Sashe 99
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowar Aliyu daga wanka ta sa shi gyara kwanciyar sa ya lumshe idanu, dan ya san yanzu ya tisa shi gaba da sharri kala-kala, ai ko Aliyu sarkin tsokana idan ya so kuma ya zama zaki a sha miskilanci da fara'a a yaren larabcin da suka saba da shi yace "Allah gafarta malam, yau ba za'a fita bane? Ko irin fitar masu mata zaka yi yau? Dan naga ka farka tashin dare alamar an fara kaɗa maka ƙararrawa."
Yawu Jabir ya haÉ—iyi sannan ya buÉ—a idanu a hankali ya tashi zaune, saida ya jingina a gadon ya rumgume hannaye sannan ya dube shi yace" Zan fita."
Aliyu dke neman kayan da zai saka da kulawa yace" Ya kamata dai, dan ka ce sammako zaka yi kaje wajen Abba akan maganar tafiya Agadez."
Shiru Jabir ya sake yi bai ce komai ba saboda tuna masa da wani abu da Aliyu ya yi, Agadez? Wajen su Anna? Hmmmm ! Zai je, ba zai ce a'a ba, tunda Abban shi ya ce ya je saboda Anna da Abbu sun damu zai je, sai dai ba zai taɓa manta wofantar da shi da sukayi ba, bai da laifi, bai taka ma ko ɗaya daga cikin su ba, amma haka suka banzatar da shi ba wanda ya tallafe shi a rayuwa?
Yana cikin wannan tunanin ya ji muryar Aliyu yace "To, ni zan wuce, wataƙila ma yau mu wuni bamu sake haɗuwa ba, dan dukanmu sabgogi ne a gaban mu."
Hannu Jabir ya miƙo masa sukayi musabiha sannan ya furta msa "Fatan nasara."
Murmushi Aliyu yayi yace "Kaima haka." Daga haka ya fice daga É—akin, ganin haka sai Jabir da baya jin zai iya tashi lokacin ya sake komawa ya kwanta, shi ruwan É—umi ma yake sha'awar yin wanka da su, ka ga kuwa da mata gare shi sai ta dafa masa ai. A hankali ya sauke numfashi tare da ayyana _" Rashin mata bai yi ba."_
Gagarumin bacci mai cike da salamar da ya rasa daren jiya ne ya kwashe shi, sai da kiran Abban nashi ya tashe shi kaÉ—ai ya farka, rana tayi fauuu sosai yadda ba ka iya É—aga ka kalle ta, a gurguje ya shirya ya fita daga gidan ba tare da ya bi ta kan kowa ba.
Ƙofar gida ya samu Abban shi tare da maƙocin shi suna hira, ko d suka gaisa sosai Abban ya ƙarewa Jabir kallo, sai kawai ya girgiza kai tare da mayar da hankalin hi kan maƙocin nashi, saida suka gama tattauna abinda ya haɗa su bayan ya tafi sannan ya sake kallon Jabir, cikin nutsuwa ba kuma alamar wasa yace masa "Jabir, za ko ka iya jiran *Kuwailat*?"
Wani irin *rassss* gaban shi ya bada, a rikice ya kalle shi har yana neman sarƙewa yace "Na'am Abba? Ban....ban gane ba?"
Murmushi Abban nashi yayi ya gyara tsayuwar shi yace "Ba munyi da Alhaji zamu haÉ—u ba dama ranar asabar? To ai akan maganar ka da Kuwailat ne, amma sai nake ganin kai kuma kamar..."
Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Kuwailat ? Me kenan Abba ya aikata? Kuwailat ya bashi tun yanzu? Ya gane me yake ji akan ta ne dama? Ya fahimce shi kenan? Kenan dai Abba ya fahimci yana son Kuwailat? Yayin da shi kuma wannan Abban ke neman fahimtar mafarkin da ya kwana yana yi daren jiya? To wai su manya nan.... Maama, it ta sake zuwa masa a rai, kalaman nan nata, sun jirkita masa lissafi sosai ta yadda har yanzu ya kasa gane me yasa ta faÉ—a, sai dai abu É—aya da zai ce yake tunani a kai bai wuce kamar tana da damuwar da Abba ya kasa fahimta ba, shiyasa ma ta zunduma musu kuÉ—in goro duk ta watsar.
Shirun nan ne ya tabbatar ma mahaifin shi da gaskiya ne, inda shi kuma tunanin da yake yi ne yasa yayi shirun, dafa kafaɗar shi yayi yace "Kar ka damu, Abban naka ai mai ƙaunar ka ne da tausayin ka, da ya fahimci hakan zai yi ƙoƙarin kawo maka mafita, yanzu ya maganar tafiya gaishe da su Anna? Da kuma su Mama?"
Sunkuyar da kai Jabir yayi, cikin ladabi da kunyar abinda mahaifin nashi ke ta gani a tare da shi ya amsa da" Abba, duk yadda ka ce, haka za'a yi in sha Allah."
Jinjina kai yayi da jin daÉ—i yce" Shikenan to, ina ga ko zan je islamiyyar su Uzei na nemo mata izini a wajen malamin su, kaga sai mu tafi tare dukanmu ai, dan gaskiya mun jima rabon mu da can."
Jinjina kai yayi yace" Shikenan Abba, Allah ya yarda."
Juyawa yayi da niyyar shiga ciki yna faÉ—in" Mu shiga ciki ku gaisa."
Duk da ba ya ƙaunar yadda matar Baban ke share shi tana hararen shi, amma haka ya bi bayan shi bai masa musu ba, idan da sabo dai ai ya saba ko? Kuma da hakan cutuwa ne gare shi da ya mutu tun yana ƙaramin shi ma.
Rabon ayi ya sake shigowa gidan saboda tunanin ko ta manta ko kuma ganin Jabir zai sa ta yi shiru, sai dai ya manta wacece Bara, tana ganin shi ta taso daga kan kujera cike da hargagin bala'i tana faÉ—in "Ahaf! Dama ba na gaya maka ka dawo ba? Ai baka da inda ya fi nan, to gashi ka dawo ni kuma ina nan kan bakana, babur É—ina wallahi tallahi sai ka biyani, kai har ka isa ka raina min wayo? Daga fita da babur ka dawo ka ce wai wata tsiya an É—auke, to baka isa ba Billahillazi, ka biyani ko kuma kotu ce zata rabani da kai."
Duk wannan abu da take Jabir na kallon ta, takaici na mamaye masa zuciya, tausayin mahaifin shi na sake baibaye shi. A rikice Abban ya wawuri takalmin shi da niyyar ya cakume ta ya gaggaura mata dukan tsiya, da azama Jabir ya riƙe shi...
Wani irin tattausan riƙo ne ya mishi, amma da ya sake ƙoƙarin ƙwacewa dan ya kai ga jikin Bara sai ya ji shi ram a hannun ɗan shi, ya sani dama ba daga nan in dai Jabir ne, to tun yana da shekarun shi bisa kai dama idan yayi niyyar kafewa ba ya iya juya shi, bare yanzu da ya zama bqlagaggen baligi haka, baya ga wannan ai ba zai manta ranar da ya wuntsila shi akan babur ɗin wannan jarababbiyar matar ba.
Cikin nutsuwa Jabir ya juya ya kalle ta sai kuwa faÉ—i take "Sake shi mana, aikin banza, bashi ya zo dan Allah naga me zai yi, kai dai ka manta ni ko?"
Cikin yanayin ƙufula da hassala Jabir yace da ita "Dan Allah shiga ciki, ba na son tashin hankali."
