← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 168

Sashe 56

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani irin masifaffen kallo ya bita da shu'umin murmushi yace "Ko ma haka ɗin ne ai kin san kin kai a so ki dan hakan, bare kuma ni ina ji har ƙarshen rayuwa nake so mu rayu."

Sake yatsina fuska tayi tana ɗauke kai tace "Idan ma aure ne ya kawo ka gaskiya ban da lokacin shi yanzu, dan sai da aka so yi mi auren nan amma na ƙi, dan haka zaka iya ƙarawa gaba ka nemi wacce ta shirya aure."

Tsareta yayi da idanu yace "Me yasa? Me ya sa ba kya son auren yanzu?"

Waina idanunta tayi tana taɓe baki tare da gyara tsayuwar ta tace "Ba wai ban isa auren bane, dan kai da gani kasan zan iya zama da kowane irin namiji, kawai dai ina da wasu burika ne da nake son cikawa kafin auren, idan kuma auren ya gaggauta zuwa min ban shirya ba, a gaskiya kashe shi zanyi na fito na yi rayuwar da nake sha'awa, daga baya na sake yin wani auren."

Murmushi Fahad yayi jin wani dace, dan kuwa Ali ne ya ga Ali ai, shi ma gyara tsayuwar yayi yace" Tunda hakane, me zai haka mu fara gudanar da rayuwar da muke so, daga baya sai muyi auren."

Wata shaƙiyiyar dariya Nabila tayi tana kallon shi tace" Mahaukaci, ta ya kake tsammanin zan yi rayuwar da nake hasaso ma kaina da kai, sai kuma na ƙare da auren ka?"

Gyara tsayuwar shi ya sake yi sosai tare da rumgume hannayen shi a ƙirji yana kallon ta ba alamar wasa yace" Idan kin yarda zaki yi soyayya dani, ni zan iya yi miki komai da kike so a rayuwa, amma sharaɗina shine ba zaki kula kowa ba, ina da kishi da kuma ƙyanƙyami, hakan zai sa ko *bayan abada ma dake kawai zan rayu*, ke ma kuma baki da wani zaɓi da ya wuce ki rayu da ni."

Cike da shaƙiyanci Nabila ba tare da tayi tunani akan abinda ya faɗa ba ta kalle shi sama da ƙasa sannan ta ɗauke idanun ta tace" Ka tabbata za ka iya riƙe ni?"

Kusa sosai ta yadda kaf jikin su ke gugar na juna ya matso ta da salon nashi shaƙiyancin yana ɗora hannayen shi a mota ya mata rumfa yace" Shafa da kyau kiji, dan ki tabbatar zan yi."

Wannan shine mafarin sake fanɗarewar Nabila gaba da baya, tun da ƙuruciyar ta dama dalilin gidajen haya rayuwar ta ta fara gurɓacewa, sai dai duk da haka tana riƙe da budurcinta saboda dogon burin ta da son ganin wanda ya dace da ita, sakamakon shigowar Fahad rayuwar ta kuma sai ta damƙa mishi ragamar komai nata har da mutumcin kan shi, tamkar wasu miji da mata haka suka fara rayuwa a gidan da suka kama haya kafin tafiyar su. Shaƙuwa tayi shaƙuwa, soyayya ta kai soyayya sai dai gurɓatacciya, ido sun ƙara buɗewa Nabila inda ta sake kankaro wulaƙanci da rashin mutumci, tana juya kuɗi yanzu yadda take so, dan da babbar waya tana cazar duk gaulan da ta so kuɗi, amma kuma bata son ta haɗu da kai bare ka nuna ka na da buƙata gare ta, dan kuwa alƙawari ne da ta riƙe la Fahad ba wanda zata ba kanta bayan shi.

Da wannan suka zama tamkar tamtabaru, sun daina zama a gidajen su sai lokaci lokaci, kullum suna cikin yawo da fita garuruwa shagulgula, wani sa'ilin ma zai kawo mata ziyara har garin ta, sai ta tare à wajen shi har sai ya tafi. Garin hakane har Nabila ta fara koyon busa sigari a hannun Fahad, kawai yana sha ta same shi, ranta ɓace na faɗan da Mama ta mata da nasiha sa kawai ta kar;e karan ta zuƙa, tari ta fara yi kamar za ta mutu, sai ya karɓa ya shiga nuna mata yadda ake yi, da hakane sai komai ya sake lalacewa.

