← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 168

Sashe 44

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yayin da Abbu Mukhtar kuma duk ya watsar da lamarin matan Yayan nashi ya shiga nemawa Eesha magani, da fari aikin da aka mata ne yasa shi zuwa dan a tabbatar mishi tana lafiya, sai kuma gwaji ya nuna ƴaƴan hanjinta sun yi kusa da samun matsala sakamakon abubuwan da aka saka mata a ciki, wanda dama masu irin hakanan kasada ce suke yi da rayuwar su, wasu ma kafin wannan aikin diyya ake basu su bar wa iyalinsu. Bai faɗawa ko ita kan ta Aisha ba haka suka fita ƙasar waje suka sake ganin ƙwararren likita, daga nan aka ɗorata magani har tsawon wata uku, bayan nan su sake komawa dan ganin ci gaban da aka samu. Wannan abu da ya faru sai Fa'iza ta zama kamar mujiya a gidan, ga dai mai laifin na samun kulawa da riritawa, amma ita sai kowa yayi gefe da ita hatta mijin nasu kan shi ya ƙaurace mata a komai ma, su Hajia kaɗai ke mata kara da kawaicin amsa gaisuwar ta da yi mata magana idan ya zama dole, sai kuma Aisha da Kabil da basu san me ke faruwa ba, dan Fahad ma ba'a batun shi da ba zama yake a gidan ba, dan kuwa lamarin shi yana ƙaa girma ne lalacewa na ƙara zuwa mi shi kamar mai shafar aljanu.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.

Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._

_Bismillahir-rahamanir-rahim._

*20*

*WATA UKU* da tafiyar Aisha komai ya lalace mishi, gida ba dadi waje ba daɗi, mahaifin shi ya daina kula shi gaba ɗaya ma, yanzu ko ɗan faɗa da rigimar nan sun daina, haka ma Hajia Kaka da yake jin daɗin zama da ita ta canza mishi, sai kuma mahaifiyar shi da ta tsiro da wasu sababbin halaye na zuzuta Ahalin Aisha har ma take faɗin _"Ai da na san yarinyar nan tana da alaƙa ta jini da Ahalin Ahlan, wallahi tallahi da ban bari an tafi da ita ba sai na sa ka aure ta."_ Sosai ya fahimci maman shi kenan auren jari take so ta mishi, auren ƙwarya ta bi ƙwarya, a wata ukun nan ya gane yana mugu-mugun son yarinyar nan da gaske, ƙwarai take hana shi sukuni har ya gagara nutsuwa a baccin shi, sunan *Abbu* shi ya fi komai tsaya mishi a rai, narkakkun idanun ta wanda ya ga irin su a fuskar mahaifin ta, da kuma tatausan muryar ta sanda take mishi ƙiriniya. Amma abun da ke ɗaga mishi hankali shine idan ya tuna ranar da ta kalli fuskar shi ta furta mishi cewa ta tsane shi, hakan dagula mishi lissafi yake, kiɗima tunanin shi hakan je yi, wani lokaci har ya fara sakin layi bai sani ba, dan abun da bai kai na rigima ba sai ya dinga masifa yana neman bala'i ido rufe.

A ƙarshe kawai sai ya ji ba zai iya zaman garin nan ba, take ya haɗa kayan shi kawai ya sanar da ƙanin mahaifin shi Alhaji *Hisham* cewa yana zuwa zai zauna tare da su. *Bayan* zuwan shi can ya samu canjin yanayi da ruwa da ma abinci, sai dai damuwar shi na nan tare da shi, hasalima wata sabuwar damuwar da ta kunno mi shi kai wato *Fadila*.

Ƴa ce ga ƙanin mahaifin shi, shi da zai ganta a hanya ma kafin zuwan shi nan ba zai gane ta ba, amma daga zuwan shi yarinyar nan da bata wuce 17 ba take ta ta ƙoƙarin shiga jikin shi tana son samun kusanci da shi, komai dai *Yaya Sa'ad*, abinda ya fahimta game da haka kuma a zahiri shine *son shi take*, yayin da shi kuma neman sassaucin soyayyar wata ne ya kawo shi garin su har ma take mishi wannan rawar kan.

