← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 249 OF 286

Sashe 249

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a baya saidai a lokacin dagasu sai diyansune a wanan irin zaman sabanin yanzu da suke da bakin fuskan da suke gani a cikinsu. Wanda ba kowa bane sai hjy murja da yaranta biyu da take riko a yanzu a hannunta wanda hjy yabi take gani da sun mata kutse a rayuwanta dana diyanta don ganin hjy murja din takeyi a matsayin yar ci rani a cikinsu tazo zata koma. Daddy dinne ya fito daga part dinshi dama kusan ko yaushe shike karshen fitowa gashi anyi sa,a kowa na gidan yana nan don har kananin sun samu hutu sunzo a lokacin. Yar computer yake kokarin dannawa har ya kai zaune suke gaidashi yake amsawa kafin ya dago yana fadin mustapha bari na faral gaisawa da babban yayan ku ko ? Muji lafiyan su nasa dana iyalansa a cikin mamaki yaron daya kira da musty din ya dago yace wa,wooo daddy big brother kuma bayan ya Yasir akwai wanine ? Kwarai kuwa first son dina Ahmed mai sunan dad dina yanzu yana aiki a America shine zan kira ku gaisa dashi a karo na farko ya kamata ku sanshi ko ya kalli yaron sai yaron ya dan daga kai yana mamaki. Hello Abba an wuni lafiya yaya aiki ya iyali lafiya kalau muke baba karami ya can ya naka iyalin kuma ya dan sosa kai yace suna lafiya Abba. Ga brothers dinka zaku gaisa dasu yau don kowa na gida a yau mun hadu wani iri kowansu yaji a lokacin cikin ransa Ahmed din ya gyara yace OK cikin nuna rashin damuwa. Yasir kazo kusa ku gaisa dashi Abban ya fada kamar ba zai taso ba sai shi karamin yace bani mu gaisa daddy ya leko kai don ganin fuskan sabon yayan nasu da mahaifin nasu ya fada. Yace wonderful wanan ai kamar kai daddy hakan ya kara tarwatsa zuciyan hjy yabi dake zaune a gefe takai iyakan kuluwa da zancen mahaifin nasu wai yau ita ake fadawa wani zancen dan uban diyanta a gabanta. Dan uban kuma har yakai matakin da taron gabansa a yanzu sai tayi aiki sosai kafin ta shawo hakan don ya riga har ya taka kasa ya wuce tata a wurin ta a yanzu. Look alike wanan ai photo start din daddy ne aje yasir da bata san yakai wurin ba ya fadi hakan tare da dagawa dan uwan nasa hannu yace hey shima ya dago yana fadin sallamu alaikum. Saman karamin table din gaban shi ya aje na,uran suna zuwa daya bayan daya suna gaisawa dashi tare da fada mashi sunan su yana furta masha Allah shukuran. Har yakai hjy murja da kowa na falon in ka debe hjy yabi dako motsawa batayi ba a inda take din zaune don firgita saboda bata taba sawa a zuciyanta akwai irin wanan ranan tafe mata ba. Muryan shi radau a cikin nauran yake fadin ina mama firgigit ta dawo da hankalinta tana kallon na,uran yaji sunce gata zaune aka juya fuskan computer a wajenta . Hannayenta ta matse lokaci daya a jikin kujera don firgita da irin kaman data gani yaran na fadi ta dauka kamar wasace sai ga idonta ya gano mata zahiri ta gani itama. Lalai kan idan rana ya fito tafin hannu baya rufeshi don tayi sake dan zaki ya girma bata iya taronshi a yanzu don wanan matashin akwai baiwa a tare dashi wanda ya hasaka kuma taga hakan a fuskansa yanzun din da suke waya. Mama kuna lafiya ya family sannu da kokari ya fada a cikin waye kuma kai tsaye yana sake murmushin da take ganin barazane yanzun a gareta kai tsaye. Suna gama gaisawa shi da kansa yace bye Abba i will call you letter in the night see you guys ya kashe na,uran wayan dip lokaci guda. Falon yayi tsit kamar ba mahakuki a cikinsa sai zuwa can hjy murja tayi karfin halim fadin kai amma gaskiya Alh kamar ku dashi har ya baci da ganinsa ba sai an tambaya ba don ba inda ya rageka