← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 168

Sashe 110

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da bata jin daɗin jikin ta, amma abinda ya faru a tafiyar ta iyayen nata ya sa dole Eesha mirtsikewa ta zo masaukin nasu dan duba Maman ta, ta ɗauka Maman ta ta daina damuwa da ƴar uwar ta da ita ma bsu san inda take ba, amma yau ta tabbatar lallai maman su kawai tana taushewa ne dan ba yadda ta iya, irin kukan da take yi da hargagin kiran sunan aunty Ummu ya sa ba ta jin haƙurin da suke ta bata da rarrashi, cikin tausayawa Aisha tana rumgume da Maman nata tace "Mamie, ba dai aunty Ummu ƴar ki bace, wallahi zan dawo miki da ita, ni da kaina zan je gidan gobe ko ta ƙarfi ne sai ta zo gare ki, dan Allah Mamie ki nutsu, kinsan damuwar ki tashin hankalin mu ce."

Cike da tabbaci Mama Nuriyya ta jinjina kai tace "Ƴata ce, haka naji a jikina, kuma ita ma bata musa ba, Maman ta tana kallo ai, ta ya za'a ce ba ƴata bace dan Allah? Ta ya?"

Cikin kulawa dai Aisha tace" Hakane Mamie, su ma ina ga basu gane bane, ta ya zasu ƙi yarda dake? Basu san mun jima muna neman ta bane?"

Haka ta ci gaba da shafa bayan ta tana rarrashi har bacci ya ɗauke ta, ba wai dan ta shirya ba sai dan kukan da ta ci da kuma samun jikin Aisha tana sauke shasheƙa, ganin baccin Maman ya sa Aisha kallon Sa'ad da su ke zaune sun buga tagumi tace" Abbu, dan Allah ka min izini da safe na je gidan aunty Ummu muyi magana da ita?"

Da sauri Abbu Mukhtar ya kalle ya yace" Ki je ki ce mata me Eesha? Zato fa kawai muke, amma bamu da wata hujja ko makama."

Kallon shi tayi tace" Ina da hujja Abbu, zan kuma gano hakan da yardar Allah, ko iya abinda kuka ji daga haÉ—uwa da ita kawai ya isa ya zama hujja."

A hankali Abbu ya girgiza kai yace" A'a Eesha, hakan abu ne da zai iya faruwa ga kowa, wataƙila kawai jin..."

Da sauri Aisha ta katse shi da" Abbu ya fi ƙarfin haka, kawai ku amince naje na ganta muyi magana."

Jinjina kai yayi a kasalance yace" Shikenan, ga mijin naki nan ai."

Kallon Sa'ad tayi da bai ce komai ba har lokacin, dan shi tunanin shi daban ne akan wannan matsalar, shi so yake ya shiga lamarin ta hanyar bincike, ba kawai ta haka kowa ya dage Æ´ar sa bace, tana kallon shi ya lumshe idanu a tausashe yace" Ba damuwa, Allah nuna mana goben."

"Ameen." Ta faÉ—a har da sauke ajiyar zuciya, haka ta ci gba da shafa maman ta dan bata so ma ta farka ta sake É—ora musu rogimar nan tamkar wata jaririyar goye.

*WASHE GARI*

Tsatsaye suke yana dafe da kafaÉ—ar ta, ita kuwa sai faman share hawaye take, Alhaji da hankalin shi na kan Khamis ne ya sake duban ta yace "Yi shiru mana auta, na gaya miki Maman ki fa tana gidan su Nabila, kuma ga Khamis zan sa ya aje ki can, kinga sai ki wuni a can tunda yau juma'a dama ba karatu."

Ba ta ce komai ba sai share hawaye da take yi, Khamis da har yanzu bacci ne a idanun shi tun komawar da yayi bayan sallah asuba yace" Abba, can gidan su Nabilan zan kaita? To a can aunty Ummu ta kwana ne?"

Kallon Khamis É—in yayiya É—aga masa kai yace" E, dan Allah maza É—auko makulli ka kai min ita."