Ba ma ita ba, kawun shi ne a gaban shi yanzu da ya fuskanci kamar yana ɗan yawan damuwa, wanda damuwar ta haifar masa da hawan jinin da yake ganin likita duk sati biyu zuwa wata ɗaya, ya tambaye shi sau ɗaya bai faɗa mishi komai ba, hakan kuma ya kasa haƙura duba da yana damuwar fiye da kima. Dan haka yanzu ma ya sake tunkarar shi da maganar, amsa ɗaya da ya bashi ita ce _"Kar ka damu da damuwata Sa'ad, domin kuwa bata da magani, kawai kai da ka tayani da addu'a Allah ya gafarta min zunubin dana aikata a baya."_

*Zunubi*? Zunubi? Wane zunubi Kaxun shi ya aikata a rayuwar shi haka da ya dame shi? Ko da yake kowane bawa mai aikata saɓo ne, na wani kawai ke fin na wani girma, dan haka zai tayashi da addu'a Allah ya gafarta mishi, kamar yadda shi ma addu'ar shi bata wuce _Allah ya mantar da shi Eesha idan ba alkairi bace a gare shi, idan kuma alkairi ce Allah ya kawo ƙarshen matsalar shi da ita da Ahalin ta_, addu'a ta gaba kuma d yake yi ita _Allah kawo ranar da zai ga ƙarshen DG_, dan duk da yana wani garin yanzu haka bai daina samun labarin shiga da ficen shi ba, kuma wannan burin yana da shi na ganin ya gurfanar da shi ƙasa wanwar.

*******************

Tana zaune kan kujera da ƙaramar carbin ta tana ja ɗaya daga cikin masu kula da ɓangaren su ta shigo da sallama falon nata, a sanyaye ta amsa tana waigawa, ganin ita ce kawai ta dawo da dubanta tana ci gaba da abinda take, tana zuwa mai aikin ta durƙusa gaban ta tace "Sannu da hutawa Hajia?"

A tsanake ta amsa da "Sannun ki, lafiya ?" Da ladabi mai aikin ta miƙomata enveloppe ɗin hannun ta tace "Yallaɓai ne ya ce na baki wannan, sannan na gaya miki sun tafi Amerika, kuma ba zasu dawo ba sai Hajia Abida ta haihu."

Kamar wacce bata gane yaren na mai aikin ba take kallon bakin ta, ganin dai ita ma mai aikin na ɗan kallon ta yasa da mamaki tace "Wane yallaɓan ne ya baki?"

A ladabce tace "Hajia Yallaɓai dai naki."

Wani mamakin ne ya sake baibaye ta, to ita fa tasan Bilal baya garin nan, yau kwana huɗu kenan da tafiyar shi Singapour wai zai je duba kamfanin Alhaji a yadda ya faɗa mata, to yaushe ya dawo? Ko da yake zai iya yiwuwa turowa yayi, dan haka tace" To wa ye ya kawo saƙon?"

Mai aikin dai da rashin gane mahimmancin tambayoyin tace" Shine da hannun shi ya bani."

A É—an razane tace" Ya baki? Yaushe?"

" Yanzu, yana bani suka fita ni kuma na taho kawo miki." Cewar mai aikin, girgiza kai Fa'iza ta dinga yi alamar gigicewa ta kalli enveloppe É—in tace" Shi da kan shi? To yaushe ya dawo? Kuma shine bai neme ni ba?"

Da mamaki mai aikin tace" Hajia...ai Yallaɓai a gidan nan ya kwana."

Kasa magana Fa'iza tayi sai kallon bakin ta kawai a ranta tana nanata a gidan nan ya kwana? Tafasar da zyciyar ta ke yi yasa kawai ta mata alama da hannu cewa ta tashi, miƙewa mai aikin tayi za ta fita sai kuma Fa'iza ta ɗan juya tace" Ina ya ce miki zasu tafi?"

A ladabce ta bata amsa da" Amerika, wai sai ta haihu zasu dawo."

Shiru Fa'iza tayi har saida ta ji fitar mai aikin da sauri ta miƙe tana ɗaukar wayar ta dan kiran lambar shi, abun mamaki tsaf ta dinga kiran shi sai kiran ya dawo alamar dai ya jefa lambar ta a baƙin jadawali. A haukace ta jefa wayar a kujera ta ɗauki enveloppe ɗin ta shiga buɗewa da sauri.
Chapter 44 · 0% Book details