← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 168

Sashe 61

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta kalli Aslam ɗin tare da mishi alamar _" Kai! Yo shiru."_ Sai kuma ta juyo a hankali ta saci kallon Bilal da suka bari nan tsaye, duk da ya ji abinda ya faɗa yaron bai kawo komai a ran shi ba, amma kuma yanayin da Abida ta nuna da juyowa da tayi ta kalle shi, sai kawai ya ji kamar bai yarda da ita ba tare da dasa mata alamar tambaya, in ba haka ba miye na ma yaron nuni da ya yi shiru? Miye na wani juyowa ta kalle shi? Waye kuma kawu Hashim ɗin da yaron ya faɗa? Ummmmm! Ya tuna, wanda ta taɓa nuna mishi a matsayin cousin ɗin ta ko? Hakane, to amma me yasa Aslam ya faɗi haka? Wace shaƙuwa ce ta shiga tsakanin su? Bayan ta faɗa mishi shi Hashim ɗin ba ma a nan garin yake ba, sannan a ranar da ya fara ganin shi ta ce ranar ne farkon zuwan shi gidan nan ya kawo mata ziyara, har ya gama tunanin shi bai kawo komai a ran shi ba, dan ko ranar da ya samu yaron har madafa shi da ita suna hira bai ji zargin su a ran shi ba, ya bar hkan a matsayin zumunci ne kawai.

Murmushin yaƙe ya yi ya koma ɗakin da ƙudirin idan suka dawo zai zauna da yaron dan jin me kawu Hashim ke mishi da har ya fi ƙaunar shi da shi uban da ya haife shi yake kula da shi da ɗaukar duk wata ɗawainiyar shi.

*Ɓangaren* Mama Nuriyya kuma farin cikin zuwan su Aisha ya sa har yanzu bata koma wajen su Hajia ba, yanzu haka rumgume take da ƴar da Aisha ke goyo wacce ita ce ƴa ta uku da ta haifa kuma duk mata, inda ta maida gaba ɗaya hankalin ta kan Aisha dake zaune kusan ta kamar ƙawayen juna tana tambayar ta "Kenan dai har yanzu sarakuwar ki na son ki?"

Murmushi Eesha tayi na mamakin irin tambayiyin da Mama ke mata tace "E mana Mamie, ita fa irin matan nan ne masu son kuɗi, ina mata kyauta sannan ina mata ladabi da biyayya, shiyasa take sona kuma har gargaɗi take ma Abbu kar ya ɓata min rai, ranar ma fa cewa tayi idan ya muzguna min bata yafe masa ba."

Dariya Mamie tayi tace" Iyeh! Lallai kin samu soyayyar ta, to shi fa, ba ya miki komai dai ko?"

Da sigar ƙaguwa Aisha tace" Mamie, kin tambaye ni fa ɗazu."

Turo baki tayi tace" To ki sake bani amsa mana, hankalina ba zan kwanta ba idan ba kya farin ciki a gidan ki."

Riƙo hannun Mamie ɗin tayi da fara'a a fuskar ta tace" Mamie, yana sona, yana kyautata min, har yanzu fa kamar ango da amarya muke, kuma kinga yana zama dani a gida muyi hira, yana tayani aikin gida, Mamie, idan kika cire saɓanin da akan iya samu a kowane zama, bana da wata matsala da Abbu, ki yarda dani."

Ɗaga mata gira Mamie tayi da yanayin raha ta kalle ta sama da ƙasa tace" Umm! Na gani ai, tunda ga jikin ki nan ya nuna, Amma dai Eesha kin daina motsa jiki ko? Dubi fa nema kike ki zama ke ce mahaifiyar ta wa."

Turo baki. Aisha tayi cikin shagwaɓa ta dora kanta a kafaɗar Mamie tace "Mamie, wallahi fa shi ƙibar nan yake so, a haka fa wai cewa yake baya so idan kuka ganni ku ce yana barina da yunwa."

Dariya ita ma Mamin tayi tace "Ban san wane irin raino Sa'ad yake miki a gidan nan ba, duk ya lalata min ke wallahi."

Murmushi Aisha tayi tana shafa hannun Mamien da ita kuma take jijjiga Yusrah dake bacci, jin ba ta ce komai ba yasa ta ƙoƙarin aje Yusrah tana faɗin "Bari kiga in tashi, akwai wani abu da nake son haɗa miki ki tafi da shi, nima a wajen *aunty Ummu* na koya."

Kallon ta Aisha tayi tace "Mamie, wai har yanzu grp É—in nan yana nan?"

Kallon ta tayi bayan aje Yusrah da yanayi irin wanda kake magana da ƙawar ka tace "Sosai ma, ai kullu gidan mu gaba yake ci, a ƙalla grp biyar aka buɗe duk ta dalilin shi, ke har da fondation muka buɗe na taimakawa mabuƙata (in sha Allah mu ma muna nan muna shirin yin haka, ga duk wacce take neman lahira da burin ta barin duniya aikin alkairin ta na bin ta, to ta shirya sannan ta mana magana, in sha Allah zamu buɗe ƙungiya dan taimakon marayu da mabuƙata, kuma ba sai mai kuɗi ba, da naira ɗaya zaki iya taimakawa wanda ba ya da ita, Allah ka tallafa mana akan wannan ƙudiri namu)..."

Sai kuma ta tsaya da kyau tana kallon Aisha tace" Wai dakata, kenan baki taɓa bayar da taimako ga gidauniyar mu ba?"

