← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 168

Sashe 50

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sigar zolaya yace "Dan ɗan kwali ? Bari na ƙarasa ɗaura miki." Ya faɗa yana matsawa inda take, Aisha kuma ƙarasawa tayi ta aje jakar Hannunta inda taga maman ta na ajiyewa, tuni ko ya zaunar da ita gaban madubi ya fara durfafa mata ɗaurin, dariya Aisha tayi ta zagaya kusan su tace" Gaskiya Mamie ki bar min Abbuna ya huta, ni zan ɗaura miki."

Dariya yayi yana matsawa gefe saboda ƙoƙarin kama kallabin da Aisha ke yi yace" Nagode sarauniyata, Kinga ƴa ta fanshi Abbun ta."

Kallonshi tayi duk da Aisha ta fara mata É—aurin tace" ÆŠaurin ma da nasan dama ba iyawa za'a yi ba."

Da sauri Aisha ta ƙarasa mata ɗaurin ganin Abbun ta na cire machete ɗin hannun shi alamar zai cire kayan jikin shi ya shiga wanka, tana gama ɗaura mata tace" Mamie duba madubi kiga, nasan baki taɓa irin wannan ɗaurin ba."

Miƙewa tayi daga kujera ta juya kan madubi tana dubawa, yayi kyau kam ɗaurin, juyowa tayi dan yi ma Aisha magana sai taga har ta janye Kabil sun bar ɗakin, dan haka ta ƙarasa kusa da mahaifin nasu dan taya shi wanka da duk abinda ta san ta saba yi mishi a wannan lokacin.

Suna cin abinci a falo cike da raha da jin ina ma ɗaya ƴar su tana nan? Ai da farin cikin ya fi wanzuwa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya danna alarme na ƙofa, juyawa sukayi suka kalli ƙofar, sai kuma mai aiki da ta fito kai tsaye ta nufi ƙofar ta buɗe, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne sukayi magana sannan ta maida ƙofar ta rufe ta dawo inda suke da ladabi ta tsaya tana kallon Abbu tace "Yallaɓai, wai kayi baƙo a waje, ya ce yana son ganin ka."

Kallonta yayi da mamakin wanda ya zo masa ba tare da ya san da zuwan nashi ba yace "Wa ye?"

Da ladabi tace "Bai faɗa ba, amma dai ya ce a ce wai baƙo ne, kuma sunan shi Sa'ad ne."

Da mamaki ya sake ƙanƙance idanu dan shi har ga Allah ya ma manta da sunan wanda ya taimaki Aisha, hakan yasa ya shiga waina idanu yana son tuna inda ya taɓa jin sunan. Mama Nuriyya da ta kalli Aisha tunda aka ambaci Sa'ad ta ga tayi wani iri ta zaro idanu tace "Eesha, ko dai mariƙin ki ne?"

Kallon Maman nata tay da yanayin rashin gaskiya tace "Ban sani ba Mamie."

A kausashe Abbu ya kalli Mamie yace "Ba dai mariƙin ta ba, sai dai mazalincin ta, wanda ya nemi halaka mana yarinya?"

Tsaki yaja tare da kallon mai aikin yace "Kinga, ki je kiga idan har shine wanda yake ikrarin ya taimaki Eesha, to a gaggauta fitar min da shi daga nan, bana son sake ganin shi a rayuwata."

Yana faÉ—a ya maida hankalin shi kan cin abincin shi, tunda yayi maganar Aisha ta zuba mishi idanu kamar za ta fashe da kuka tana kallon shi, Mama kuma tsaf take lura da ita har mai aikin ta fita daga falon, tsakurar abincin kawai ta shiga yi tana jin duk ba daÉ—i, zuciyar ta kawai raya mata take ta tashi ta je ta same shi, amma kuma bata so tayi hakan gaskiya.

Suna haka mai aikin ta dawo falon, kai tsaye wajen su ta sake nufowa saboda saƙon da Sa'ad ɗin ya bata, ita kanta sai da ya bata tausayi da ta ga ya juya jiki a sanyaye ya fita bayan takardar da ya bata ta ba Aisha, tana zuwa kam ta tsaya ta miƙowa Aisha takardar tace "Hajia ƙarama , in ji shi wai a baki."

Da sauri abin ka da wanda zuciya ke marari ta sa hannu zata karɓa, sai kuma suka haɗa ido da mahaifin ta dake mata wani irin kallo mai tarin tambayoyi da mamaki, ƙin karɓa tayi tare da sadda kanta ƙasa ta furta "Ku gafarce ni."

Da sauri ya sa hannu ya karɓi takardar ya shiga warwarewa, inda mai aikin ta bar wurin shi kuma ya karanta gajeran saƙon kamar haka _"Na tafi, amma zan dawo gobe ma, saboda ina sonki, kuma na zo ne dan na koma dake a matsayin matata."_ Cikin jin haushi Abbu Mukhtar ya kalli Mama Nuriyya ya nuna mata takardar ya ce" Ki ji fa, me yaron nan yake taƙamada shi? Ba Ya ce gobe zai dawo ba? To ya zo, wallahi da jami'ai zan haɗa shi."