haskene kawai ya dan daraka dashi yanzu. Sai ko yawan fara,a don yafika sakin fuska da alama shima yana da saukin kai sosai Dad amma baka taba fada muna zancen shi ba ki sau daya. Ko yanzun ne din ya zama danka kaima kasan dashi Salima ce me wanan tambayan daga inda hjy yabi take zuciya yana cinta tace kuma dai kwa tambayeshi hakan don da dan halak ne da kowa yasan shi tun farko ai. Keee ya fada a cikin wani irin tsawan da duk basu san yana da murya haka ba ga dan yatsan shi daya daga ya nuna mata a makale ya kasa saukewa haka kuma banda kalman ta ke ba abinda ya iya yi a lokacin sai hannun dayake nunawa matar tashi. Kada yatsan ya farayi yana carstinel da ita tana bada sauti kas kas kafin ya tsayar ya kara nunata ya juyo da yatsan yana nuna yayanshi kana ya dawo da hannunsa kan hjy yabi din yace duk daya suke da wayan nan. Na fada maki duk daya yake da wa yan nan yadda aka taru aka daura auren ki har kika haifa min yara gasu haka aka taru aka daura aurena da uwarshi har muka sameshi . But daddy as how ita mum din nasa bamu santa ba kuma bamu taba jin labarin hakan ba don ace muna mun ce first wife dinka ai ga wanan kace ya girmeni kuma. Good question zan dan fadama yanzu abinda nake son ku tambayeni ke nan tun farko zan fadama in brief saura kuje gun uwarku ku tambayeta dalili itake da amsan hakan. Falon yayi tsit yace anyi wani lokaci da wasu azzalumai sukai min asiri na bar gida na bar iyayyena da dukiya don kawai suna son su mallaki dukiyan nawa da Allah ya ban ta hanyat gada a wurin mahaifiyata da itama kamar nine gada tayi gun nata mahaifan da tazamo ita kadai a wurinsu. A wanan lokacin na shiga duniya na nufi garin illorin nabi motan masu kai shanu a can a illorin din na danyi shekaru biyu a can ina aikin shanu nasha bakar wahala gani da kwazo da iyayyena suka samu labarin inda nake suka biyoni na samu kabarin zuwan su . Shine a ranan nagudu nabi wani Alh dan Zamfara da mukai sabo dashi idan sun kawo kaya shi nabi zuwa garinsu a cikin babban motarsu na katako da ake kwasan kaya dashi har zuwa gusau da yanzu ake kira da zamfara. Shiya zama uban gidana a can har ya tsaya min akai aurena da wata yarinya mai tallan kunu a wurin mu itace mahaifiyar Ahmed shekaran mu biyu da rabi da aure Allah ya bata cikin Ahmed. Mahaifina kuma bai zauna ba suna magani sosai kuma sun rike min amanan dukiyana sun hana wa yan nan azzaluman tabawa da sukaga haka shine suka kara yin asirin da zan dawo gida. A daidai lokacin haihuwan Ahmed lokacin asirin ya kare a kaina naji gida kawai nake son zuwa a lokacin ji nake kamar wuta ake saka min a zamfara din. Naso nazo da matata nan mambila ita kuma sai iyayyenta suka kafe bazasu bani itaba zuwa wuri mai nisa a lokacin shine suka sa na saketa duk muna son juna a lokacin tun wanan tafiyan ban sake ganin shi ba ko tunawa dashi . Saboda wa yan nan azzaluman da suka sake plan a kaina suka mantar dani wanan yaron suka makala min son su suna juyani yadda suke so akan abin duniya. Sai gashi Allah da ikonsa a yanzu Allah yayi shidin rayeyene ya girma ya nemoni lokacin har yayi aure yana aiki yanzu a America ne acan kuma yake zaune tare da iyalanshi. Kai kai kai Dad su waye wa yan nan azzaluma gaskiya sunci akai gaban alkali ayi karansu wanan zalunci yayi yawa dad da zan gansu dani zan hukuntasu da kaina don suncuce ka dayawa. Kallon hjy yabi yayi tare da alama da hannu kinji ko daga bakin diyan cikinki caraf a idon hjy murja ya dan share hawayen daya gangaro mai a fuskanshi ya mike tare da fadin zan shiga inyi alwala sauran bayani anjima mu hadu.
Chapter 249 · 0% Book details