← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 168

Sashe 143

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassan ya kalla dake kusa da shi lokacin har liman ya shigo yana haramar tayar da sallah yace "Hassan, da mun idar da sallah fa zan kama hanyar komawa, na tuna wani muhimmin abu a gida."

Da mamaki Hassan ya kalle shi yace "Gida kuma? Karatun shi? Haka kwatsam? Lafiya?"

Kallon shi Jabir yayi, sai dai kafin ya bashi amsa sai kawai ya ƙyale shi saboda kabbarar harama da aka fara yi, haka Hassan ya ƙyale shi har suka idar da sallah, ba yadda ya iya haka ya mishi addu'ar sauka lafiya bayan ya ɗauki jakar shi da kayan da ko warware su bai yi ba, haka ya sake kama hanya a fujajen kamar dai yadda ya taho ɗin nan, saida ya kama hanya sannan ya kunna wayar shi da ya ji shakkar kunnawa dan yasan zai samu kira da dama.

*Alhamdulillah.*

[02/09 à 16:19] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*66*

Kiran Abban shi (mahaifin shi) da ya fi yawa shi yafi ɗaga masa hankali, gashi wai har da kiran Mama uwar marayu da Hajia da aunty Mardiyya, sai suka ma bashi dariya, wai su yanzu duk sun yarda su aura masa maama ne? Saboda Allah wannan wace irin fitina ce suke neman haɗawa? Ko da yake yayi alƙawarin ba zai sake jin auren nan a matsayin wata masifa ko mummunar *RUBUTACCIYA* ba, tunda ubangiji ma ya bashi alamar dake nuna yana bayan wannan haɗi. *Tunda* saƙo ya shiga wayoyin su na Jabir ya dawo kan sadarwa har suke riga-rigan kiran shi saboda lokacin kowa ya tashi sallah, kiran Hajia ne ya fara shigowa wayar shi, yana ɗagawa tun suna gaisawa ya ji wayar na ɗin-ɗin-ɗin, yana dubawa ya ga kiran Aliyu ne, bai mayar da wayar kunnen shi ba saida ya ga kiran Abban shi.

Sauraren Hajia ya fara yi da tace "Dattijo, ya zaka min haka kuma? Bayan ina ta faɗa da ƙarfi cewa kai ɗin mutumin kirki ne har da ƙari, wanda ba zai bamu kunya ba dan mun bashi zaɓin mu."

A nutse Jabir da ke tuƙi a hankali ya lumshe idanun shi, cikin wannan muryar tashi mai kama da fuskar shi yace" Ta ya kuka ga haka ya dace? Hajia Maama fa matar Abba.."

Da sauri ta katse shi da cewa" Tsohuwar matar Abban ka dai, dattijo kada ka bari wannan aikin ladan ya wuce ka mana, na sani ba zaka kamo ƙafar Abban ka Kabir wajen dattako ba, dan gaskiya ko ni da nafi kowa farin cikin abinda ya aikata, ina tausaya masa da kuma jinjinawa nagartarsa, sai dai ba na so kuma ka bari Jibril ya fi ka nagarta a wajen kowa, dan iyayen Ummu sun tabbatar idan baka amince ba to zasu ba wa Jibril ita, abinda yayi a baya na neman mata kuma zasu ɗauke shi a matsayin ajizanci ne."

Cije leɓen shi yayi yana ƙara damƙe sitiyari sosai, saida ya ji zafi a leɓen nashi sannan ya saki da sauri yana faɗin" Hajia ba za'a daina kawo maganar *ɗan nan* bane? Bai dace da Maama ba."

Da sauri Hajia dake murmushi tace" Dan haka sai ka aure maaman ka, ko kuma kana kallo a bata wanda bai dace ba."

