Sashe 82
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haɗe fuska tayi ta kawar da kan ta, maganar ta soke ta sosai, fisabilillah ya kalle ta da girman ta ya ce ƙarya take? Idan ma ƙaryar ce ai ba zai faɗa mata kai tsaye haka ba ko? Sai ya bar abun à ranshi, amma da ɗiyar ta budurwa da shekarun ta *talatin* cif a duniya ya ce ƙarya take kai tsaye, gaskiya ba ta ji daɗi ba kuma ranta ya ɓace.
Cikin faɗa Alhaji ya ci gaba da faɗin "Za ki tashi ki shirya ko sai na ɓata miki rai? Ummu ke yarinya ce ƙarama da za'a zauna ana yawan nanata magana da ke?"
Wani kallon sama da ƙasa ta mishi tace "Kasan ba yarinya bace ni ka ce ina ƙarya?"
Shi fa ya É—an sha'afa da wacece matar sa, dan haka kuwa ya sake faÉ—in "E É—in na faÉ—a, duka sati biyu da kika gama al'adar ki, to mahaukaciya ce al'adar da zata sake dawo miki yanzu."
Tashi tayi tsaye da irin masifa ita ma tace "To kai baka san al'ada bane? Wane irin canji ne ba ta yi wa mata? Idan baka sani ba ka je ka tambaya ka ji, bayan jinin lafiya ai har na ciwo ke akwai, a wata ɗaya ne ba zan iya jini biyu ba? Bayan kuma wasu matan suna iya yin jinin sati biyu har zuwa kwana na goma sha biyar ma, daga nan idan ya wuce ya zama na ciwo, sai ka tsaya kana faɗa min ƙarya kike ƙarya kike kuma ba ko tausasawa ma, da girmana ne zan zauna ina maka ƙaryar?"
A hassale ta kama hanyar madafa dan dama girkin da su Aliyu suka saka ta take yi, da kallo ya bita, yadda take maganar alamar ta hassala ne, sai kuma ya tuna da maganar daa ta yi wai da girman ta zai ce tana ƙarya? OK, shine ya sa tayi hushi kenan? To sh yanzu Ummu ta kalle shi ta gaya masa girma? Jinjina kai yayi shima cike da jin ai shine mijin ya bita madafar, daga bakin ƙofa yace "Za ki je asibitin ko na tafiya ta hsabgogina?"
Ba tare da ta juyo ba ranta ɓace tace "Ka je kawai, ni dama ban hna ka zuwa sabgogin naka ba ai, kuma nima ina da harkokina da nake yi ai ka sani, ba zaman banza nake yi gidan ba."
To! To wai me ya mata? Daga magana? Taɓe baki yayi ya juya zai fice yace "Sannu mai aikin yi, kar ki je ɗin."
Duk da ya fita, amma takaicin wai ita zai ce wa kar ta je ɗin? Alhaji raina ta ne yayi ko me? Ita fa ba yarinya bace yanzu, me yasa yake datsa mata magna ne haka ? Da gasken gaske ƙwalla ce ta cika mata idanu, ya sani sarai ta tsani duk abinda zai kawo mata raini a rayuwa, ya sani bata son rashin girmamawa, ko ya fi ta shekaru ai ya mutumta ta saboda ita ma tana da shekarun, cikin wannan ƙwalla dake neman gangaro mata da ɓacin rai ta ɗaga murya tace "B zan je ɗin ba, idan ma asibiti zan je ai ba kai zaka kai ni ba, ni ba yarinya bace zan iya kai kaina, kuma wallahi kar ka sake kulani dan ba zan kula ka ba ni."
Yana jin me take faɗa, ta ɗan bashi mamaki da fari na yadda ta hassala lokaci ɗaya, amma kuma sai yaji ta bashi dariya da kuma tausayi, dariyar da ga bashi ita ce yadda da gaske take maganar, tausayin ta kuma da ya kama shi bai wuce yadda ya san Ummu da wani irin hali na son girma ba, ita dai a rayuwar ta a girmama ta kawai, kaɗan ne fa a aikin Ummu ta yi kuka dan kawai ta yi sallama a grp na WhatsApp kuma ga wasu online amma a ƙi amsa ta, da fari da wasa y ɗauki wannan matsalar, amma daga baya ya fahimci kawai hakane take, shiyasa tunda ya gane ta yake girmmata da furta mata kalmar da babu raini a ciki, yau ma ran shi ne ya ɓace ganin ita ba yarinya ba amma ta zauna da ciwo a gida.
********************
Kallon shi Hajia ke yi har ya ƙaraso kan teburin da suke cin abincin, ba mutum ne dake tashi da sassafe ba, yau me ya faru da ya taso warhaka? Wannan mamakin ya sa take kallon shi har ya zauna bayan ya gaishe da mutanen dake wurin, Hajia dake masa wani irin kallo ya kalla yana murmushi yace "Mamie ina kwana?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa da "Barka da safiya."
Maida duban shi yayi ga abincin da duk suke ci, sai ya ture farantin gaban shi kaÉ—an alamar ba abinci zai ci ba, kofi ya É—auka ya fara haÉ—a ma kan sa shayi, babu dai mai cewa komai kowa na abinda ke gaban shi, saida aka kwashe mintuna haka kafin Yaya Bilal ya kalle shi yace "Jiya da muka dawo daga gidan su Fati baka nan, har na kwanta ni dai ban ji shigowar ka ba."
