Sashe 55
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wacce ta kira da ƙawar ta ta ita ma da fara'a ta shiga tambayar ta za ta zo ne? Da zumuɗi Nabila tace "Me zai hana ƙawata? Shagalin bikin ki a ce ban zo ba, wa zai zo garin nan to? Ki kwantar da hankalin ki, yanzu haka fa wanka ne zanyi ina so naje wajen wannan marar mutumcin Zizo ɗin naga idan ya ɗinke min nawa ankon, kin san shi ɗan iska ne ai."
Da irin hargagin nan na kangararrun yara dan kuwa wacce Nabila ke kira da ƙawar ta ma ta girmeta nesa ba kusa ba, kawai ƙawance ne irin na ɗan duniya ya samu ɗan uwansa ɗan duniya, zigata take kan ta je dan kar ya mata halin da ya saba, dan idan bata saka nata ankon ba ita ma ba zata saka ba.
*Fahad* da yau ƙiriniyar ta kawo shi Maraɗi saboda shagalin bikin da za'a gabatar gobe na budurwar abokin cin mushen nashi wato Ja'afar, mota sukutum ba'a sani ba Ja'afar ɗin ya ɗauko kuma suka tuƙota har nan, Allah ne da kariyar sa suka kawo garin nan lafiya lau da kuma katin shaidar ɗan ƙasa da dukansu suke da, tun jiya suka zo kuma suke neman gidan da zasu zauna na sati ɗaya, an kaisu gidaje dayawa daga jiya zuwa yau amma bai musu ba, shine fa aka musu kwatancen nan da tabbacin zasu samu.
To yanzu ma tambaya ne suke so su yi shine suka dakata saboda ganin Nabila da sukayi yasa Ja'afar taka birki yana fitowa daga motar da cewa "Bari mu tambayi wannan yarinyar."
Fahad da ya hangi fanfo fitowa yayi da niyyar wanke hannayen shi daya gama cin sandwich kafin ya sha faro dake motar, ganin tana waya sai Ja'afar ya ɗan dakace ta har ta idar, Fahad kuma na fitowa kai tsaye wajen bokitin ya nufa, ganin ba sai ya sha wahalar kunna fanfon ba sai kawai ya saka hannun shi na hagu da ya fi iya anfani da shi yana ɗebo ruwan yana wanke duka hannayen nashi biyu. Lokacin ne Nabila ta kula da abinda ke faruwa, tana shirin ba wa ƙawar ta ta amsa ta kashe kiran tana juyowa gaba ɗayanta tana faɗin "Kutumar babakeren kan buru'uban nan... Malam ruwan wankan nawa? Kai! Kai dakata."
Duk tayi maganar ne a yanayi na hauka da ɗaga murya da kuma jaye bokitin a haukace tana mishi wani arnen kallo kamar zata kifeshi da mari. Tunda ta fara wannan hargagin duk suke kallon ta har shi kan shi Fahad da ya ɗago da niyyar ko ƴar gidan uban waye sai ya zabga mata mari sannan ya bar wurin, to amma yana ɗora idanun shi a fuskar Nabila, sai siririn kyawunta da kuma fuskar duniyancin da ya gani ƙarara a suffar ta sai suka birge shi, ba zato ba tsammani gabanshi ya faɗi, zuciyarshi ta buga da ƙarfin gaske tare da jin wani yanayi na daban da zai iya kira da matuƙar birgewa.
Zahirin gaskiya duk wannan rayuwar da yake yi baya neman mata, babu macen da zata nuna kanta tace shi ya taɓa nemen ta, abu ɗaya kawai da ya saka a gaban shi shine shaye-shaye, to a Dalilin shaye-shayen har ya kan iya ɗaukar kuɗin iyayen shi duk dan ya yi, kai a yanzu ba ma abinda ba ya iya ɗauka dan ya samu kayan maye, har agogon Sabeer ya ɗauka ya bayar aka bashi kayan shaye-shaye, kuma abu mafi masa daɗi ita ce shisha ya mata haɗin kakkauran flavour da ɗan sinadari mai bugawar a ciki, shikenan to rayuwa na yi masa daidai.
