Sashe 122
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan gama ganin wurin da nuna masa abubuwan da aka canza Aliyu ya jinjina kai yace "E lallai malam Jabir, wato duniya sabuwa zaka buɗewa kan ka ko? Yanzu Alaramma ku kuke koya mana mu ƙauracewa duniya, shine kai zaka shinfiɗa irin wannan rayuwar, to yaushe amaryar za ta tare?"
Girgiza kai Jabir yayi yana kallon shi kamar mai ciwon baki yace" Aliyu na farko da na sani a rayuwata mai surutu, sahabin Annabinmu (SAW) bayan jarumta da yake da har da miskilancin da kan hanashi yawan hayaniya idan ba wajen faÉ—in Allah da Manzon sa bane, amma kai..."
Sai kawai ya sake girgiza kai tare da juyawa zasu fita daga gidan, Aliyu dake ta dariya ya biyo bayan shi faÉ—i yake" To ai nima da miskilin ne, da Abba ya tashi tura min abokin zaa sai ya tura min *adunkuma*, to idan ni nayi dukum kai ma kayi É—ummm abun ka, wa ye zai tayar da wani kenan? Dole ni ai na sauke girmana da ajina kawai nake surutu abuna, dan ya fi daÉ—i ma wallahi, kuma ni dake fama da É—alibai idan ban yi surutu ba to me zan koyawa yaran mutane."
Juyowa Jabir yayi ya masa wani kallo ba alamar wasa yace" Na ce ka ɗauke ni aiki ka ƙ ko? Ba ka buƙatata kusa da kai ne?"
Taɓe baki Aliyu yayi yana ƙoƙarin buɗe mota inda Jabir ɗin ke rufe gidan yqce" Ni ma ai nace ka min aiki kyauta, kafin na tsaya da ƙafafuna sai na fara biyan ka albashi."
Bai ce mishi komai ba saida ya shiga mota Aliyu zai tayar sannan ya kalle shi fuska a haÉ—e yace" Ba zan yi a kyauta ba, kuÉ—i nake nema ni, kuma zan fara aiki a makarantar ko baka so dole ka biya ni."
Kallon shi Aliyu yayi galala, sai kuma ya tayar da motar yace" To! Ina ga fa haushin Abba ya ce sai Kuwailat ta kammala karatu ya sa kake so ka fara huce haushin ka a kaina, dan yanzu tunanin ka nuna ma yake ni nake jan karatun ko?"
Cike da shashantar da zancen Jabir ya gyara zama a miskilance yace" Na faɗa maka ina buƙatar ƙanwar ka ne yanzu dan raino, ku bari ta ƙara ƙwari, kwa miƙo min ita."
Dariya Aliyu ya fashe da ita yana nuna kan shi yce" Alaramma ni kake faÉ—awa haka?"
Taɓe baki Jabir yayi bai ko sake bi ta kan shi ba, shi bai san yanzu idan aka yi maganar Kuwailat ba ma gyatumar ta ce ke zuwa masa lissafi, da gaske dai zawarci take a gida, Abba yana ji yana gani zai ƙyale ta tayi abin da take so? Kwana uku yau ya je gidan gaishe da Mama wai bata nan, yawo take zuwa ko? Ita kawai Maama hali dai irin na ƙuruciya sai tayi ta aikata shi, bayan budurwa gare ta. Shi ya ma rasa da wanne zai ji ne? Kula da haƙƙin *Abba margayi*? (Baban su Nabila), ko kuma kula da haƙƙin *Abba mai rai*? Kowanen su ya masa alkairi kuma baya so ya ga wani abu ya samu iyalin su, to ita Maama ai ba zai iya yi mata faɗa ba ko? Kuma sun saka Abba gaba kan yayi haƙuri dan Allah mana su manta d komai, amma dake shima Abban baya so su yarda tsufa bai fara jigata shi ba kawai ya ce wai su bar zancen, yanzu gashi can Maama ta yi free, dan tsaf yake sa lissafi a kan shi, yau kwanan ta shida da kammala wa'adin nan, to ina daɗi irin haka fisabilillah!
Kai tsaye gida suka wuce saboda Aliyu dake bada sallah magrib da subah a masallacin Alhaji yanzu, kuma sun taho tare ne dan akwai karatun da zasu tafi daga nan, ƙofar gida suka aje motar suka wuce masallaci.
*Ummu* da tund suka doso unguwar ta ji bata ji muryar limami ana sallah ba sai ta ɗauka nan har sun idar da sallah, dan haka ta kawo Kuwailat ƙofar gidan ta aje, yadda take ta tuttura baki yasa ta kallon ta tace "Ke! Wai lafiya kike ta sha min magani? Me na miki?"
Cikin turo bakin tace "Ba komai."
"Ba komai ɗin ne kike ta turo min bakin nan?" Ta faɗa cikin yanayin faɗa, a hankali ta ɗan saki bakin amma ba duka ba, buɗe mota tayi za ta fita Ummu tace mata "Yanzu haka zamuyi sallama? Kuwailat dan nace ba zaki bini ba shine kike wannan hushin? Me yasa kike so ki katse karatun ki to? So kike Yayan ki Aliyu ya yi tunanin dan yana na gida ne za'a dinga masa haka? Kiyi haƙuri mana, idan da rai da lafiya idan Nabila ta haihu sai ki je, ko ba haka ba?"
Ba dai dan ta saki fuskar ta ba tace" Shikenan Mamie, sai anjima."