Kallon shi yayi da girmamawa yace "Hakane, na É—an je wani wuri ne."
Ajiyar zuciya Yaya Bilal É—in ya sauke tare da ci gaba da cin abincin shi yace "Dama dan mu sanar da kai ne kawu Abbas ya amince da auren ka da Fatima, Abbu kuma ya saka rana nan da juma'a mai zuwa in sha Allah, dan haka ka fara shiri."
Wani kallo ya ma Yaya Bilal ɗin a rashin sani irin mai kama da hararan nan, sai kawai yayi wani irin murmushi dake nuna kuma dai da wasa kuke, saida ya ƙara kurɓa shayin shi sannan yace" Yaya Bilal, akwai wacce nake so na aura, Nabila, kun san ta ai dan jiya ta zo nan, ban so mu samu matsala da ku akan maganar aurena, ko mace yanzu ba'a mata auren da bata so bare kuma namiji, na yarda muna rayuwa ni da Nabila wacce bata da kyau, amma ko ma menene ni na koya mata komai, dan a gaban iyayen ta na same ta, dalilina ta fara yin nesa har take bijirewa umarnin su, ita akwai abinda take hango mana wanda take ganin bai dace muyi aure tun yanzu ba, ni kuma na kawo mata hujojjin d suka fi nata ƙarfi tare da nuna mata auren shi ya fi alkairi gare mu ko dan mutumcin ku, na sha wahala sosai kafin na sa ta yarda za ta yi aure dani yanzu, kuna ganin ya dace na juya mata baya a wannan gaɓar? Dan Allah ku barni na aure ta, tun farko na fara son ta ne saboda soyayya ta aure, sheɗan ne kawai ya rinjaye mu har muka dinga abinda bai dace ba."
Sosai da sosai Abbu Mukhtar ya fahimci Fahad, bai san me yasa ya ji ya bashi tausayi ba har da ita yarinyar kan ta? Haka kuma bai san me yasa ya ji ya dace a bar su suyi aure ba? Ko dan Æ´aÆ´an shi duka mata ne? Shi dai a ganin shi suyi aure, tunda har ya gamsu zai iya zama da ita ai ba matsala bane, kuma ya faÉ—a da bakin shi shi ya fara kangarar da ita, to ya iyayen ta za su ji idan aka ce ya juya mata baya? Gaskiya ba adalci a ciki.
Abbu kuma da jin haushi ya kalle shi yace "Me zai faru idan ba'a bar ka ka auren ta ba?"
Kallon fuskar Abbu ɗin ya yi, sai bai ce komai ba ya ƙurawa kofin dake gaban shi idanu, hakan yasa Alhaji faɗin "To ba zaka aure ta ba, na faɗa maka haka ba tun yanzu ba, wataƙila ka ɗauka wasa nake maka shiyasa, ka yarda ka auri Fatima ita ce ta dace da kai saboda tarbiyyar ta, amma yarinyar da kake so ka kawo mana cikin ahalin mu, sam bata dace ba dan ƴar ƙananan mutane ce..."
Da sauri Fahad ya katse shi a kausashe da cewa" A'a Abbu, kar ka zargi iyayen ta akan gurɓacewar tarbiyyar ta, wai me yasa kake hakane? Shikenan duk wanda bai da tarbiyya to laifin iyayen sa ne? To me zaka ce a game da ni kenan? Kenan da gaske sakacin ku ne ko naka?"
A tsawace Sabeer ya miƙe yana neman cakumo Fahad tare da faɗin "Fahad! Mahaifin namu kake faɗawa haka?"
Da sauri Yaya Bilal da ya san yana dukan shi Hajia za ta fara hawaye yayi gaggawar riƙe shi yace "Kar ka taɓa shi Sabeer, yi masa magana kawai."
Cike da takaici Sabeer ya kalli Yaya Bilal ɗin kamar zai cije shi yace "Wai me yasa kuke hakane? Yaron nan tun ba yau ba ya kamata a ɗauki mataki akan iskanxin shi, amma da nayi yunƙurin haka sai ku hana, me yasa? Ta hakane zai gyaru? Har kamar Fahad ne zai zauna Abbu na faɗa yana faɗa? Bai kamata ɗaya a cikin mu ya ladabtar da shi ba?"
Ba tare da ya miƙe tsaye ba ya kalli Yaya Sabeer ɗin yana taɓe baki yace" Gaskiya fa na faɗa, iyayen Nabila mutanen kirki, mahaifin ta ma fa baya raye, mahaifiyar ta kuma matar arziki ce, wacce kullum take ɗaukar ƴaƴan kowa a matsayin nata..."
Hajia da ta cije leɓe dan hana kanta kuka ya kalla yace" Mamie, kin san wani abu? Uwar marayu fa ake kiran ta a unguwar su, ba wai ga wanda ya rasa uwa ko uba ba, hatta yaran da suka ɓata gidan ta ake kai su, ni ban taɓa ganin mutuniyar kirki a wannan zamanin ba kamar ita, ta aurar da yarinyar da ba ita ce ta haife ta ba, ta raini ɗan ƙanwar ta har ya yi aure shima, idan ba Nabila da ta faɗa min ba, ban taɓa sanin ba ita ta haife su ba."