A yanzu da yake kallon Nabila, sai ya ji yarinyar ta birge shi kuma har ya ji kamar ya ce mata *yana son ta*, sai dai wace irin soyayya? Shi kan shi bai sani ba a yanzun, yanayin ɓacin ran ya fara haɗiyewa kafin ya tsurawa fuskar ta idanu yace "Ke ce kike wannan ashariyar?"
A kuwa kausashe kamar za ta haɗeshi tace "Ni ce da kaina, idan ba ni ba wa? Ya zaka saka min hannun ka da ban san me ka taɓa da shi ba a ruwan da zanyi wanka, nasan najasar dake hannun ka ne?"
Da ɓacin rai Ja'afar ya matso shi ma a kausashe yana duban ta yace "Ke dallah ƙaramar ƴar ƙwaya, kinsan wanene shi da kike faɗa masa haka? Wace najasa zai taɓa da zata lalata ruwan wankan ƙazama irin ki?"
A rikice ta kalli Ja'afar da mamakin kalaman shi, ranta ya sake ɓaci sosai, a yanzu dai ba abun da ta fara sha, amma tana ganin su *Arkiya* nayi musamman ma shisha, kuma tana sha'awar farawa ita ma ko dan baƙin cikin rayuwa, baya ga haka ma tana son taga ita ma ta iya jan hayaƙin nan sannan ta feso shi ta hanci cikin ƙwarewa. To amma yadda Ja'afar ɗin ya mata sai ta ga da buƙatar ta nuna mishi hali irin na su Arkiya idan suka bugu, dan haka a gigice ta sunkuya ta juye ruwan na bokiti suka zube ƙasa a banza, ba ta ɓata lokaci ba ta ɗauki bokitin sai kuma a fuskar Ja'afar da haro ga Allah da ya ga abinda take yi bai taɓa kawowa a ran shi wai shi za ta nufa da sunan ta buga ma ba.
Ai kuwa ji kake rumutsuuu a fuskar Ja'afar da wahalar bazata ta saka shi yin wata ƙaƙƙarfar ihu tare da sunkuyawa dafe da fuskar shi, lokaci ɗaya kuma azaba da zafin kalaman da take faɗi bayan ta ragargaza mishi fuska cewa "Aikin banza, har ni zaka kalla ka kira ƙazama? Ka ga ƙazami ma irin ka jahili da baka san me kake yi ba."
A zafafe ya yi niyyar nufa kanta bayan duba tafin hannun shi ya ga jinin da ya fito daga bakin shi yana faÉ—in "Na rantse da girman All..."
Da mugun sauri Fahad ya rirriƙe hannayen shi tare da fuskantar shi ya tare shi yana murmushi ganin yadda idanun Ja'afar sukayi jajir yana faɗin "Come on abokina, share kawai, yarinya ce fa."
Da maɗaukakin mamaki ya kalle shi yace "Yarinya? Wannan karuwar? Na rantse da Allah ko shugaban ƙasa ne ubanta yau sai ta gane bata da gata a duniyar nan, dallah kauce min!"
Yadda yayi maganar à tsawace tare da ƙoƙarin ture Fahad shi kuma ya ƙi bashi damar hakan yana sake bashi haƙuri da cewa "Ka manta nace Ja'afar, yarinya ce, kar ka biye mata dan Allah."
Ƙara kallon shi yayi yace "Wai akan me zaka ce na ƙyaleta? Oho! Dan ba kai ta ma ba ko? To wallahi sai na rama."
Da É—an É—aga murya Fahad yace "Ba zaka rama ba Ja'afar, ba zan bari ka rama ba."
A kausashe Ja'afar yace "Wallahi sai na rama, sake ni Fahad?"