"To." Ya faÉ—a yana kallon Kuwailat da idanun ta sukayi jajir yace "Haba auta, shikenan daga aunty bata nan sai kuka? Kamar ba kowa a gidan, ba naga wajen Hajia kika kwana ba?"

Kallon ta Alhaji ke yi yana juran ya ji amsar da zata bashi amma shiru, hakan yasa Khamis nufa ɗakin nasu, sai kuma yana bada baya Aliyu na shigo tare da Aisha a bayan shi da tayo sammako, saida suka ƙaraso Aisha tayi sallama Alhaji ya amsa suka gaisa sosai kamar sun san juna, ita bata yi tsamanin shine mijin aunty Ummu ba, a tunanin ta surukin ta ne ma'ana wanda ya haifa mata miji. Dan haka suna gama gaisawa cikin rusunawa Aisha da nutsuwar ta dake kan Kuwailat mai kama da fuskar Hajia tace "Abba, dama na zo ganin aunty Ummu ne."

Gyara tsayuwa Alhaji yayi, haka ma Aliyu dake son ya ji amsar da zai bayar, ya shiga ɓangaren Ummu dan gaishe ta kamar yadda ya saba, amma sai Kuwailat dake shiri tace Mamie bata nan, ina taje da safe haka? Shiyasa da matar take tambaya nan ne ya ce e ta shigo kawai, cikin nutsuwa Alhaji yace "Gaskiya Ummu bata nan, ta fita ne, amma idan son ki da ganin ya na ujila ne to ga ƴar ta nan yanzu can ta nufa, zaku iya tafiya tare."

Faɗaɗa murmushi Aisha tayi, ƙaunar yarinyat lokaci guda yana tsarga mata tamkar ɗaya daga cikin yaran ta, hannu ta miƙawa Kuwailat da kulawa tace" Zo mana ƴan mata."

Duk da Kuwailat an zama Æ´an mata, amma haka ta turo baki ta matsa kusan Aisha, dafa kan ta tayi tana kallon Alhaji tace" Zamu iya tafiya? A mota nake."

Kallon ya shima Alhaji yayi yace" Yayan ta ne zai kaita, ya..yawwa gashi nan ma zuwa."

Jinjina kai tayu tace" Ba damuwa, ni sai na bar mota ta a nan, idan muka dawo na É—auka."

Girgiza kai Alhaji yayi yace" A'a, kuje da ita, sai ya muku jagora."

Ta ji daɗin hakan ƙwarai, dan haka Khamis na zuwa Alhaji ya faɗa mishi yadda zasuyi, riƙe yake da hannun Kuwailat har suka fita Aisha na godiya, Aliyu na tsaye gaban Alhaji yana masa wani kallon tuhuma yace" Abba, me aunty ta je yi gida tunda safe? Kuwailat ta ce min wai a can ma ta kwana? Lafiya?"

Juyawa Alhaji yayi yna kallon ɓangaren na Ummu yace" Ba komai, lafiya lau."

Cike da rashin yarda duba da jiya ai gaban su ya share ta kuma tana kuma yasa shi komawa inda yake fuskantar Alhajin yace" Abba, dan Allah ka faÉ—a min me ke faruwa? Naga kamar akwai damuwa tsakanin ku."

Kallon shi Alhaji yayi fuska haÉ—e cikin kaushin murya yace" Mun rabu da Ummu, na sake ta."

Yana faɗin haka kawai ya kama hanyar zuwa ɓangaren Hajia, haɗewa sukayi da Hayat hakan yasa shi faɗin" Ka ce Maman ka ta same ni ɓangaren Hajia Luba, har da Maman Aliyu ma, yanzu yanzu."

Da ladabi Hayat ya amsa ya koma ɓangaren na Maman shi da ya fi kusa da shi. Aliyu da ya bishi da kallo saida ya ji kan shi ya sara, hankalin shi ya tashi sosai, zuciyat shi ta gagara fahimtar komai, rabuwa Abba da Ummu? Akan wane dalili? Me ya yi zafi haka da Abba ba zai yi haƙuri ba? Yana ganin wannan hukuncin yayi daidai kenan? Gaskiya bai ji daɗi ba ko kaɗan, kuma ba zai kasa faɗawa Abban nashi ba.

