← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 286

Sashe 80

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Enough Ahmed enough ka dauka cewa ba maiyiwa wani sai Allah a rayuwa bayinshi anyi hakan ne don aga an hanani farin a rayuwana ko uwata tayi baki ciki kamar yadda akeson ganin mu kullun. Abu daya na sani na kuma rike har in ina son kane da gaske ba wanda ya isa ya hana wanan a tsakanin mu don kawai kai din baka nuna hakan bane na kuma san bashi mukeyi ba mutuncine kawai. Naja bayane kuma don nasan Abba ya saka muna ido don kada najawa rayuwan ka matsala kana gab da gama karatun ka a yanzu din don hakane banson najawo maka matsala. Murmushi naji yayi kafin ya sauke wani ajiyan zuciya da har nake jinshi yace zahra banda wani matsala indai a kankine duk abinda Abba zaisa amin idan har zan samu zuciyarki na dauki hakan a mukadarine a gareni kan samun ki. Idona na lumshe ina jin wani iri a zuciyana yaci gaba da fadin tsorana daya a yanzu shine kada na nace akan abinda zan dawo ina wahala daga baya kanshi ya kasance cewa ke baki min irin son da nake maki a zuciyana . Har yayi ya gama ban samu bakin fadan komai ba ina dai sauraren shi ga hawayen daya wanke min fuska ni kadai a daki ina tunane saida ya ji shirun yayi yawa yake fadin kina jina zahra ? Hello Zahra kina tare dani kuwa ko kin daukane na amsa da ina ji Ok kin fahinci me nake nufi kiyi hakkuri da hukuncin Abba a kan mu ba sai mun hadu bane alakan mu zai daure dake matukan waya yana aiki zamu iya gaisawa har zuwa lokacin da kika shirya hakan jin nayi shiru ba amsa yace Kina jina zahra nace naji idan mun hadu zamuyi maganan sai anjima na kashe wayan yabi wayan da kallo na dan lokaci kafin ya aje ajiyan da dan karfi ya fara kokarin tura wayan cikin aljihun shi. Daga kai yayi ya kalli hanyar daya ratsa ta gaban gidansu sai yan mutane dadaya ke wucewa a lokacin hakan yasa yasan dare ya fara dan nisa ya cire kafa ya daga da niyar shiga gida a lokacin Dije data gaji da zaman jiranshi ta leko daga cikin gida suka hade. Amadi lafiya yau kakai wanan lokacin baka dawo gida ba tana tambayan shi cikin nuna damuwanta gareshi a lokacin. Yanzun ba gani ba Dije, na dan tsaya yin wani abune a nan waje ai tundazun ina kofan gidan nan bandai shigo bane ciki ya bata amsa yana skn su shiga cikin gidan nasu. Amadi Dije ta ambaci sunanshi a sanyaye ya juyo yana kallonta tare da fahintar akwai wani abinda ke faruwa da tsohuwan zomu shiga ciki yace da ita ta fara takawa zuwa shiga cikin gidan nasu tabiyo bayan shi a baya. Kayan daya dauko ya fara ajewa kofan dakinshi kafin ya dago ya dan duba bayan shi har lokacin Dije tana biye dashi kamar jela. Muje daga ciki yunwa nake ji Dije banci komai yau tun wayewan gari sai kunun tsamiya danashi kafin na shiga makaranta. Da alama yau akwai abinda yasaka nishadi Amadi don na dade banganka cikin wanan yanayin haka irin na yau ? Kuma dai ya fada yana zama daga kofan dakin Dijen tace barin dauko ma abincin kaci saidai yayi sanyi yanzu don tunda sauran rana na girkashi na zata zaka dawo da wurine ai na dafa a cikin lokaci. Bani hakana inci ya fada yana kaiwa zaune a hajiye ra shiga daki can ta fito dauke da kwanon tuwo dana miya dagware da juna ta aje gaban shi kafin ta nufi wurin randan ruwan su ta dabo mashi ruwan sha. Hannu ya wanke kafin ya bude kwanon da yar hasken wayan shi yake amfani a cikin duhun ya gyara jawo kwanon kusa dashi yana bissimillah ta kai hannu ya yanki loman tuwon yakai a bakinshi. Tuwon farar shinkafa miyar shuwaka data daure da kuli kuli sai dan manshanu da tayi amfani dashi ya ba miyan ma,ana don babu wani wadataccen kayan hadi tankwana busashe sai albasa da dan manja ta hada miyan dashi sai kayan yaji da daddawa da bussashen kifi. Loma kamar uku yayi Dije din tace dashi yau na nemi uwar garke a gidan nan na rasa tun bayan fitan ka nake yawon neman ta ban gata na kewaye unguwan nan kaf babu labarinta . Haka har kudi naba yaron nan dan gidan malam sule duk basu ganta ba hannu ya tsame daga cikin abincin yana kallonta cikin mamaki don jin abinda ta fada din. Yayin da gaban shi ke wani irin faduwa na tashin hankali dakyat ya iya budan bakin shi yace garin yaya Dije har ta banye ta fita ba a sani ba ? Shine abinda ya daure min kai nima ai don naga dabbobin nan basu fita ko ina a gida suke kiwon su yadda na saba masu nakewa bandaki ina fadin in fito in zuba masu sauran kowan wanken nan daka sayo masu. Fitowa na naga wayau sai sauran bisoshin ke tsaye tsirma tsirma kamar suna cikin tsoro a lokacin hankan yasa na gane akwai wani abinda ke faru saina duba bata cikin yan uwa ga igiyar ta na dauri a yadda yake amma banda ita. Uwar gareke ta bata kuma ba a ganta ba to ina ta shiga ko kuma waya shigo gidan nan ya banye ta daga dauren da take din ya fada yana rufe kwanon abincin lokaci guda tare da mikewa tsaye.
Chapter 80 · 0% Book details