Girgiza kai Aisha tayi tace" Mamie baki taɓa faɗa min ba ai, kenan dai kun tsayu kan ƙafafun ku?"

Da irin kurin nan Mamie har da juya idanu tace" Ƙwarai ma, kuma wallahi sai kin fara bayar da gudummuwar ki ma."

Dariya dai Aisha tayi tana kwantawa kan doguwar kujerar tace" Na ji to Mamie, yanzu dai a kawo min abinda aka aje min."

Nufa É—akin ta tayi tana faÉ—in" Bari na dawo, amma sai na sake tambayar auntyna yadda ake haÉ—awa."

Jima kaɗan ta dawo riƙe da wata leda a hannu, tana zuwa ta miƙo ma Aisha tana faɗin "Bari na kira ka tsaye na tambaye ta naji, shi wannan cristaux de mente ya ne za'a yi gyaran gashi da shi?"

Da mamaki Aisha ta kalle ta tace "Gyaran gashi kuma Mamie?"

Kallon ta ita ma tayi tace "E, ko ba za ki yi ba?"

A sanyaye ta girgiza kai tace "Mamie ni na isa? Amma ai ba abinda ya samu gashina kuma yana da tsayi."

Tsaki Mamie tayi tace "Shirme, nea nake yadda zan gyara miki shi."

Kiran da ta aikawa lambar Ummu ya sa sukayi shiru, kuma ba jimawa ta ɗaga dan lokacin tana madafa tsaye kan ƙafafun ta tana girkawa Alhaji abinda zai ci dan suna hanya, tana ɗauka da fara'a da kuma sabon da sukayi da matar da take kira aunty tace" *Auntyna* ina kwana?"

Ita ma da fara'a da shaƙuwar da Allah ne kawai ya saka ta a tsakanin su tana murmushi mai cike da jin ƙaunar aunty Ummun tace" Ina kwana aunty, ya gida ya aiki?"

Daga wajen Ummu ta amsa da" Lafiya lau wallahi, ya naku hidiman?"

" Alhamdulillah." Ta faɗa tana hararen Aisha dake dariyar jin kowa aunty ke kiran kowa, to ina aunty a cikin su kenan? Cikin taushin murya Mamie tace" Aunty Ummu, wai gyaran gashin nan da kika faɗa min, ai na nuna miki mayukan duka na same su, to shi Cristaux ɗin ne nake so na ji ya za'a yi da shi? Dan na ganshi garai-garai kamar ƙanƙara."

Da kulawa sosai Ummu tace" A'a aunty, ba cristaux É—in ba, sai idan ba'a samu man shi bane ake anfani da shi kaÉ—an, zaki iya yin garin shi sai ki cakuÉ—a a cikin haÉ—in."

ÆŠan dafe gaban goshi Mamie tayi tace" Ayya, ni kuma ban nemi man ba iya shi kawai na nema, amma bari yanzu zan je na samo shi."

Dariya Ummu tayi daga inda take tace" E, zai fi anfani gaskiya, amma idan babu karki damu aunty, kawai ki sa wannan É—in, amma fa kaÉ—an."

Da fara'a ta sake amsa mata da" Shikenan auntyna nagode."

Ita ma da farin ciki ta amsa da" Ba damuwa, ana tare."

Har za ta kashe wayar sai kuma Mamie tace" Tun safe ban gan ki en ligne ba, ko dai ana ta shirin tarban Yayan mu ne?"

Jim! Ummu ta yi saboda Yayan nasu da ta faɗa, ko da yake da ta san shekarun mijin ta da bata faɗi haka ba, wanda ya cika saba'in a duniya har ya fara haurawa, hmmmm! Dariya kawai ta yi, dan duk shaƙuwar su da hirar su akan iyalin su ko mazan su wani lokaci basu taɓa tattauna matsalolin su ba, hirar maza ma ba dayawa suke yin ta ba gaskiya dan har yanzu ko hoton juna basu taɓa gani ba, hakan yasa suna kula da sirrikan su da abinda zasu tattauna tsakanin su, duk da tana da matsala a baɗini, amma a zahiri sai ta ce "Gaskiya kam, dan suna daf da higowa gari ma, Shiyasa bana kula wayar idan ba kira aka yi ba."

Da fara'a da kuma zolaya Mamie tace mata "To shikenan, Allah ya taimaka, nasan dai mu da sake ganin ki a grp kuma sai ko nan da kwana biyu, dan nasan Yayana zan rufe ki a É—aki ne kuyi ta raya sunna."

Wata ajiyar zuciya Ummu ta sauke da murmushi a fuskar ta na fatan hakan ya kasance musamman ma da ta haÉ—awa kan ta haÉ—in da aka bata tabbaci namiji na jimawa idan haro ya ci abinci da yajin tace" In sha Allah aunty, amma dai za ku ganni."

Daga haka sukayi sallama inda Aisha ke ta duban Maman nata, miƙewa Mamie tayi tana faɗin" Bari na ɗauko gyalena muje mu siyo man cristaux ɗin."

Da shagwaɓa Aisha tace" Mamie da wuri haka? Mu jira har gobe mana."

Da yanayin tsawa tace" Ke dallah ni taso, a hanya ma zan kira gyatumin ki na nemi izinin."

Miƙexa Aisha tayi a sanyaye tace" Allah sarki Abbuna, yana cikin gidan fa."

Jiyowa tayi ta kalle ta tace" Sai muje can mu nemi izinin, kinga kema kya tambaya daga nan."
Chapter 61 · 0% Book details