Yanayin hassalar da yayi mata magana da shi yasa ta ƙura masa idanu, sai kawai ta ji ta kasa masa gardama, ɗan ta ne fa, tunda ɗan mijin ta ne ai, amma tsaf ta haɗiye abin da ke ranta ta juya ta shiga ɗakin kuma wanda ta san ko shi uban shi ya bata wannan umarnin ba zta yi abinda ya ce ɗin ba. Ganin haka sai Jabir ya saki mahaifin nashi à sanyaye yana faɗin "Bana so gaskiya, bana son haka Abba."
Bai jira ya ce komai ba kuma sai ya raɓa shi ya fice yana faɗin "Zan dawo anjima."
Da wannan haushin ya fita a gidan, kai ina dalili ina anfani mata irin matar Baban shi? Ba fa dan ba kyau ba, da sai ya dakonci mahaifin sa baya nan zai shigo mata cikin dare ya rufe ta a ɗaki wallahi ya zane ta, to amma babu kyau haka ai, amma dai mata irin ta baban shi, irin su ne suka saka ka aiki da ayar da ta ce a dake su dan su gyara, Haba. Gashi yanzu ta hassala mahaifin shi, shi ma kuma ta harzuƙa shi, almubazzarancin da ya ba so yayi da kuɗin shi saboda aikin dake gaban shi, shine ta sa ya yi, dan kuwa wasu irin dalla-dallan babur guda biyu ya yanko mata ita da mahaifin nashi, mark ɗaya sai dai kala kowa da ta shi, to akan babu ɗin take cewa za ta kai uban shi kotu? Ita ga mahaukaciya ba.
A cewar mahaifin Jabir ba'a taɓa masa sallama mafi ƙolokuwar arziƙi irin ta yau ba, bayan an bashi makullayen su da takardu aka shiga da su ciki, saida yayi ƙwallan farin ciki, dama rashin abun hawan ya sa yake karɓan nata ai, to ɗan sa ya huce masa takaici, tun yana ƙofar gida Jabir ya kira shi, bayan ya amsa sa albarkar da ya masa à nutse ya furta "Abba."
Shima a nutsen ya amsa da "Na'am, Jabir."
Cikin sigar rigima Jabir yace "Abba, ni fa ka gaya wa matar ka, gaskiya ta daina É—aga maka hankali, kai kaÉ—ai gare ni fa."
Wani daÉ—i ne ya kama mahaifin shi, sai yayi saurin juyawa cikin gida yana saka wayar a amsa-kuwa dan kawai ya bata haushi dan halin Bara'atu sai Allah yana faÉ—in "Ban ji ba Jabir, me ka ce? Kamar sadarwa ba kyau."
Ya ƙarashe maganar da hararen Bara da ta rikice ganin moto guda biyu sai zagaye su take tana kallo tana taɓawa da neman ƙarin bayanin na waye? Cikin siririyar murya kuwa Jabir da bai san ya saka shi amsa kuwa ba yace" Abba, na ce ka faɗawa aunty ta daina ɗaga maka hankali, bana so ko kaɗan, zuciyata gaza ɗaukar hakan take yi."
Bai jira ya ce komai ba kuma sai yace" Sai anjima Abba." Wani shaƙiyin murmushi ya saki yana maida wayar aljihu ba tare da ya kalle ta ba yace" Ɗana Jabiru kenan, Allah ya maka albarka."
Taɓe baki tayi tana ayyana _" E lallai Jabir ya ƙaro wulaƙanci, yanzu ita yake gayawa haka? Gashi kuma yanzu ba zai daku ba, to w ma zai dake shi? Dama can ai uban dake da kashi ɗaya take saka wa yana dukan nashi, to yanzu kuma sun ɗinke."_
Makulli ya cilla mata yace" Ki É—auki É—aya, É—ayan nawa ne, ÆŠana ya siya min sannan ya min shamaki daga tonan asirin ki."
Bai ko kalle ta ba ya wuce É—aki yana faÉ—in" Bari nayi wanka na fita zaga gari, yau hankalina kwance."