← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 168

Sashe 26

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da lalaci da shashantar da abinda ta faɗa ɗin DG yace" To naji, amma ki sani idan har buƙatar maganar dake ta taso zan kira ki."

Cike da gadara da iko Fa'iza tace" Ni kuma sai na saka ka a baƙin jadawali... Ba iya a wayata kawai ba, har akan aikin nan, kasan kuma maza basu yi ƙaraci a duniyar da muke rayuwa ba, kuma abinda na tura maka ko a jikina bare ka yi tunanin ko zai bibiye ka su ne, dan na wuce wannan ajin."

Da sauri da kuma ladabi yace" Kiyi haƙuri ranki shi daɗe, ki yi haƙuri, sai kin kirani ɗin."

Tsaki tayi mai sauti tare da yanke kiran tana daddana wayar sannan ta koma zuwa ɗakin, tana zuwa ta samu an canza tsarin, yanzu Nuriyya za ta tafi tare da su, murmushi tayi wanda iya laɓɓa ya tsaya tana cewa" Haba dai ƴar uwa, ya zaki tafi tare da su kuma bayan duk gamu a gidan? Kinga ki zauna kawai sai mu tafi mu tare da Kabil ɗin, dan ni daga nan zan wuce karɓo cake ɗin da Kabil zai yanka anjima, Kinga ke sai ki kula mana da abinda yayi saura nan, duk da dai masu aikin da Abida ta ɗauko suna ƙoƙari, dan daga ƙasa na hangi yadda suka ƙawata wajen da kwalliya mai ban sha'awa."

Miƙewa Mukhtar yayi tare da jawo Nuriyya dake ƙiƙƙifta idanu jikin shi ya rumgumata yana mai kallon tsakiyar fuskar Fa'iza fuskar shi ba yabo ba fallasa yace" Babu abinda za ta yi a nan, kawai ta tafi tare da shi, idan ke ma zaki je ba damuwa, dukanku kuje, nima Kinga sai na rakaku ai."

Kai tsaye maganar Mukhtar ta nuna shi kanshi bai da nutsuwa da Fa'iza kuma bai yarda da ita ba, kamar yadda tun farko bai cika son shiga sabgar ta ba dan bata da sakin fuskar ma da mutum zai shiga lamuran nata, ba zai yarda yayi wasarere da rayuwar Kabil ba wanda shi kaɗai ne jika a gidan nan wanda ya fito daga tsatson namiji. Fa'iza da taji ba daɗi har zuciyar ta wani shaƙiyin murmushi tayi marar makama tana kallon shi ita ma tace "Haba mana Abbun Kabil, ni da Abida ai mun isheta komai, ba hidimar shagalin ƙarin shekara ba, ai ina ga ko aure Kabil zaiyi mun isa mu tsaya mata, ko ba haka ba Mamie?"

Ta faÉ—i hakan tare da maida duban ta inda Hajia take, maganar ta gaskiya ce, musamman ma su suna da kara akan lamura irin waÉ—annan, hakan yasa Hajia jinjina kai tace" Hakane, Mukhtar, ka bar su su tafi, mu sai muyi wani abun a gidan."

Kallon Hajiar yayi da ladabi sosai da kuma tausasa murya yace" Kuyi haƙuri Ammie, hankalina zai fi kwanciya idan muka tafi tare da shi, Ammie yara biyu na rasa a dalilin yarda da mutane, ba zan yarda na sake rasa Kabil ba da irin wannan yardar."

Kaf maganar yayi ne yana kallon cikin madubin idanun Fa'iza, da fari ta shiga wani yanayi na me yake nufi? Amma da ya dire kalaman sai ta gane ina ya dosa, sai kawai ta bishi da wani makirin murmushi har da ɗan ɗaga masa gira tayi sake yin murmushin gefen laɓɓa tana kallon nashi idanun ita ma tace "Shikenan, tunda haka kace, za mu gani."

Da kallon tsana da jin haushi ya bita, wallahi ba dan matar Yayan sa bace da sai ya kauÉ—eta da tafi, shi kam da É—an uwa na sakin matar É—an uwan sa a kowane irin hali, Allah da sai ya sake ta saki dubu uku ma kuwa rasss zai yanka mata.

Haka dai Abida da Nuriyya na rumgume da Kabil suka tafi suka dawo aka ci gaba da shirye shirye. Ƙwarai Abida ta sake shiga ransu da irin wannan bajinta da tayi, masu shirya wurin taro ta ɗauko musamman suka kula da komai ta biya su, hatta cake ɗin da ta bayar oda daga wani garin aka kawo shi sak mai suffa da girman Kabil ɗin wanda hakan ya birge mutane ƙwarai tare da ban ƙawa har aka dinga magana akan haka.

Lokacin da maƙiya suka ruɗe shine sa'ilin ba wa Kabil kyaututtuka, duk mai mugu da ƙudirin nufi ya so bayyana sai dai kawai ka ƙara ɓoye shi dan kar ka fallasa kan ka, hasalima irin kyautar da Saheeb Ahlan ya ma Kabil ko ƴaƴan da ya haifa zai iya gayyato hassadar su da kuma baƙin cikin su akan yaron, bare kuma waɗanda suke ganin su basu da wanda za'a ma wannan kyautar su ji daɗi.