Shima a kausashe yace "Ba zan sake ba, ba zaka rama ba Ja'afar, saboda..."
A tsawace yace "Saboda me?" Saida ya saci kallon Nabila da ta dafe ƙugu tana hararensu tana ayyana _"Sake shi ya zo mana, maza dama na iya faɗa da mata ne? Mun fa san lagon naku, banza kawai, wallahi kana zuwa tsiyata ka zanyi ba kai ba sake moruwa a gaban mace."_
Murmushi ya sake yi saboda kallon Nabila da yayi, sai kuma ya kalli Ja'afar ya sassauta murya cikin raÉ—a yace" Saboda *ina son ta*, ta yi min, dan Allah ka min kara ka ji."
Kallon Fahad ɗin yayi sosai yana tuna ai bai ta;à mishi irin wasan nan ba, ma'ana ya ga mace ya ce yana so, wataƙila da gaske yake tunda ya faɗi hakan à kan wannan da zai bawa sunan *bugagga*, ɗan siracewa yayi ya jinjina kai a sanyaye yace" Shikenan, amma fa idan har ba gaskiya bane ka sani wallahi yarinyar nan ko hayar ƴan daba sai na ɗauka dan su zane min ita."
Dariya Fahad yayi yana juyawa ga Nabila yace" Ba ma zaka saka ba, dan da gaske ta birge ni, kai baka ga ƴar duniya bace ta ƙarshe? Kunnuwan ta sun fi komai ɗaukar hankalina."
Yana jayawa ga Nabila ya zuba mata idanu yace "Ya sunan ki?"
Sama da ƙasa ta ƙwala mai wata arniyar harara sannan ta sake jan tsaki kawai ta nufi da bokitin ta bakin fanfon ta sake kunna ruwa, kusanta ya matsa ya sake cewa "Ya sunan ki dan Allah? Nan ne gidan ku?"
Ya faɗa yana nuna gidan nasu, bata kula shi ba har ta ɗibi ruwan ta ta ɗauka juya ta shige cikin gida tana binsu da harara, ganin inda ta shiga yasa shi girgiza kai yana jinjina tantirancin yarinyar, a girme ya girme ta sosai, amma ya ga ta fi shi iya dabanci yarinyar, tunda gashi da ɗaurin ƙrji ma take fitowa daga gidan su, juyawa yayi ga Ja'afar ya kama hannun shi yace "Muje abokina, tunda mun ga gidan zamu sake dawowa."
Taɓe baki kawai Ja'afar yayi bai ce mishi ƙala ba yana ta murza bakin shi da ya ji kamar ya fara kumbura har suka shiga mota suka bar ƙofar gidan da niyyar su tambayi wani a gaba.
*HaÉ—uwar su* ta biyu sun yi ta a wajen shagalin Arkiya, inda suka cika da mamakin yadda suka san juna, a bayan Arkiya ta faÉ—a mata wanene Fahad da irin gatan shi ne ma ta ji zata iya sauraren shi ba dan kuÉ—in su ba sai dan tunanin zai iya yi mata wata bajinta duba da yadda Arkiya ke faÉ—a mata irin É—awainiya da kashe kuÉ—in da Ja'afar ke mata.
Jingine take a jikin motar su tana wasa da ƙaramar wayar ta cikin wata irin fitsararriyar shigar ankon da sukayi na shadda, riga da siket ne ɗamammu da suka lafe a jikin ta kanta babu ɗan kwali ko kaɗan, yatsina fuska ta sake yi ba tare da ta damu da yadda ya matse ta sosai ba kamar zai kwanta jikin ta tace "Wane irin so kake min?"
Murmushin shaƙiyanci yayi yana kallon ta yace "Irin wanda kike da buƙata a miki? Kowane iri zuciyar ki ta raya miki, to shi nake miki."
Tsakiyar idanun shi ta kalla ba kunya bare fargaba tace "Kenan da iskanci kake sona? Bayan ka samu abinda kake so Shikenan?"