Murmushi Ummu tayi tace" Ina ƙaunar ki."
Tana fita daga motar tace" Nima haka." Rufo ƙofar tayi ta nufi ciki Ummu na faɗin" Ki gaishe da su Hajia."
Ko juyowa Kuwailat ba ta yi ba, Ummu da ta fahimci har yanzu dai bata haƙura ba murmushi kawai tayi tana girgiza kai tare da ƙoƙarin tayar da motar ta wuce tana faɗin" Allah ya shirya min ke *takwarata*."
Muryar Idi mai gadi ce ta katse mata hanzari sanda ya furta" A'a, Hajiar auta ce a gidan namu?"
Ba ta so zuwan kowa ba ko wani ya gan ta, saida ta rintse idanu a hankali ta juyo ta kalle shi tana murmushin yaƙe, dan Alhaji gida yake sallah magrib sai in ba ya gari, idan fa suna cikin gaisawa ya zo? Ba tare da ta saki jiki ba tace" Ina wuni Baba Idi?"
Da fara'a ya amsa da" Lafiya ƙalau Hajia, ina wuni?"
Ba ta iya kora da hali ba ma bare wulaƙanci, amma a gaisuwar da yake ta mata har da ɗan mata nasiha na me zai hana ayi haƙuri a dawo ko dan yarinyar nan ta takura sosai, amma haka ta daure kawai tana jin shi tana kuma amsa mishi, saboda dai ta ga ta bar wurin tace "In sha Allah Baba Idi zan dawo, abinda ya faru ma tsautsayi ne, nagode sosai da kulawa, sai kwana biyu kuma."
Ta ƙara yi wa motar key kawai ta ji muryar da ta saka gaban ta wani irin tsinkewa ta faɗi cikin yanayin rashin jin daɗin haɗewa da suka yi ɗin yana faɗin" Barka uwar auta."
Nan ma rintse idanu tayi ta cije leɓe ta sadda kan ta, ta ɗan ɗauki sakanni haka kafin ta buɗe motar ta zuro ƙafar ta a nutse dan ta fito su gaisa, ko da suna zaman aure ba ta gaishe shi tsatsaye haka bare yanzu wanda rabon da ta saka shi idanun ta tun daren da ya yanka mata tikitin zuwa gidan su, kuma har yanzu tana jin haushin shi na ɗanyen hukuncin da ya yanke mata, amma ba zata gagara girmama shi ba tunda dai anyi zaman amana.
A nutse ta fito har lokacin bata kalle shi ba, cikin nutsatsiyar murya tace "Ina wuni?"
Da fara'a Alhaji dake binta da wani irin kallo yace "Lafiya lau maman auta, ya kike? Ya kuma kwana biyu?"
A matuƙar tausashe ba tare da ta kalli inda yake ba tace "Lafiya lau wallahi, dama Kuwailat na kawo, ni zan wuce."
Da fara'a ya É—ora da "Da wuri haka? Ko ciki b zaki shiga ku gaisa ba?"
Murmushi tayi kanta na ƙasa tace "Sauri nake, dama daga gurin karɓo ɗinkin Kuwailat muke, wani lokacin na shiga."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan, ya kuma shirye shirye? Nabila ana shirin amarcewa."
Murmushi tayi a taƙaice kawai tace "In sha Allah."
Ƙara buɗe murfin motar tayi zata shiga tana faɗin "Na wuce, sai anjim..."
Again muryar Aliyu ce ta sake dukan kunnuwan ta wanda suke tahowa shi da Jabir, farin cikin ganin su ya saka Aliyu yin murmushin jin daÉ—i yace "Gaskiya aunty ni dai ban yarda da wannan abu ba, kuma ni sam ban gane komai ba."
A nutse Ummu ta juyo ta kalle shi, shadda ce jikin shi da ta masa kyau irin ɗinkin zamani, sai Jabir da ya ƙara rage kuzarin tafiyar shi yana ƙare mata kallo yana ayyana _"Wato Maama an fara koyon bidi'a, tsabar a nunawa duniya yanzu ba'a tare da mariƙi shine har da saka sange."_
Ummu ko fuskar shi bta kalla ba da ta fahimci yau shigar ta shi da ta Aliyu kusan iri ɗaya ce, saida suka ƙaraso Aliyu yace" Ina wuni aunty?"
Da fara'a ta sadda kai cike da kunya tace" Ina wuni Yayan yara?"
Da girmamawa ya amsa da" Lafiya lau auntynmu, ya kuma kuke tsaya nan Abba?"
Yayi maganar yana kallon Abba dake ta kallon fuskar Ummu, haÉ—e fuska yayi ya kalli Aliyu yace" A ina kake son ganin mu?"
Murmushi Aliyu yayi bai ce komai ba, hakan yasa Ummu da tayi murmushi ita ma ta ƙara buɗe ƙofar mota ta ɗaga ƙafar ta ta shiga, zata zauna Jabir da tun haɗuwar su bai ce komai ba yace" Maama, ina hijabin ki kuma? Na ga da shi kike sakawa? Baki san ubangiji ya ce ku rufe al'aurar ku bane? Ke kuma gashi wiyan ki, hannayen ki duk a fili."
Kamar dai yadda kasan uba da ƴar sa, sai ya ƙara haɗe fuska har da girgiza kai ya goya hannayen shi baya yace" Ki daina haka kin ji Maama? Babu kyau, kuma mu ma ubangiji zai tambaye mu saboda mun gani kuma bamu tsawatar miki ba."