Ƙwarai tayi jarumtar riƙe hawayen da suka cika mata idanu, amma da ya ambaci jami'ai sai ta ture farantin gabanta ta miƙe da gudu ta nufi kusurwar ɗakin ta, dan fashe musu zata yi da kuka duk da ita ma bata san dalili ba. Da kallon mamaki suka bita, sai kuma Mamie da ta haɗa da kallon tausaya mata, to ya zasu yi tunda ya gama yi musu illa? Duk da ba haka ta so ba, amma ba zata bari hakan ya zama silar shiga damuwar ƴar ta ba, za ta mata duk abinda take so saboda ita kaɗai gare ta.

*WASHE GARI*

Tayi ɗaukin shi a makaranta yau ma kamar jiya, sai dai sam bata gan shi ba har suka gama ta dawo gida, haka ta wuni ba fara'a ba walwala, hatta sashen aunty Abida bata leƙa ba ko sau ɗaya.

*Da* yamma tana saman bene wurin da aka ware dan shan iska tana karatu, dake tsaye take tana ɗan kai da kawowa saboda abinda take so ta hardace a kan ta, kamar an ce ta juya saitin ƙofar shigowa ta hangi Sa'ad da jami'in dake tsaron ƙofar suna gaisawa da fara'a kamar dai sun san juna, amma sai ta fahimci kamar ba zai bari ya shigo ba dan yadda taga yana ma Sa'ad ɗin magana a nutse kamar kwatanta masa wani abu yake, yayin da shi kuma yake sake bashi hannu da jinjina kai sannan ya yi niyyar juyawa zai fita, da sauri ta dawo ta ɗauki wayar ta dake kan farin teburin tare da jakar ta, wata gajeruwar lamba ta rattaɓa sannan ta ɗora a kunne, tana kallo jami'in ya zagaya ya ɗauki wayar tangarahon dake nan yana faɗin "Na'am."

Da sauri Aisha tace "Ka shigo da shi, na san shi."

A ladabce duk da ya san wacece yace "Hajia ƙarama nima na san shi, abokina ne ai, amma jiya Alhajin Kabil ya bamu umarnin kar mu sake barin shi ya shiga."

A É—an kausashe tace "Ni nace ka bar shi ya shigo."

Da ladabi ya sake cewa "Kiyi haƙuri Hajia ƙarama, wallahi Alhajin Kabil ya mana alƙawarin ɓacin rai idan muka barshi ya shiga, abinda na kwatanta masa kenan kuma ya fahimta, duk da dai ya ce zai dawo ko da za'a kashe shi."

Cikin jin haushi da takaici ta aje wayar tare da tattare kayan ta da sauri ta shiga sauka daga benen riƙe da jakar ta, tana dirowa falon su Mamie na zaune da wayar ta a hannu da kuma wasu tilin wasu shaddodi gaban ta na ankon bikin Abida da ita aka ba kwangilar fiddowa, tsaye tayi gaban ta a rikice tace "Mamie, me yasa Abbu zai ce kada a bari Sa'ad ya ƙara shigowa?"

Da mamaki ta kalle tada rashin gane gaban zancen tace "Sa'ad kuma? Shine ya gaya miki? Yaushe aka yi haka ma ban sani ba?"

A tsaurare tace "Mamie, gashi can ya zo amma an hana shi shigowa, wai ya ce Abbu ne ya basu umarni kar su bari ya sake shigowa."

Ajiyar zuciya Mamie din ta sauke tare da tara mata hannu alamar ta taho, ƙara gimtse fuska Aisha tayi ta turo baki tare da yin takwaf takwaf da fuska alamar za ta yi kuka, hakan yasa Mamie yin murmushi tace" Haba sarauniyata, zo mana in ji."

Hannun ta miƙo mata a sanyaye ta matso ta zaunar da ita kan cinyar ta, ƙurawa fuskar Aisha idanu tayi tace" Uhum! Ina jinki! Me ye tsakanin ki da Sa'ad ɗin nan ne?"

Girgiza kai tayi à sanyaye suna kallon juna tace" Ba komai Mamie, amma ai ya taimake ni, bai kamata a mishi haka ba, tunda dai bai muzguna min ba a zamana da shi."

Murmushi tayi ta jinjina kai tace" Hakane, to me ya sa naga kina damuwa da shi sosai? Kin tabbata ba son shi kike ba?"

Da sauri ta waro idanu ta kalle ta tace" Mamie, so fa ? A'a wallahi, ni kawai Abbuna na É—auke shi."

Ba tare data daina murmushi ba tace" Ki faÉ—a min gaskiya Eesha, zan taimaka miki ne ai."

Cikin shagwaɓa sosai ta turo baki tace" Mamie ba komai ba."

Jinjina kai ta sake yi da sigar zolaya tace" Amma ai shi ya ce yana sonki, shin ke ba kya jin son shi ne?"

Da sauri Aisha ta sa wutsiyar kallabin ta ta rufe fuskar ta saboda kunya, rumgumata tayi a jikin ta tana dariya tace" Na ganoki sarauniya, karki damu kin ji, zanyi magana da Abbun ki idan ya dawo."

Jinjina kai tayi ta miƙe daga ƙafafun ta ta nufi ɗakin ta cike da kunyar abinda tayi har Mamie ɗin ta gane ta. Sa'ad kuma kamar yadda ya faɗa zai dawo, yana idar d sallah magariba ya sake dawowa da burin ganin mahaifin Aisha ido da ido, ba zai yi hushi ba, ba kuma zai ɓata ran shi ba dan ƴarsu yake so, kuma yana ganin tashi soyayar a idanun ta ita ma, dan haka ba zaiyi abinda zai kawo naƙasu a yi musu biyayya ba.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Chapter 50 · 0% Book details