← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 168

Sashe 142

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harara Mama taa watso mata tace "Ke ki fita idona kin ji, wallahi na ji kin kira shi sai dai Maman ki ta harare ni bayan na bada baya, amma ba abinda zai hanani zane ki Ummu."

Turo baki Ummu tayi ta kalli Nabila da tayi dariya sannan ta kalli Mamie ma da tayi dariyar tace "Wa ce ni Maman aunty, mutuwa ai tana kunyar idanun mahaifi, haka na ganki fa ke da Æ´ar ta ki."

Sai kuma ta kalli Ummu tace "Maza ki karya ki tashi ki haÉ—a kayan ki ku wuce, ga Nabila nan za ta raka ki sai ta dawo."

Da mamaki Ummu tace "Ina kuma? Ina zan je aunty?"

A taƙaice tce "Waje Mammie, saboda nan akwai baƙin da zasu fara zuwa yau, zuwa anjima gidan nan ya cika, gashi kuma akwai al'adar da muke so mu cika tunda mu yanzu a wurin mu auren fari ne zakiyi."

Da yanayik damuwa Ummu tace "To amma aunty..."

A taƙaice Mamie tace "Kiyi abinda nace aunty."

Da sauri ta sake cewa "Amma aun..."

Mama ce ta É—auki cokalin dake cikin kofin shayi tayi kamar zata jefa mata tana faÉ—in "Yau ni naga iskanci, ke Ummu abinda ta ce kiyi É—in n..."

Tuni Ummu ta miƙe tana wartar bredin dake hannun Nabila ta nufi ɗakin ta tana faɗin "Na tafi Mama, na tafi wallahi."

Da kallo suka bita inda take ta kunkunin _"Wai saboda Allah me yasa suke mata haka? Sai wani rainon ta suke kamar Kuwailat ce zasu ma aure? Basu san ta girma bane wai? Shekara nawa gareta saboda Allah? Sai a dinga mata abubuwa irin haka, ga ta da jikin girma ma sai sun sa ta karya ƙashin kwankwason ta wajen gudu."_

Ba jimawa ta fito a shirye da duk abinda take da buƙata tana ta turo baki, saida ta je wajen Hajia tana ta ƙorafin tana kallo z'a tura ta wani wuri? Sannan Nabila ta same ta anan suka wuce inda dreba ke jiran su.

********************

Gashi dai ya bar garin ne wai dan ya samu nutsuwa ya kuma sake yin nesa da masu kawo mishi zancen ne irin na marasa lafiya, amma abun ya ƙi fita a ran shi, shi fa har zuciyar shi yake jin sun aikata kuskure da wannan furuci da sukayi, hakan yasa gashi dai ga Hassan yana ta mishi hira, amma ya kasa sakewa saboda akwai abinda ke ran shi ƙwarai kua yake damun shi, idan ma yayi dariya ko murmushi take kake fahimtar irin yaƙen nan ne kawai.

Suna shirin kwanciya bacci Hassan É—in ya dubi Jabir yace "Da gaske gobe zaka fara zuwa wajen malam Muhammad Sani? Dan gaskiya mun fi kusa da shi sosai, kuma kaga a masallacin nake sallah isha'i kullum, idan dai ba wani uzuri ba ya kama ni kamar dai yau da bamu samu zuwa ba."

Jinjina masa kai Jabir yayi yace "Ummm!" Sai kuma ya ga kamar rashin dacewar amsar sai yace "In sha Allah, abinda ya kawo ni kenan, gwara na fara da wurwuri."

Jinjina kai Hassan yayi yana sak rigar filon d Jabir zai kwanta yace "Allah ya kaimu."

Da "Ameen." Jabir ya amsa yana saka safar ƙafar shi irin ta baccin ne ta zallar audiga, yana gama gyara masa ya miƙe tsaye yana faɗin "Bari na faɗawa Jibril ya sanar da Hajia muna buƙatar abun kari da wuri idan Allah ya kaimu, dan ka karya kafin k fita."

Sunan Jibril da Hassan ya faɗa ya saka Jabir ƙura ma Hassan idnu yana kallon shi, sunan Jibril... Ba wai ya tsani sunan bane, sai dai ya tsani wannan ɗayan mai wannan sunan, bayan tunawa da sunan shi ma sai ya tuna har abinda Abba ya faɗa mishi na cewa _"Idan bai amince da auren Maama ba, to Jibril ɗin da baya so shine zai aure ta."_

A rikice ya miƙe tsaye wani sabon tashin hankali na ziyartar shi, yada yake zaro idanu da fara safa da marwa ya sa Hassan dakatawa ya kalle shi yace" Ya dai Jabir?"

Girgiza kai Jabir yayi ya kalle shi, shi ma bai sani ba, ji dai yayi yana nanata sunan Jibril da Maama? Jibril ya auri Maama? Bayan kuma ya san ƙudurin shi? Idan yayi haka ai bai kyautawa kowa ba kuma, tunda ya san manufar shi ba mai kyau bace, ita kan ta maaman bata sani ba.

*To ko dai ya amince ne*? Ta hakae kaɗai zai kuɓutar da maama daga sharrin shi, dan ba zai sake magana akan maneman ta ba ya ce a maya magana, ba kula zai ce a fasa auren ba a fasa tunda dai shi ba kowa bane wajen su, amma idan ya amince da auren, to dama da zai kuɓutar da maama daga sharrin Jibril. To amma kuma maama fa? Maama zai aura jama'a? Shi ya yarda a ɗaura masa igiyoyin da Abba ya kasa iya ja? Ya Allah? Shi matsalar ba ma zai yarda a ɗaura masa su bane bare har mutane su samu abun yayatawa, ai da ya yarda an ɗaura da ya tabbatar Jibril ya cire idanun shi akan maaman shi sai ya saketa.

