugo waya yace zakuje asibiti yau da mahaifiyar ki tana nan tafe ku tafi. Dije ki debo min kwallon tumfafiya don Allah na fada a wahalace cikin mamaki tace kwallon tumfafiya kuma nace eh dije don Allah yanzun nan tace amma dai kinsan ba a cinsa ko ? Eh na sani a debo min dai tana fita inna na shigowa da ruwan magani a kofi yana tururi da gani lokacin ta sauke shi a wuta ta debo min tace gashi ance da yayi sanyi ki kafa kai kisha da dan duminshi . Gabanane ya fadi don tunawa da zancen mafalkin da nayi da asuba din na karba na aje a gefena sai naji tace kawo dai na fifita yayi sanyi lokacin dije ta shigo da kwallon tumdafiyan a hannunta zasu kai biyar da sauri na karba daga hannunta . Jikina rawa na bare na fara ina dagawa