← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 168

Sashe 128

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ya sake juyawa ya ci gaba da tafiyar shi har ya fice a gidan, Fahad bai san me ya faru ba a waje, amma da ya sani wataƙila a yi ɓatacciya sosai, dan kuwa Ummu ƴar ɗan uwan sa ce, amma shi a ran shi kamar ƙanwa ko wacce aka haife su tare yake kallon ta dan shekarar su ɗaya, ya kuma san Jibril wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda yake ma nasiha da su bar abinda suke su tuba kamar yadda shima ya yi, yanzun haka ba dan sabga ce da yake buƙatar mutane dayawa ba da ba ruwan shi da Jibril da ma ire-iren shi da suka zo maa sabgar nan. Waɗanda suka gani kuma masu nutsuwa ne da basu tayar da zancen ga kowa ba face tsakanin su da suka sake tattauna abun, daga nan kuma suka bar shi kawai ya wuce a zuwan saɓani ne.

*An* sha biki sosai an kuma yi lafiya an gama lafiya, an ma amarya kwalliya an ɗauke ta hotuna da ƙawayen da suka zo cika mata taro da kuma ƴan uwa da abokanan arziki, dan zuwa safiyar gobe za'a ɗauki hanya da amarya, hakane yasa tun daren su Yaya Luƙman suka gana da ƴar uwar su har Mama ma ta mata nasihar da zata iya yi mata, inda kuma Ummu da babbar Yayar su Mama da ƙanwar Baba (margayi) sai wacce ke kamar Kaka ga Nabila ta wajen uba ne zasu rakata zuwa ɗakin ta, da wannan shirin aka kwanta huta gajiyar yau da aka ɗauka kafin a shiga ta gobe.

*WASHE GARI*

Ƙarfe 09:20 mota uku daga wajen sj Fahad ta zo, kamar an ce wa Nabila ga motar da zata ɗauki ran ta nan sai ta fashe da wani kuka, har aka gama ɗaukar iya abinda motocin zasu iya ɗauka a bayan motar su dan tuni motar kaya masu yawan tayi gaba tun daren jiya, da ƙyar su Inna suka raba su har da Ummu wacce ita ma da shirin tafiya ta kwana biyu ne zata bar garin, sai gashi ita ma kukan take, saida Yaya Luƙman ya mata jan idanu yace "Ummu zan fa ci uwar ki, me ye haka wai? Kinga dama dan kina matar mai gidana ne bana son taɓaki, yanzu ko sai in zane ki."

Ƙanwar Mama Kubra ce tace "Haba Luƙman, ka bisu sannu mana, dole suyi kuka ai."

Ƙwafa yayi bai ce komai ba dan shi fatan shi ya ga tafiyar su kafin ya je kiran da Alhaji Kabir ke mishi wanda tun jiya ya ce ya zo idan baya komai, da ƙyar da suɗin goshi aka raba su kowace ta shiga mota Mama na kuka su suna kuka aka tafi cike da ɗauki da kewar junan su, inda Mama ta shiga bin su da addu'a. Ummu kuma sanin sai an yi ta koke koke yasa jiya ta sa aka maida Kuwailat gida ta ƙi yarda ta kwana, kuma ce mata tayi zata tura a ɗaukoya da wuri dan suyi sallama, share wa ne kawai ta yi idan ta zo ta ga bata nan ai ba zata ga kukan d zatayi ba bare ta ɗaga mata hankali.

Hanya kam sun sha ta sosai dan har dare sannan suka shiga, sun samu tarba mai ban mamaki na abinci da sakin fuska, dan kuwa Nabila ma a cikin katafaren gidan nan aka ware mata na ta ɓangaren kamar dai yadda yake burin Alhaji, suna gama ci da sha wanka sukayi ɗaya bayan ɗaya inda Ummu ta musu sallama ta nufi ɓangaren Maman ta anan ta kwana.

*MARAÆŠI*

Da ladabi Yaya Luƙman yake zaune gaban Alhaji da shima yake kallon shi cikin dattako yace "Luƙman, kasan me yasa na kira ka?"

Girgiza kai yayi ba tare da ya kalle shi ba yace "A'a Alhaji."

Numfashi ya sauke sannan yace "Luƙman, shekaran jiya Jabir ya zo nan yake faɗa min ya ga Ummu da wani tsoho suna hira, a yadda ya faɗa min kamar ma ya fini shekaru, sai nake ta tunanin to ita kuma me zai kaita kula wanda ya fini? Bayan kuma ta san abinda ya rabamu da ita, kuma ina tunanin kuma kun sani, amma me ya san kuka ƙyale ta?"

Da mamaki Yaya Luƙman ya kalli fuskar Alhaji yace" Tsoho kuma? A gaskiya Alhaji ban san da wani na neman auren Ummu ba bayan Alhaji Haris, kuma ina ga da akwai ko Mama ba ta faɗa min ba ita zata gaya min da kan ta."

Alhaji ma kallon shi yayi yace" Wane Alhaji Haris É—in?"

A ladabce yace" Alhaji Haris dai wannan, Mado."

Gaban Alhaji saida ya buga da ƙarfi, to ana nan dai, shi kam da ya bar Ummu ta auri Alhaji Harisu ai gara ya maida ita ɗakin shi wallahi, komai lalacewar shi dai zai iya soka mata allurar shi ko da bata tsikare ta da kyau ba, amma Alhaji Haris? Kallon Yaya Luƙman yayi yace "Amma kuma kai kasan da haka kuma ka ƙyale ta take ci gaba da sauraren shi?"