A ƙofar gida Khamis ya sauke su yace ma Kuwailat "Auta ki gaishe min da aunty, anjima zan dawo na ɗauke ku."

Kuwailat bata kula shi ba, dan ita bata ga dalilin da ya sa Maman ya kwana ba a gidan Baban ta ba, Aisha ce kawai ta masa godiya sosai kafin ta bi bayan Kuwailat su shiga. Tsakar gida suka samu Mama tana gyara abin da za su karya, har ƙasa Aisha ta duƙa saboda Mama zaune take suka dinga gaisawa da fara'a, kafin Mama ta dubi Kuwailat tace "Ke kuma lafiya kike ta jan idanu?"

Murmushi Aisha tayi tace "Ai kuka take ta yi wai Maman ta."

Da mamaki Mama ta nuna Kuwailay tace "A haka É—in ganÉ—anÉ—an dake? To Allah ya kyauta."

Murmushi Aisha ta sake yi tace "Ameen Mama, aunty Ummu É—in tana ciki? Nima ita na zo gani."

Kallon fuskar ta Mama tayi, cikar kamala da haiba yasa Mama faÉ—in "E tana ciki, ku wuce ciki, tana nan bacci take."

Har Aisha zata miƙe sai kuma ta dakata ta dubi Mama tace "Na san baku gane ni ba Mama, sunana Aisha, ƴar Alhaji Mukhtar Yaya ga uncle Fahad, jiya ai sun zo ni ban samu zuwa ba saboda ban ji daɗin jikina ba."

Da kulawa sosai Mama ta sake kallon ta tace "Allah sarki A'ishatu, ƙwarai kuwa hakane, ai ko Nabila ma dan ta tafi islamiyya da kun haɗe, nagode sosai, ku wuce ciki tana nan."

Da jin daɗi Aishata miƙe ta shiga, ɗakin da ta tabbatar nan Kuwailat ta shiga ita ma ta shiga dan tana jin kamar sautin kuka, tana shiga ko ta samu Kuwailat a ƙirjin Ummu da shigowar Kuwailat ɗin ta farka daga bacci saboda kwana da tayi tana sallah kan ubangiji ya kawo mata mafita cikin lamarin ta, dan haka ƙala ma bata ce ma Kuwailat ba saboda yadda ta faɗo mata a jiki tana kuka, daddaɓa bayan ta kawai take yi har Aisha ta shigo, a sakanni ƙalilan suka kalli juna, amma take irin ƙaunar nan da ake cewa *daga Allah* ta tsargu tsakanin su, ga kuma kowa da yake ganin kamannin wani a fuskokin junan su, Aisha na ganin kamannin Hajia da aka bata labari, Ummu kuma na ganin kamannin dattijon nan (Abbu Mukhtar) a fuskar matashiyar da duk ƙibar ta bata sa Ummu jin wannan ba zata gaza yin ƙanwa da ita ba.

Sallamar da Aisha tayi ta amsa a tausashe, kafin ta gyara zaman ta sannan ta daddaɓa Kuwailat tace "Kukan ya isa haka, yanzu je ki ban ɗaki zuba min ruwa nayi wanka."

A kunyace Kuwailat ta miƙe tana rufe fuska saboda kunya, sai Ummu da ta miƙe tana nuna ma Aisha gadon ta zauna duk da bata san ta ba amma tana jin tana da alaƙa da mutanen jiya, a tausashe tace" Bismillah zauna."

Da fara'a Aisha ta zauna tana murmushi da cewa" Nagode." Saida ta zauna Ummu ta sake duban ta tace" Muna lafiya?"

Kallon ta Aisha tayi tace" Ina kwana aunty Ummu. "
Chapter 110 · 0% Book details