← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 168

Sashe 80

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*38*

*Tun da* sanyin safiya tana ɗain baccin ta ko madafa ba ta shiga ba, hasalima yau niyyar ta shine kawai Kuwailat ta sha ko da cascroot ne ko cornflakes ta tafi makaranta, sam ba ta da karsashin yin girkin yau ma, dan haka ta tashi ba walwala, bugun ƙofar da ake yi ne yasa ta ƙwala kiran sunan Kuwailat, daga ɗakin ta ta amsa da "Na'am Mamie."

A kasalance tace "Ki duba ki ga wa ye a ƙofa."

"To Mamie." Ta amsa tana É—aukar kallabin ta ta É—aura a kai sannan ta fito, tana buÉ—ewa tayi tozali da Aliyu da Jabir, shigowar su kenan daga masallaci tun asuba suke ta zagayen gaishe da iyayen gidan, murmushi ta sakar musu tare da kauce musu a hanya tace "Yaya, ina kwanan ku ? Ku shigo ciki, Mamie tana É—aki."

Aliyu ne ya fara shigo yana sake yin sallama, sai kuma Jabir da ya biyo bayan shi, ƙamshin Turare ne ya musu maraba, kuma abun burgewa da mamaki shine yau ba ta samu tayi Turare ko ɗaya a ɗakin ba, ba ma haka ba, tun jiya da safe da ta yi ba ta sake saka wani turaren ba, amma ya kama ɗakin saboda tana yawan anfani da shi kuma turaren mai kyau da inganci, sannan kujeru ma da labulayen ta duk tana da turare na musamman da take fesa musu, hakan yasa ƙamshin su ma ya ishi kwantar da hankalin bawa, ta ƙofar ɗakin Ummu kawai za ka wuce amma sai ka ji ƙamshi a gurin, na daga cikin dalilin da yasa indai za ta ce ma Alhaji ya bata kuɗi za ta sa a kawo mata turare yke bata jikin shi na rawa tare da ƙarfafa mata guiwar a ci gaba da saka ƙamshi.

Aliyu dake ma Kuwailat ne murmushi dafa kanta yayi yace "Auta, ki faÉ—awa aunty mun zo gaishe ta ne."

Da sauri ta juya tana faÉ—in "To Yaya."

Tana shiga ɗakin Aliyu ya ɗaga kai yana kallon ɓangaren yana faɗin "Ka ga wurin nan kamar ba iri ɗaya da na su Mama da Hajia ba, sai naji kamar nayi bacci wallahi saboda ƙamshi."

Wani kallo Jabir ya watsa mishi kawai ya É—auke kai bai ce uffan ba, hakan ya sa Aliyu yin murmushi yace "Alaramma ka dinga yin magana mana, wannan shirun naka yayi yawa."

Nan ma shirun ya mishi bai ce komai ba sai maida hannayen shi biyu da yayi baya ya ɗan juya yana kallon ƙofar shigowa, ba jimawa Kuwailat ta fito tare da nufa ɗakin ta saboda Maman nata na bayan ta, a nutse Ummu ta fito da hijabin ta fari tas mai hannaye da ƴar fara'a a fuskar ta.

Ƙarasowa tayi tana faɗin "Assalama alaikunna."

Murmushi Aliyu yayi ya amsa da "Wa'alaiki salam, auntynmu barka da safiya?"

Yadda yayi maganar har da rusunawa É—in nan ya saka ta jin kunya ta amsa da "Barka babban Yayan su, antashi lafiya?"

Kafin ya bata amsa Jabir ma ya juyo, saida yayi irin ranƙwafawar nan kamar zai yi ruku'u kamar kuma zai yi tsugunnon maza cikin taushin murya ba tare da ya kalli fuskar ta ba yace "Barka da safiya Maama?"

Da murmushi shima ta amsa mishi da "Barka Jabir, antashi lafiya? Ya gajiya kuma?"

A tare suka amsa da "Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya."

Da farin cikin girmamawa dar ta samu daga gare su tace "Ma sha Allah, nagode sosai da kulawa, Allah ya saka da alkairi."

Murmushi duk sukayi sai Aliyu da ya nufi wajen teburin cin abinci da ya ga an masa kwalliya da kwanukan abinci masu irin ƙyallin nan da babbar flask da sauran kayan da dama kawai ana kwalliya da su ne, kasancewar shi mutum mai saurin sabo da barkwanci da son zama da kowa lafiya yasa yake faɗin "Auntynmu Allah sa zamu samu abinci? Kinsan bana son *zakina* ya fara jin yunwa ban tanadar masa komai ba, matsala ake samu da haka."

Dariya Ummu tayi ta saci kallon Jabir da ya sunkuyar da kai ƙasa yana girgiza kai shima, cikin taushin murya Ummu ta kalli Aliyu tace" Babu abinci gaskiya, sai dai za'a iya haɗa muku idan kuna buƙatar hakan?"

Dakatawa yayi daga shirin isa teburin ya juyo yace" Gaskiya zamu so haka, dan Mama ta ce wai masu aiki ke haÉ—a mata abun kari, shi kuma oga ko a can baya cin abinci ko ina."

