Sashe 43
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin haka yasa Sabeer da Bilal duk motsawa da niyyar su ma su samu su yi sallah isha'i, dan magariba tun a Maraɗi sukayi gidan aminin Alhaji da ya tarbe su tun zuwan su kuma ya haɗasu da drebobi da motock aka tuƙo su. Cikin dakakkiyar murya Abbu Mukhtar ya kalli Fa'iza da ita ma ta juya za ta nufi nata ɓangaren yace "Fa'iza..."
Ƙwarai da gaske gaba. ta ya faɗi sosai har saida duk tsigar jikin ta ta tashi, a hankali ta dakata sannan ta juyo à sanyaye tace "Na'am."
Sai kuma ya kalli Yaya Bilal a tausashe yace "Ka yi haƙuri Yaya, ba zan ci gaba da ɓoyewa ba, musamman a yanzu da na samu ƴata ɗaya, dan na gaji da zama da muke da *makashinmu*, ɗan uwa Bilal, ina so ka sani matarka Fa'iza nake zargi da ɓatan yarana guda biyu, saboda wasu dalilai masu ƙarfin gaske."
Babu wanda ya razana ba jin furucin shi, dan ko da akwai masu zargin ta babu mai niyyar yi mata wannan fallasar, kawai dai kowa yayi shiru ne a zuba mata ido an san dubun ta zata cika wata rana, a kiÉ—ime Yaya Bilal yake kallon shi da tsantsar mamakin da babu algus a ciki yace "Mukhtar, kasan me kake faÉ—a kuwa? Matar tawa?"
Ya kai maƙura ne, dan haka ya kalle shi tare da jinjina kai yace "E ɗan uwa, ita dai."
Cike da dattako Alhaji ya kalli Mukhtar É—in yace "Uban Kabil, kayi shiru ka ji, ka bar maganar, zamu tattauna anjima."
Sai kuma ya kalli Fa'iza da zaka rantse sassaƙata à kayi a wurin yace "Fa'iza, je ki sashen ki kin ji, je kuyi sallah."
Da sauri Abbu Mukhtar yace "A'a Abbu, dan Allah ka bari muyi maganar nan."
A É—an kausashe Yaya Bilal yace "Wace irin magana zamuyi Mukhtar, matata ? Kake zargi da sace yaran ka? Me cece hujjar ka?"
Ajiyar zuciya Abbu Mukhtar ya sauke yana kallon fuskar Yaya Bilal ɗin sannan yace "Kowa a gidan nan ya san Rabi Fa'iza kaɗai take ma aiki, nesa da sukayi yasa ta bar aiki anan daf da haihuwar Eesha, amma a daren da ta zo mana barka sai muka nemi Eesha muka rasa, sannan su Hajia sun ce ta zo da cikin da suke ta mamakin dama da ciki ta bar gidan nan, tun daga haka kuma su dai basu ji labarin haihuwar ta ba, sai zuwan da tayi kwanakin baya ne take faɗa ma su Hajia wai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Bayan duk wannan Yaya Bilal duk damuwar da muke shiga ta ɓatan yaran nan ko a kwalar rigar matar ka, sannan ranar da aka ce a bayar da sanarwa, wataƙila ta manta ne ko kuma wata manufar da ban tasa tayi haka, ita ce ta faɗa mana a saka cikakken sunan Aisha Mukhtar Ahlan, wanda muna hanya yanzu na tambayi Aisha ta ce a gidan marayu haka ake kiran ta, sannan..."
Sai kuma ya kalli Fa'izan dake kallon shi ga da ga sannan yace" Ita fa ta zo mana da labarin wani ya kira ya ce an samu inda Aisha take, ita ta jagorancemu har inda yake sannan ya kai mu gidan da Eesha take, shin dukanku bakuyi mamakin yadda mutumin yana ganin Fa'iza ya gane ita ce ba sannan yake girmama ta? Ta ya mutumin da ya kira lambar ta ne kawai ya san *wacece* ita a cikin mata huÉ—u da muka tafi da su? Sannan me yasa *sai lambar ta aka kira*? Bayan kuma a lambobin da muka bayar wanda za'a iya kiran idan an samu masaniya ko lambar *uwar da ta haifi Eesha* babu."
Ƙwarai maganar shi ta kama hankalin su har suka shiga kallon Fa'iza irin suna jira su ji ta bakin ta, shi kan shi Yaya Bilal da yayi niyyar kare mutumcin ta da iya ƙarfin shi sai ya samu kan shi da zuba mata idanu yana jira ya ji me za ta ce? Ganin kow ita yake kallo da tuhuma har da Abida da ta saje a cikin su sai hankalin Fa'iza ya sake tashi ta shiga rarraba idanu cikin ɓarin murya ta shiga faɗin "Eee..haba...Abbun Kabil, ni me zai sa na sace yaran...nan? Wal..."
Da hannu Abbu Mukhtar ya dakatar da ita tare da faÉ—in "Dakata Fa'iza, nan babban gida, kuma muna girmama ki matsayin ki na matar babban Yayanmu da muke kallon shi uba gare mu, ba wai nayi haka bane dan ina so na É—auki fansa ko a hukunta ki ba, kawai nayi magana ne dan kisan mun san ke ce sannan ki kiyaye, dan wallahi yanzu duk abinda ya samu É—aya daga cikin yarana, na rantse da Allah zan É—auki mummunan matakin da ba zai yiwa bawa daÉ—i ba."