Hakan jarabta ce, wataƙila ta wani kuskure da suka aikata ko kuma dai dan jaraba imanin su, ba dan haka ba duniya za ta yi mamaki a ce ƴar Mama Amina uwr marayu ce a wannan rayuwar, magana dai kam ba ta wanda take ji, bata sauraren kowa bare ta nutsu, fata da addu'ar shiriya kawai Mama da duk wani makusanci da abun yake damu suke kan yi.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.

Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._

_Bismillahir-rahamanir-rahim._

*27*

Cikin tashin hankali Mama ta haɗa kanta da hannun kujerar zaman mutum ɗaya ta rufe fuska da hijabi tana kuka za ka rantse da Allah ita ce ake duka, Nabila kuma da Yaya Luƙman le mata dukan sababi a falo kuma ya rufe ƙofa ihu kawai take da neman ceto da agaji amma babu mai kawo mata ɗauki, ta kai shi maƙura yau ta yadda a karo na biyu ya sake taɓa lafiyar jikin ta, ba son ran shi bane a ce kamar shi da iyalin shi ace yana dukan balagaggiyar ƙanwar shi da ke ɗauke da shekara *ashirin da shida*, a ce wai gawurtar Nabila ta kai yanzu har tana iya share wata uku babu ko wanda ya ce ya ganta ma bare ta leƙo gidan, wata uku fa! Akan wane dalili, dan kawai sun ce za su aurar da ita ga abokin shi? Tunda ita ta ƙi fito da mijin, yaron kuma da aka mata tsakani da shi ta ƙi fita harkar shi.

Ba wai rashin dawowar bane babban tashin hankali, yadda Nabila ta dawo musu gidan ne ya sake ɗaga hankalin su, kamar yadda da ta ji matsa a hannun Yaya Luƙman ɗin take faɗa mishi tana Niamey, daga can wa ita da ƙawar ta suka je aka musu allura wacce take saka hasken fata, madadin shafe-shafen mayuka an samu ci gaba sai dai allura kawai, shine Nabila tayi wani irin haske kamar zabiya ga wata ƙiba da tayi mai kyau fa dan kyau, to bayan dukan da tasha ne yake tambayar ta wannan sarƙar ta ƙafar ta fa, dan shi yana ji a cikin gari ai ya kuma san me haka ke nufi a wasu lokutta, shine ta rantse masa da Allah ba ta harkar matan banza, hasalima ko maza bata kulawa bayan Fahad, kawai shi Fahad ne ya ce hakan na birge shi sai ya siyo mata ta zinare ta saka.

Cikin tashin hankali Mama ta rufe kunnuwan ta dan ta gaji da jin sunan wannan Fahad da Nabila ke ta ambata, Yaya Luƙman kuma dake ɗaki da ita wata shaƙa ya ma wuyan ta a matuƙar hassale yana faɗin "Shi kuma wannan askin fa? Na rashin mutumcin gidan uban waye? Aski fa Nabila ? Kina mace? Baki san haramun bane? Shi ma Fahad ɗin ne ya ce kiyi ko? Tunda shine uban ki ?"

Idanunta dake warwaje duk sun fito tana ta neman ɗauke numfashi, jin ba ta ce komai ba saboda ya shaƙeta sosai ya sake ta tare da gwara kanta da bango yana faɗin" Ina jinki?"

Shasheƙa kawai take à zuciyar ta Allah Allah take ƙofr ɗakin nan ta buɗe, ta fita ko? Ta dai samu ta fita ko? Wallahi su da ganinta sai sun neme ta, Shiyasa kaf bata shiga harkar su, Ummu kaɗai take yin ta da ita saboda ita ka fi ƙaruwa ma da ita, a haka ma dan tana ɗaga ƙafa ne kan wani abun saboda Ummu, ba dan haka ba su sun isa yanzu ma su ganta ne? Ai dan Ummu ce ta ce ta zo ta ga Mama mana, shine za'a mata wannan dukan a wannan jar fatar ta ta da tayi kyau.

Aski kuma ko? Ta je tayi, kitso aka mata a salon zane mai kyau Fahad ya ce ya birge shi, dalilin haka ya tara gashin shi abunka ga buzu dandan yayi tsayi ya je aka mishi irin kitson, shine ya gora mata wai yayi kitso saboda ita, ita fa me zata iya yi? Shine ita ma ta aske nata kan aka mata irin askin da ya fi yi, yo à haka ma ai gashin ya fara fitowa ne ba kamar askin na sabo ba. Hmmmm! Yaya Luƙman kenan, kenan mutuwa zaiyi da hargagi idan ya ga tatoo ɗin dake ƙrijin ta da kuma tsakiyar ƙugun ta da na bayan wuyan ta da aka rubuta sunan Fahad? Haka kawai abi a takura mutum.
Chapter 56 · 0% Book details