Juyawa Jabir yayi ya kalle shi, da idanun shi ya mishi alamar zamu haɗu, daga haka ya kalli Ummu cikin nutsuwa da ladabi da burin son samun albarka daga bakin duk wanda yake gaba da shi, musamman ma su da yake musu kallon iyaye ya ƙara rusunawa yace" Maama, zan wuce ni, muna buƙatar addu'arku?"

ÆŠan jim tayi ta kalle shi da mamakin ita kuma? Sai kuma tayi murmushi ganin har lokacin bai É—ago daga rusunawar da yayi ba tace" Addu'ar mu ta alkairi kullum tana tare da ku Jabir, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah kuma ya sa kuyi anfani da abinda kuka karanta, Allah kuma ya baku zuri'a ta gari."

Da jin daɗi matuƙa ya amsa da" Ameen ya Hayyu ya Qayyum Maama, Allah ƙara lafiya."

Aliyu kuma da tsokana ya saci kallon Jabir yace" Me yasa ban ji kayi ƙorafin ba'a maka Addu'ar yin aure a kwanan nan ba? Naga abinda kake so kenan."

Jallon shi Jabir ya yi, sai kawai ya juya ya fice bai sake juyowa ba, Aliyu kuma da murmushi dan yasan sai ya fito zasu yi rigimar, dan gaskiya yana al'ajabin yadda Jabir ke girmama Ummu, wani irin maɗaukakin girma ne yake bata kamar na ɗa da uwar da suka rayu tare amma bisa koyarwa irin ta addini, kunyar ta yake, girmama ta yake, nauyin ta yake ji, ganin ƙimar ta yake yadda ko fuskar ta shi yasan ba zai iya kalla ba. Shima shirin ficewa yayi Ummu na tambayar "To me za'a haɗa?"

Da fara'a yace "Ko me ma muka samu auntyn mu Alhamdulillah." Jinjina kai tayi alamar shikenan, saida suka fita ta cire hijabin ta aje kan kujera ta shiga madafa tana faÉ—awa Kuwailat dake É—aki ta same ta can kafin ta wuce.

Tsakiyar shukoki suka samu Alhaji zaune kan kujera yana jin daÉ—in yanayin sosai, suna isowa duk suke zaune suna sake gaisawa duk da sun haÉ—u masallaci, saida suka gaisa ya nunawa Aliyu kujerun dake wajen mai gadi yace "ÆŠauko ku zo ku zauna na ji."

Bin umarnin shi Aliyu yayi, jim kaÉ—an ya dawo da kujerun ya aje suka zauna shi da Jabir, sake kallon su yayi yace "To ina sauraren ku, kun ce akwai maganar da zamuyi idan kuka dawo?"

Jabir ne ya fara kallon shi yace "Abba ba yanzu ba, ka bari har jikin ka ya ƙara yin kyau."

Murmushi Abban yayi ya dafa kafaÉ—ar shi yace "Karka damu Jabir, burina yanzu shine naga ku manyan Æ´aÆ´an nawa kun hau kan turbar da ta dace, Alhamdulillah kun samu ilimin addinin da nasan ko iya shi kawai ya isheku rayuwa mai nagarta, amma bayan haka ina so na ji abinda kuke son faÉ—a min da wuri wuri, dan naga ko da taimakon da zan iya muku?"

Kallon juna sukayi shi da Aliyu, da idanu suka gama yanke shawarar kawai su sanar da shi É—in tunda ya matsa, Aliyu ne ya kalli Abban a ladabce yace" Abba, ba wani abu bane dama, kamar yadda kuka sani ina son yin koyarwa, to shine nake so ku tsaya min dan ina son buÉ—a islamiyya, zan tafiyar da ita ne akan wani tsari da na gani a Madina, sai shi kuma Jabir, kun san dama shi dai É—an kasuwa ne, kuma har tafiyar can ma bai daina aikin wahala ba dan ya samu kuÉ—i, to Alhamdulillah ya tara kuÉ—in kam..."

Aliyu yayi maganar yana dariya saboda hararan da Jabir ya watso mishi, dariya Alhaji ma yayi yana ci gaba da sauraren Aliyu da ya ci gaba da faɗin" Ya nemi kuɗi sosai Abba, yayi aikin wahala ya wa larabawa bauta duk dan ya tsaya da ƙafafun shi, da taimakon Allah kuma ya fara siyan kaya a can yana turowa wani abokin mu anan, to Alhamdulillah zan iya cewa ya zama babban gwaska ta nan wajen, dan yanzu haka a Saudia da Madina da Lebanon akwai wasu da yayi sabo da su kuma yake siyan kayan nan namu na gida yana raba musu suna bashi kuɗin, Abba, a taƙaice dai Jabir ya tsayu sosai."

Gyara zama Aliyu yayi yace" Abinda yasa na faɗa muku haka Abba, yana son buɗa babban shagon da zai zama a cikin yake ɗaukan kayan da yake rabawa, to shine yake son ka saka masa hannu, dan yana son shagon ya kasance a idanun jama'a ne, sai taimako na gaba kuma da yake buƙata Abba... Conteneur ɗin ka dake yawan tasowa daga Dubai da Chine, yana so idan ana muku lodi ya dinga bada nashi saƙon, idan abubuwa suka yi kyau wata rana shima sai mu rasa wurin zama tsabar yawan conteneur ɗin da ya kawo a garin nan."
Chapter 80 · 0% Book details