Kyautar hannun jarin shi ya ma Kabil da ya saka a wani kamfani dake Austriya, kamfanin da a yanzu suke ta jin raɗeraɗin nema yake ya zama nashi dan dama yanzu hannun jarin nashi ya fi yawa dan kaso sittin da biyar gare shi a cikin ɗari, haka kuma daga wata majiya mai ƙarfi suna kyautata zaton ya kusa siye kamfanin saboda matsalar da ta faɗawa mai ɗaya hannun jarin, ba maganar milyoyi bane, bilyoyin kuɗi ke shigo masa ta wannan kamfanin, shine kacokam ya mallaka shiyar ga Kabil ɗan shekara huɗu a duniya.

*Gagara* jura Fa'iza tayi sa'ilin da Ammie ta ba wa Kabil kyautar wani sit na kayan wasan da daga ƙasar waje ma sit ɗin ya haura miliyan biyu, dan ko jirgin wasar kamar na gaske yake dan har da matuƙin jirgi ke akwai a ciki sai dai ƙarami ne. Tana shiga ɗakin ta ta rufe cilli tayi da wayar ta kan kujera ta shiga sauke wasu numfarfashi saboda yadda zuciyar ta ke tafasa, irin zafi da ƙunar da take mata yasa ta zuwa ta ɗauko ruwa masu sanyi ta buɗe robar ta kifa kai, ba ruwa take buƙata ba, hakan yasa har ta ƙware ruwan suka zubar mata a jiki, cikin ɓacin rai da tafasar zuci shi ma goran ruwan ta yi jifa d shi kawai ta durƙushe a wurin nan ta fashe da wani irin kuka mai tsanani wanda daga zuciyar ta ne... Abubuwa ne suka taru suka mata yawa, ga rugujewar tsarinta wanda da ta samu kuɗin nan tabbas ita ma da ta fara hango kanta matsyin wacce wata rana za'a ma ɗanta irin kyautar nan, ga kuma wannan kyaututtuka da ta kalla ana ma Kabil, ko mijinta fa tana kallo y bashi babban kwalin da bata san me ye à ciki ba, amma tafi tunanin na'ura ce dan Kabil ɗin na yawan ce masa yaushe zai siyo mishi? Tun d y sme shi wata rana yana aiki da ita shi ma har ya daddana.

Ta jima tana kuka ita kaɗai kafin ta wanke fuskar ta ta duba madubi ta gyara fuskar ta da kyau sannan ta ɗauko wayar ta ta sake fitowa, tun daga nesa take hango mutane na tafiya, a haka kuma ta hango Fahad na shirin fita hannun shi riƙe da waya yana amsawa da kuma wata farar takarda mai kau an yanka masa cake ɗin sa a ciki yana ci, daga nesa take iya gane Hajia dake masa magna akan fitar da zai yi ne da kuma kashedin cika dare dan abinda kullum sai an yi ne kamar dai karatu. Take sheɗan ya raya mata tunda à yanzu dai Kabil ya mata nisa bata samu damar cika ƙudirin ta ba, to ai ga Fahad, tasa duk lalacewar sa ba zasu kasa biyan diyyar da zasu yanka musu ba. Wani murmushi ne ya suɓuce mata da ya saka haƙoran makkar ta sun bayyana a fili, babbar wayar ta mai tsadar gaske ta ɗaga ta shiga daddanawa, jim kaɗan aka ɗaga cike da girmamawa aka gaishe ta, ba tare da ta kawar da idanun ta daga Fahad ba tace "Tsarin...da kuma abun farautar duk sun canza, ka tabbatar kana kan manhajar Maps, zan turo maka da lambar abun farautar mu yanzun nan."

Amsa ɗaya kawai aka bata ita ce "Angama Hajia." Daga haka ba tace komai ba sai yanke wayar da nufa wajen taron, ganin Fahad na shirin ɓacewa ganinta ya fit a gidan a ƙafa yasa ta yin saurin ƙwalla masa kira, dakatawa yayi yana kallon ta har ta ƙaraso, da fara'a a fuskar ta tace "Fahad, dan Allah ka taimaka in baka wani saƙo mana?"

A wani ciccije yace "Na me?" da fara'a tace "Ka ga akwai wani mai ne da nake anfani da shi na hannaye, to gashi ya ƙare, shine nake so na baka a siyo min dan Allah."

Fuskar shi ba fara'a yace da ita "Kawo to, dan sauri nake gaskiya."

Murmushi tayi tare da ciro kuɗi a rigar wayar ta ta miƙa mishi, kallon ta yayi bayan ya karɓa yace "Duka wannan?"

Jinjina kai tayi, juyawa yayi ya fita yana mamakin yanzu almubazzarancin matan gidan nan ya kai su dinga siyan man shafawa a hannu na wannan kuÉ—in? Murmushi tayi har ya fita a gidan sannan ta juyo tare da tura lambar Fahad É—in ga wanda za su mata aikin nan, daga haka kuma ta shiga harkokin ta cike da tsammanin jiran sakamakon aikin nata.

*02:14* ta leƙa ɗakin nashi kamar yadda ta saba a kowane dare ta kan tabbatar ya shigo gidan kafin ta kwanta, duk da ta sha yi masa faɗa a kan cika daren nan, amma Sam Fahad baya jin magana gashi kullum lamarin shi ƙaruwa yake, Alhaji dai kuma ya zuba masa idanu ne kawai bai cika yi mishi magana ba. Saɓanin kullum wayam ta samu ɗakin ba Fahad ba labarin shi, tun a lokacin hankalin ta ya tashi ta kuma yi kwanan zaune dan duk rashin jin shi in dai ka ga bai kwana gidan nan ba to tabbas baya garin, abinda ya saka ta damuwa kuma shine jiya har fiye da 11 na dare yana gidan nan dan har aka gama shagalin nan.
Chapter 26 · 0% Book details