Yana gama faÉ—in haka ya juya a fusace ya bar falon, da kallo duk suka bishi har ita Fa'iza, sai Yaya Bilal da ya matso kusa da ita yan binta da wani kallo yace" Fa'iza, abinda zaki min kenan ni da ahalina?"
A hankali ta girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka tana faÉ—in" A'a Bab, wallahi ban aikata komai ba, ba gaskiya bane abinda kuke zargina, ta ya kuke tunanin zan iya aikata haka gare ku? Wallahi ban aikata ba."
Sabeer dake maka mata harara ne ya ja tsaki yace" To idan zargin ki ne ake ki wanke kanki mana."
Kallon shi tayi sai kuma ta jinjina kai ta kalli su Hajia tace" Mamie, dan Allah Mamie ki sa baki, wallahi ban aikata komai ba Mamie, Abbu..."
Tsawa Yaya Bilal ya daka mata yace" Shiru dallah malama! Idan ƙarya aka miki ki musa mana..."
Sai kuma ya girgiza kai cike da takaici yace" Kin ban mamaki Fa'iza, ban taɓa tunanin zaki iya aikata haka ba."
Raɓata yayi zai wuce d sauri ta riƙo hannun shi tana fashewa da kuka da cewa" Bab...bani na aikata ba, na yarda nayi wasu kurakurai, amma wallahi don taimakon ahalin nan ne, daidai da rana ɗaya ban taɓa tunanin cutar da mutanen gidan nan ba, matsala ta kawai *da na san mai hannu a ɓatan yaran kuma nayi shiru* da bakina saboda wata manufa, amma zan faɗa muku gaskiya Bab, dan Allah kar kayi hushi da ni."
Gyara tsayuwa yayi alamar yana so ya ji me zata faɗa, hakan yasa Abida fahimtar Fa'iza fa na shirin ɓallo mata ruwa, ai daidai Fa'iza na buɗa baki tace" Ranar da aka..."
Sai kuwa Abida tayi luuuuuu! Ta faɗi ƙasa tamkar wacce ta suma da gaske duk da kuwa ta ji bala'in ciwon faɗuwar, amma haka tayi gaggawar dakatar da tafiyar numfashin ta sa'ilin da aka yi caaa! A kan ta ana salallami da jimami da kuma son bata agaji.
Da sauri Yaya Bilal ya É—auketa ya kwantar a kan kujera yana murza tafin hannun ta da kiran sunan ta a nutse, da kulawa Hajia ta dube shi tace "Bilal, ka kira likita mana ya zo ya duba ta."
Da sauri ya jinjina kai sai kuma Sabeer yayi azamar ciro wayar shi yace "Bari na kira Zeinab."
Da gaggawa ya aika kiran, jim kaɗan kuma ta ɗaga yake sanar da ita abinda yake faruwa, da tabbaci ta ce mishi tana zuwa ba da jimawa ba, jugum-jugum sukayi babu mai magana sama da minti sha biyar kafin Dr. Zeinab ta iso gidan, kai tsaye ta shigo babban falon a taƙaice kawai suka gaisa da mutanen ta nufi inda Abida take, gwajin da duk ya kamata tayi mata ta mata har da ɗaukar jinin ta akan yatsa sannan ta sadashi da inda za'a fayyace halin da jinin nata yake ciki, hatta ciki idan tana da za'a iya ganewa ta wannan awon dan abun gwajin babba ne na gaske.
Kafin sakamakon jinin ya bayyana ne ta kalli Yaya Bilal É—in da duk hankalin shi ke tashe tace "Gashi kuma ba jinin ta bane ya hau."
Sai kuma ta kalli Abida da ta farka take ta lumshe idanu tace "Kan ki yana ciwo ne?"
Girgiza mata kai tayi a hankali alamar a'a, É—orawa tayi da "Jiri fa?"
Cikin kwantar da murya kamar mai ciwon gaske Abida tace "KaÉ—an kaÉ—an nake ji yanzu."
Murmushi Dr. Zeinab ɗin tayi tare da ɗauko gwajin tana faɗin "OK, bari mu ga me gwaji..." Kasa ƙarasa maganar ta tayi ta dubi Yaya Bilal dake kallon ta shi ma, sai kuma ta kalli Abida tana murmushi tace "Barkanmu Ahalin Ahlan, amma kafin na faɗa..."
Sai kuma ta kalli dukkansu sannan tace "Zaku bani goron albishir."
Da azama Yaya Bilal yace "Zeinab, me yake faruwa da Abida?"
Miƙewa tayi tsaye tana faɗin "Oga, Abida fa ta fara nauyi."
Hajia da Alhaji ne suka zaro ido da ɗumbin mamaki, lokaci ɗaya kuma farin ciki ya baibaye su jin wannan abu da suka ɗauki shekaru suna nema ido buɗe, musamman ma Yaya Bilal da ya rasa inda zai saka kan shi dan farin ciki da rashin tunanin ganin wannan rana rayuwar shi. Farin ciki mai sunan farin ciki an gan shi a wannan iyali, Abida na ganin kulawa tamkar babu gobe, riritawa take samu daga wajen kowa a gidan nan, musamman da ta zama macijin ƙaiƙayi ce sari ka noƙe, a wajen ire-iren su Mama Nuriyya ganin su sakawa Abida da alkairin da ta musu na nuna kulawa tamkar wajibi ne a gare su, dan haka kowa ke bayar da tashi gudummuwar.