← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 286

Sashe 166

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ya samu sosai ni kuma ina aikin girkina inayi ina dan dubashi har lokacin da na kusa sauke girkin nawa din duk yana kwance yana barci son sanyin wurin. Ina mamaki a raina don ban taba ganin shi yana barci ba haka da rana irin wanan ranan don hakane abin yake ban mamaki. Na fada maku ku kwantar da hankalinku indai wanan aikin ne ba a wuce sati biyu insha Allahu bukata bai biya ba irin hakan. Tunda har kunce ya fara kiranku alama ya nuna aiki yana kyau ke nan insha Allahu saidai mu jira muga ikon Allah yanzun kam. Har in bai kiraba yau zai kiraku zuwa gobe da yardan Allah son duk inda yake yanzu shima a matse yake cikin kunci don aiki ya fara aiki a jikinshi sunan Allah aiba wasa bane. Hakane malam musa ai don shine mukazo yanzu mu fadama abindake gudana jn akwai wani sadakan da za a karayi sai mu bayar ayi muna akai. Kai ya girgiza masu yana fadin kwandala naku na fada maku banso cikin zancen nan don nima ina son in samu ladan da zaku samu ga wanan niyar don nima alkawari na daukarwa yaron. Godiya suka kara mai sukayi sallama dashi cike da mamakin shi gashi dai bako a garin amma bai hurda da kowa akace sai makwabtanshi da suke dan gaisawa dasu amma kuma yana da halin kirki. Ba laifi suma basu zauna ba don suna da dan rufin asirin su daidai gwagwado hakana saboda basu zaunaba akwai sana,anyi ga kuma kiwo da suka dukufa gayi har yanzu dama ba a raba bafilace da kiwo. Kamar abin almara wayan Alh jauro ya dauki kara yasaka hannu yana laluben wayan ya duba kamal farko da tafito mai a bakinshi shi Allahu akbar kunga dan halas yana kirana yanzu. Waye suka tambaya yace dangaske wallahi shine ke kirana da sauri dayan yace kaga kada ka nuna mai muna tare don na fahinci baison muji maganan. Ya dauka suka fara zolayan juna da fadin kai jiya da yaukan naci da fari wanan amini yana tunawa dani yace ko yaushe ai ina tunawa daku ban manta da kuba. Jiya muna magana wayan ya katse dan gasken ya fada hakane na dauka aikai ka kashe wayan yace saboda me nidana kiraka zan katse yanzu dai munyi maganan kai tsaye kaji damuwana. Wallahi jauro na fada maka ina cikkn matsala sosai kwanan nan in gajarcema dai wani bakon yanayi ke shiganaga don na kasa fahintar ko wani yarone nake yawan mafalkinshi kwanakin nan sosai. Don a iya tunanena na tuno sosai ko akwai yaron da muka taba zaluntane muna yara ke neman hakinshi a kaina naso ace kana tare da yan uwa a yanzu ko cikin ku akwai wanda zai iya tuna wani abu na kurciyan mu. Jam Jam yaro kuma yaro wa muka cuta irin haka da har zai dinga dawo maka yanzu a rayukan ka kaiko dangaske saidai in wani abokin aikin kane nan ? Abin ya daure min kai sosai jauro naso ace kana kusa dasu bande da Jabbo ko Allah zaisa su tuna wani abin na baya da mukayi. Aiko ina kusa dasu na tashi amma barin samesy in masu bayani sai na sake kiranka yana fadin haka ya kashe wayan. To masu karatu ku farga da iri haka ku kula idan zaki wayan siri ki natsu ki fahinci da wanda kike waya idan abin na boyene kisan abin fada don baki san wanda ke kusa da maishi ba a lokacin. Don hakanne ya kasance ga Alh dan gaske da ace wani abu mai muni ya fada game da sauran da sunji a lokacin sai aka samu ya nuna taimakonsu yake nema gaba daya a lokacin. Jin hakan yasa su jin tausayin dan uwan nasu don sunsan irin halin da yake ciki a lokacin nan sukai shawara kawai su fada mai gaskiya inda Jabbo yace su bari shi da kansa zai mashi magana idan ya bugo. Hakan akayi lokacin da suka idar da sallah la,asarne suka samu wuri a natse suka bugawa layinshi ba bata lokaci kamar yana jiran kiran nasu lokacin ya dauka sai yaji muryan Jabbo a layin yana magana. Suka gaisa akai ya kwana biyu nan yake tambayanshi ko yaji sakonshi wurin jauro yace eh shinema dalilin kiran naka yanzu don ka kara muna bayani da bakinka. Yadda ya fadawa Alh jauro haka ya karanto masa shima yai shiru yana sauranren shi cikin tausaya masa sosai a fili sai bayan ya gamane yace dashi ina fatan kana saurarena kaji mezan fada maka. Ni a tunane da kuma abinda muka hango wanan mafalkin naka yana nunine ga danka daka watsar a cikin duniya ko zaka iya tunashi yanzu ? Idan baka manta ba tunda ka barshi ka dawo mambila ban tsamani ka taba tuna wanan yaron a rayuwanka kuma alhalin kasa dankane na cikin ka. Cak yaji kamar ana zare mashi numfashi lokaci guda hankalinshi yana kokarin gushewa a jikin shi a haka wayan ya fadi a hannunshi ba tare daya sani ba.
Chapter 166 · 0% Book details