Wannan tunani barkatai da ya jima zaune yana yi har ta sa shi bayan yayi alwala kamar yadda ya saba yayi raka'a biyu biyu har shida, sai yayi biyu daban da niyyar istikara sannan yayi addu'ar da ya inganta ana karantawa (sallah istikara tana da mahimmanci a rayuwar mu, inji malamai hatta a zaɓen wanda zai shigabance mu), daga nan kan sallaya yana ta ambaton Allah neman zaɓi a gurin shi har bacci ya ɗauke shi daga zaune bayan asuba ta fara gabatowa.

Duk da a cikin bacci ne amma yanayin na masa daÉ—i sosai, idan ta shine ba zai farka wannan lokacin ba, amma kiran sallah da ladan yayi ya zaburar da shi daga farkawa baccin nan da ya masa mugun daÉ—i daga zaunen, amma abun mamaki da ya so bashi tsoro sai ya haÉ—a idanu da Hassan da shima yayi sallan daren ya kwanta kuma kiran sallah ne ya farkar da shi yanzu ma, mamakin Jabir yake da ya ga yana bacci amma yana ta wangalar baki yana dariya, wallaho sai ya mishi sak irin yadda yara ke yi idan suna bacci suna dariyar nan.

Motsawa yayi yana gyara zaman shi da matsa wuyan shi da ya ji yana masa ciwo, idanun shi kuma akan Hassan a hankali ya firta "Ya dai Hassan? Lafiya kake zaune haka kana kallona?"

Gyara zama Hassan yayi yace "Ai kai zan tambaya Jabir, kai dake ta sheƙa dariya cikin bacci kamar wani jariri."

Haɗe fuska yayi, duk da Allah bai saka shi mai wani tuna mafarki ba idan yayi, amma sai na yau ya ɗan so tsaya mas a ƙwaƙwalwa shi ma ba wai duka ba, ƙwarai zai iya tuna a baccin shi yana cikin farin ciki ne da jin daɗin da ya fallasa sirrin zahiriyar fuskar shi. *Maama*? Anya kuwa, shi Jabir wai me ke damun shi? Da gaske dai ubangiji na nufin *aure* zai haɗa shi da maama? Ya yarda da istikhara ɗari bisa ɗari, hatta ginin gida da zai yi sai da yayi istikara, mota da zai siya ma haka har kasuwancin shi ma, kai ba ya komai ne kusan sai ya yi ta dan samun zɓin Allah, musamman tunda ya ji falalar ta kuma ya ga idan yayi yana samun dacewa kan abinda ya sa a gaba.

Amma idan yayi istikara kuma yadda dama ƙa'idar ta take, ba wai za ka ga wani abu na musamman bane da zai nuna maka ka aikata abun da ka saka gaba, a'a malamai sunyi ittifaƙi kan zaka ji nutsuwa ne na ka yi abun idan shine alkairi, idan kula bari ne to za ka ji abun na fita a ran ka ne, sannan akwai wanda ubangiji zai saka maka wasi-wasi kan yi ko barin, to anan sai ka nemi shawarar manya da dattawa, ko kuma ka duba wanda ya fi alkairin sai kayi. *A* yau kum a yanzu da ya yi istikarar sai yayi mafarkin ga maama cikin shiga irin ta larabawa farare tasss tana ta dariya bayan idanun su a cikin na juna suke, ba wannan ba ma! Tashin hankali da tunanin da ya wuni yana yi har lokacin da yake tsaye yana sallah nan, yanzu bayan farkawar shi sai ya ji shi wani irin shaƙat haka kamar ba mai ɗauke da wannan yanayi da ya kasa tantance na baƙin ciki ne ko alhini.

Bai kula Hassan ma sai ban ɗaki da ya shige ya ɗauro alwala, haka Hasan shima alwala yayi ya fito suka nufi masallaci, suna hanya Jabir na tasbihi da tahmidi har suka isa, suna kaiwa ƙofar shiga sukayi addu'a suka shiga, basu zauna ba saida sukayi tahiyatul masjid sannan suka zauna, bayan an kira sallah na biyu ma suka gabatar da salatul fijir sannan suka sake zama na daƙiƙu. Nauyayyar ajiyaro zuciya Jabir ya sauke ya lumshe idanun shi, ƙwarai nutsuwa yake ji na saukar masa daga tafin ƙafar sa har zuwa kan tsakiyar kan shi, sai kawai ya ji ya zai yi? Ba zai iya ci gaba da jan wannan rigima ba, dama kuma *wata kokawar* ta fi ƙarfin iyawar ɗan adam ko aljan, lallai a yanzu da ya nemi zaɓin Allah kula ya saka shi jin nutsuwa game da lamarin, to ya yarda shine ya rubuto musu haka, dan haka basu da tsimi bare dabara daga shi har ita Maaman, shi dai kam za yarda dan yayi biyayya ga umarnin Allah, sannan ya zama ɗaya da suka ɗaffaka sunnar da aikatata yayi ƙaranci a cikin al'umma, dan haka *daƙiƙa biyar* ba zai sake ɓatawa ba wajen sanar da iyayen shi ya yi biyayya ga umarnin su, dan bai san me suka hango mishi game da tarayyar nan ba da shi ya kasa hangowa, dan ya taso ne a rayuwar shi bai san so ba barz ya san yadda ake jin shi, duk da dai ya musa abinda Aliyu ya faɗa cewa wai yna son maama, bai san menene so ɗin ba, amma fa kuma bai yarda yana son maama ba, dan idan yana son ta ai zai gane ko ya ya n je tunda shi ba *dutse* bane.
Chapter 142 · 0% Book details