Sashe 101
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ladabi to mike ki fito waje mana cikin mutane ki zauna kin kunshe kai a daki ke kadai kamar amarya. Ko wurin kawar taki ba zaki fito ba kya zauna ke kadai ina abune a waya aina fita na dai dawone na fada ina ita maryam din ? Wace maryam na tambaya cikin alamun rashin ganewa wace kuka kwana a nan tare oho ta fita dazun na bata amsa. Taso muje ta fada ta juya tana fita daga dakin na mike don dole nabi bayanta wacan dakin da muka fara sauka muka nufa da ita na zauna a nan wanka mommy din ta shiga ta fito duk ina zaune saman gadon na dan kishingida a lokacin. Hankalina yana ga wayana ina duban sakonni wanda ya waci da yan course din mune nake charting don banda wasu abokan kirki da zan rika hira dasu. Muryan mommy ne ke fadin anjima za aje kamu na fada maki kayan kamu wanda mu zamusa yan gidan ango jin hakan yasa na dago kai na amsa mata. Ta shiga ta fita a dakin har yamma yayi aka fara shirin fita zuwa wurin kamu din lokacin na mike na koma dakin hjy inda kayana suke yanzu tana falo na gaida ita na shiga. Nan na samu wanan yarinyar maryam tana shiri itama duk da nasan zata girmeni gaskiya ko ba a fada ba na shigo banyi mata magana ba bayan sallama na shige ban daki dan ruwa kadan na samu a ciki saidai hakana nayi amfani dashi ina tsanda na fito . Falo na nufa na tambayi wanan matar ina kwatance sai gata ta shigo dakin da gani irin matan unguwar nan ne dakan dafa wani su samu inda zasuci abinci suma a cikin rufin asiri don yadda naga tana aiki kuma ana sata yi da wasu aike haka. Bayan mun shigo daga ciki nake fadin kin gane dakin nan nake son a wanke robobin ruwan nan a dinga saka ruwa ko wani lokaci don Allah. Wani kallo wanan maryam din ta jefoni dashi amma tana ganin na jawo jakka ina fadin don Allah koda wanine ki saka yayi muna hakan ga wanan kiba maishi don Allah a bar barin ruwa yana katsewa a ciki. Godiya matar ta fara tana fadin ai angama yarinyar arziki kada ki damu da komai baki jin babu tunda kema kina bayarwa ai har abinda bakice nayi ba za a dinga maku a dakin nan insha Allahu. Matar ta juya ta fita tana godiya ina jin muryan hjy mai dakin tana tambayan ta tana fada masu yadda mukayi naji tsohuwar tace ai tayi maganin ku shine daidai daku. Tare dasu mommy karima zaku fitane naji muryan maryam din dake ji da kai tana ganin tafi kowa a dakin ta fada na dauka waya takeyi yasa na shareta. Dake nake nace da su mommy zaku fitane ko mu fita tare don ni ba wai nasan su bane sosai nace ayyah wallahi ban sani ba gashi dai ina shiryawa . Maryam din ta fara saka kaya a jikin ta kafin in saka tana wani zuwa tana dawowa tsakanin falo da dakin kafin nima na saka kayan na fito shar dani a cikkn tufafin. Zuwa lokacin kusan duk wanda ke gidan ya saka ankon shi a jikinshi ana fita waje mommy ce ta shigo dakin da sauri tana fadin daughter kin gama shirin kuwa ? Eh mommy nagama mama ai tare zamu tafi maryam din dake saka wani abu a jakkarta ta fada sai naji mommy tace shike nan ma da kunsan wuri sai nace a baku key kuzo tare da angone kuma ku shiga cikin su. Wa zaija motar maryam ta tambaya naji mommy tace zahra mana wace keda mota babba na shiga wurin milayan biyu da rabi naji ance bayan wanan ma kina da wata ko ? Na dan gyada kai a hankali yarinyar ta kara kallona cikin mamaki mommy dai ta juya tana fadin barin gani ko za a iya yin wani abu ta fice daga dakin kai tsaye . Sai zuwa can mommy din ta aiko wai mu fito mubi wani usman a motanshi driver ya fita da motan da take son mu shiga din. Ba ruwana don haka yadda sukace zanyi don duk a takure nake zaune dasu mun fito din wani guy ne wace tazo kiran mu ta nufa tana fadin ya usman gasu nan sun fito. Yana magana da wasu ya juyo ya kallemu suma sauran kallon mu sukeyi a dan sama sama muka gaidashi ya amsa yana satan kallon mu can yace kune zan tafi daku ko maryam din ta amsa mashi. Nikan baya na nufa maryam ta bude gaba ta shiga wanan data kiramu itama ta biyo mu muka shiga zuwa wurin taron kan mu din . Wurin ya cika da taron maza da mata ga motoci nan ko ina ka duba anyi decoration irin na gargajiya anko kan ba a maganan shi yafi kala goma da idona ya gani a wurin. Yadda akai taron ya nuna angon dan gatane sosai don yannen nasa naji dashi muna tsaye a bakin motan da mukazo cikin shi don tawagan ango muka biyo mu. Wayana ne yake vibration daga cikin jakata nake laluboshi mommy ce na dauka take fadin kun iso ko nace eh mommy take fadin ki fadawa maryam cewa zaku shigo da angone akwai yan matan da zakuzo a tare din kifayi masa liki sosai a san dakin shigo na danyi murmushi ina kashe wayan. Abinda na kula dashi shine na farko mommy nada son asani sai nabiyu kamar suna da adawa a tsakanin su da yan uwanta sai kuma nayi tunanen ko don Abba ya ban kudin bukine a gaban ta oho ? Mun kai minti ashirin kafin ace mu shiga fili amarya naciki aka bamu hanya mc na shelan fadin ga angonne zasu shigo suyi liki. Kidan ya canza saiga wani da sauri cikin abokan angon na fadin ke dake dake ya nunamu mu hudu yace wai mune a gaba don Allah ace ni cikin mamaki maryam ta tabani na juyo ina kallonta. Alama tayi min da ido nace OK ya juya ya tafi haka din kuwa muka shiga wurin muna gaba sauran tawagan na bayan mu. Sam ban yarda nayi wani rawan zakewaba don dama ba gwanan rawa bace ni din har zuwa tsakiyan taron angon yazo ya tsaya kusa da amaryan shi. Nan wuri ya rude da rawa na fara ja baya kadan na samu wuri na tsaya ina kallon abindake wakana a wurin don babu ma yadda zaka shiga kace zakayi liki ai. Har yakai mc din ya roki mutane da a fita a ba amarya da ango fili don Allah saida kyar mutane suka dan rage wata gwaggonsu ta karbi abin magana tace bata son ganin kowa a cikin fili sai amarya da angonta kawai a fili. Dole mutane suka rage yawa bayani me gamsarwa tayi wanda yasa mutane suka natsu akaci gaba da gudanar da event din. A wanan lokacin da akace yan uwan ango su fito su nuna farin cikinsu ga ango maryam data dawo kusa dani ta tsaya take fadin muje mu dan likawa uncle mu fito. Tare muka shigo duk yadda bakuwa ko bako yake a wuri za ayi saurin gane hakan don daga ni har maryam din bakine dan dama ita wasu sunsan mahaifiyar ta. Amma nikan sai mamare sukeyi a kaina da tambayan yar waye ni din cikinsu ba amsa don basu tambaya kusa da wanda ya sani. Yan dari biyar biyar nake masu liki wanan yasa mc tambayan suna aka fada mai Zahra nan yake ta ambatan zahra Abuja.