Shiru yayi kawai yana sauraren ta, ita ma shiru tayi saida ta ji ba dai zai ce mata komai ba sannan ta numfasa tace" Jabir, kai fa kake faɗa min kana so ka sakawa Abban ka Kabir da abinda ya maka a rayuwa ta hanyar kyatatawa da riƙo da iyalin shi tamkar naka, ka faɗa min indai kna raye ba zaka taɓa bari shi ko ahalinshi wani ya zubar da hawaye ba, sannan ka faɗa min kana so ka taya shi kare mutumci da martabar iyalin shi, ka manta ne? Ka faɗa min duk waɗannan maganganun? Yanzu Jabir lokaci yayi da zaka saka masa, sai ka bijire ka watsa masa ƙasa a idanu? Jabir, Ummu tsohuwar iyalin sa ce, ya fi ka sanin dalilin da ya sa ya ce ka aure ta, idan ba kai ba wani ne zai yi, shin Jabir ba zaka taya shi kare wannan martabar da kayi ikrari ba? Ka fi so Ummu ta auri wani wanda daga mu har ita bamu san manufar sa ta son auren nata ba? Idan wani abu ya faru marar kyau da ita ba ka ganin kaima kana da kamasho a ciki? Tunda har an maka tayin auren ta amma ka ƙi, kayi tunani Jabir, ni a ganina kamar hakan ma wata hanya ce da zata saka ka ci gaba da tsare mutumcin iyalin shi, sannan ni a ganina duk da Alhaji Kabir dama mai taimako ne, amma ya sake samun azamar taimaka maka ne har ka kwana gidan shi na wasu kwanaki kafin tafiyar ka karatu saboda Ummu ta bashi labarin ka kuma ta san ka, da bata san ka ba wataƙila baka samu kulawa da gatan da ka samu a wajen shi ba, kasan mutane dubbani nawa ya taimaka a rayuwar sa? Ka san da yanzu wasu ma bai san da zaman su ba? Amma me yasa kai kaɗai kayi zarra a cikin su? Saboda kawai jinin ku ya haɗu ne? A'a Jabir, shi fa komai da ka gani a rayuwar nan wallahi akwai dalilin da yasa yake faruwa, abu zai iya faruwa shekara ɗaya baya, amma sai bayan wannan shekara ɗarin wani sanadi zai faru da za'a gano dalilin da ya faru a waccen lokacin, ni a tunanina haka tunanin Alhaji Kabir ma, kamar dan wannan ranar ne waɗancen abubuwan suka dinga faruwa da suka fito da kai daga gidan Abban ka."

Numfashi Hajia ta sauke sannan tace" Zan aje waya, na ji ana ta kiran ka."

Ba ta jira me ya ce ba ta yanke kiran, Jabir da duk ta ƙara saka jikin shi yin laushi ya fara saddaƙo ma duniya ya kuma fara jin yarda lallai fa kamar hakane, yana kallon kiran Aliyu amma ya kasa ɗagawa saboda tunanin da yake yi, ganin kiran ya tsinke sai ya aje wayar a mazaunin ta, take kuma kiran Abban shi ya shigo, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga ya sa wayar a amsakuwa.

Muryar nan ce ta daki kunnuwan shi ta Baban shi wanda ya É—auki shekaru bai ji ta ba, wato muryar ingarman sojan nan cikin wannan zafin da ya raine shi da shi yna masa tsawar da duk da a zaune yake saida ya ji kamar zai sunkuya, cikin wani irin hargagi ne yace "Jabir dan ubanka kana ina?"

Zaro idanu Jabir yayi ya taka birki saboda girman abun, yaushe rabon da a zage shi shi kam? Yanzu akan wannan abun ne ake zagin malami? Take yaji tsoron mahaifin nashi ya baibaye shi kamar dai yadda suke a shekarun baya, muryar shi na É—an rawa rawa na son kuka da yake yi saboda wani sabon kaÉ—aici da kewar mahaifiya da yaji ya É—arsun masa take a wurin yace "Abba.. in...a hany...a ne.."

Cikin wata sabuwar tsawar yace "Hanyar gidan uban wa?"

Lumshe idanu Jabir yayi ya ɗan lashe leɓen shi sannan ya furta "Hanyar Kano...Abba, amma ina dawowa yanzu."

A hassale Abban yace "To maza ka dawo min gidan nan Jabir ina neman ka, sannan tun a hanya ka kira waɗanda kasan ya dace su halarci ɗaurin auren ka ka sanar da su da ƙarfe 09:00 na safiyar gobe malam Adam zai ɗaura auren ka da Ummu, ka fahimta?"

Bai buÉ—a idanun shi ba ya haÉ—e wasu yawu masu zafi zafi sannan ya amsa da" E... Abba..."

Ƙit! Abban yayi saurin yanke kiran saboda jin muryar Jabir na neman saka shi kuka. Jabir kuma haɗa kan shi yayi da sitiyari ya na hawaye, ba wai na auren da za'a masa ba, sai na yadda aka kasa samun mutum ko ɗaya ne da zai nuna ya fahimce shi sannan ya goyi bayan shi, ko da dqga baya zai nuna yana tare da sauran mutanen ne. Lallai rashin *mahaifiya* wani tabo ne babba a gurin mutum, yana da yaƙinin da tana raye wataƙila ita ta fahimce shi, idan kuma tana tare da su ne ita ma da zata rarrashe shi ne da maganganu masu daɗi, wataƙila ma har ta dinga shafa kan shi dake kan cinyar ta.
Chapter 143 · 0% Book details