Da ladabi Yaya Luƙman yace "E to Alhaji, dake ban san komai a kan shi ba gaskiya sai alkairi, kuma naga sun fara fahimtar junan su."

Girgiza kai Alhaji yayi yace "Kayya ! Luƙman ka gaggauta dakatar da alaƙar su koda tana son haka, nasan abubuwa dayawa game da Alhaji Harisu Mado, ba zan ce maka komai ba saboda kar kuyi tunanin alaƙata da Ummu za ta sa na fara mata wannan cunen, amma ka kira Alhaji Sagir ka tambaye shi wa ye Alhaji Harisu Mado, zai faɗa maka komai da ya sani."

Shiru Yaya Luƙman yayi na sakanni kafin ya jinjina kai yace" Shikenan Alhaji, nagode sosai, wallahi ban san komai ba, kuma na ɗanyi tambaya a kan shi duk maganganun alkairi ne suka fito daga bakunan waɗanda na tambaya ɗin."

Suna yin sallama tun a mota ya kira Alhaji Sagir, dake dama suna gaisawa ma ta waya bai wani tsaya faɗa masa wanene ba, yadda sukayi da Alhaji ya faɗa masa komai sannan ya tambaye shi? Numfashi Alhaji Sagir ya sauke sannan yace" Luƙman, ka datse alaƙar Ummi da Alhaji Haris, a baya ban maka musun shi mutumin kirki bane, amma sama da shekara goma Alhaji Haris maganganu na yawo a kan shi cewa ana hulɗa da malaman duba wanda zamu iya kiran su da bokaye, akwai wasu abubuwa da yake yi da ya sa dole ake zargin shi da shirka ko aikata sihiri, ka ga Alhaji Haris duk kasuwancin d zaka zo mishi da shi indai anyi sallah magriba to baya kula ka koda kuwa kasuwar ta kai ta milyan ɗari, ni nan kaina na neme shi da harka da daddare amma ko wayata bai ɗaga ba, sannan matan shi dake gidan shi yanzu ba sune matan shi na farko ba, waɗannan suna zauke ne saboda dukiya, amma an tabbatar da wata mu'amula ta aure bata haɗa shi da matan shi saboda mummunar alaƙar da yake da tsakanin shi da maza matasa, dan abinda zan iya faɗa maka kenan a kan shi, amma ka sake bincike da kyau ka tabbatar."

Zufa yaya Luƙman ya share yana feso iska har Alhaji Sagir ya yanke kiran bai sani ba, ya Hayyu ya Qayyum! Ka ga mutum a mutumce amma ace maka da dai sauƙi ɗabi'ar shi? Ya Allah!

Dan kar ya É—agawa Ummu hankali ya sa bai kirata a lokacin ba dan ya san suna kan hanya, amma fa *gari na wayewa* ya kirata ko tashi ba ta yi ba tana gadon Mama Nuriyya tana bacci a nutse kiran shi ya tashe ta, ya É—auka zata shiga damuwa ne, amma sai ya ji tace "Allah ya kyauta, nagode Yaya Luda ban sakankance da shi ba, shi kuma Allah ya shirya shi idan mai niyya ne."

Kwanan da bata koma ba kenan, duk da bata ji zafin rabuwa da shi da zatayi ba, amma dai halin nashi da aka faɗa abun ya taɓa ta ya kuma bata mamaki, sai take ganin yanzu duk nutsuwar nan tashi? Ya rasa wa zai nema sai maza? Ya Allah!

Ƙwarya ƙwaryar walima aka sake danƙarawa a gidan saboda murnar zuwan amarya da kuma Ummu cikin wannan ahali, rana ta biyu kenan da Ummu ta sake caɓa ado na ban mamaki, sannan ta cancare a cikin riga da siket na leshi da ya karɓi jikin ta ya kuma zauna mata ɗas, biki ne dai na taya juna murna da farin ciki, amma a wajen wasu sai ya zama har da yaɗa manufar su a fili wajen babbar jikar margayi Saheeb da aka tabbatar musu zawarci take. *Larwan* ma ya kasance jika ne ga ahalin Ahlan, dan mahaifiyar shi ma ita ce babba ga su Alhaji wacce ta jima da rasuwa, gaba ɗaya shekarun sa basu fi arba'in da biyu zuwa da uku ba, yana da mata ɗaa da yara biyu kasancewar shi riƙaƙƙen ɗan kasuwa kuma mai ilimin boko, ba ra'ayin sa bane auren mace biyu, amma da ya ɗora idanun shi a kan Ummu kuma ya tabbatar bata tare da mijin ta, yanayin ta da sanyin maganar ta, kyawun ta da zubin tsarin ta duka ya birge shi, sai kawai a take ana tsaka da bikin abun ka ga ɗan boko ya sanar da Yayar shi *Nargis* akan yana son Ummu, ɗari bisa ɗari ta bashi goyon baya, sai dai kuma... Ita ta ta manufar da ta sa ta amince bai wuce yadda bata so damar auren jikar Saheeb Ahlan ta kubce musu, ta sani ne yarinyar za ta kwashi arziƙi, dan akwai abubuwa dayawa da Abbu Mukhtar ke yawan furtawa da sunan ƴar sa Kuwailat da Eesha, bugu da ƙari bayyanawa ne ba'a yi ba, amma Alhaji margayi ya mallaka wasu manyan masana'antu ga jikar sa ta farko da aka fara haihuwa wato Kuwailat (Ummu), an bar maganar ne kawai saboda ɓatan ta, amma yanzu tunda ga ta tasan za'a taso da duk wata magana ma dake binne.
Chapter 128 · 0% Book details