← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 168

Sashe 103

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma tsaf Alhaji ya haɗiye harshen shi ya ƙi ko da kallon inda take bare ya amsa mata, sadda kan ta tayi tsbar kunya dan bata yi tunanin zai iya share ta gaban su su, ta ɗauka kamar yadda ba ya son Kuwailat ta san komai haka suma zai kiyaye, kukan da ya taho mata tayi saurin tarewa da tafin hannu. Aliyu da ya ga komai kallon Jabir ya yi dake satar kallon idanun Ummu da ya ga sun cika taf da hawaye, yana kallo har ƙwallan nan suka faɗo kan hijabin ta, saida ya ɗan rintse idanu saboda yadda ya ji wani irin duka a zuciya shi, da sauri ya kawar da kan shi yana dantse leɓe, ƙarfi da ya ji nutsuwar sa so take ta bar shi bayan san me yasa ba. Aliyu kuma da abun ya dame shi ta wata siga daban kallon Ummu yayi dake tsaye yace "Auntyn mu, lafiya dai ko?"

Ɗaga kan ta tayi ta kalle shi, a hankali hawayen nan suka fara sulalowa kan kumcin ta, da sauri ta sa tafin hannu ta share tana ƙaƙaro murmushi tace "Ba komai, lafiya lau wallahi."

*"Ba gaskiya bane Maama, kuka fa kike."* Cewar Jabir da ya tsare fuskar ta da idanu, É—aga nata idanun tayi ta kalli inda yake, da sauri ta kawar da duban ta dan ita wallahi Jabir da ta kalle shi ranar nan take tunawa sai taji jikin na wani irin yam yam haka ba daÉ—i dai, shiru É—akin ya É—auka ba wanda ya sake cewa komai, sai daga bisani Aliyu ya sake duban ta yace "Aunty, dama Jabir yau zai tafi Agadez gaishe da kakanin shi, yana so ya miki salama."

Ba tare da ta kalli inda Jabir É—in yake ba tace "Ahan! Allah ya tsare, Allah kiyaye hanya."

Sai kuma ta É—an yatsina fuska tace "Zan shiga ciki nayi wanka, dake ina so zan tafi gida, masu neman auren Nabila ne za su zo yau in sha Allah."

Da farin ciki Aliyu ya mata Allah ya sa alkairi, amma Jabir hankalin shi na kan mecece matsalar ta? Shi fa damuwar nan baya son ta gaskiya, har ta juya ta shige Aliyu ma ya miƙe zai fita Jabir na tsaye yana kallon ƙasa.

********************

Wani shaƙiyin murmushi Sa'ad ya kuma saki saboda ganin da gaske Mama ta ɓallo magani za ta ba wa Aisha dan amai ya tsaya, marairaicewa da tayi ta kalle shi tace "Babana, ka mata magana tasha magani kaji? Aman ne ni bana so wallahi, galabaitar da mutum yake lokaci ɗaya."

Murmushi ya sake yi yace "Mama, da kin gaya min zaki siyo mata magani da ban bari kin siyo ba, kamar dai kin manta wacece Aisha, allura ma sai anyi sa'a take karɓan jikin ta, ai yadda kika san jikin ta yayi expire haka take."

Aisha dake durƙushe ta gama kelaya amai ta ɗaga kai ta kalle shi, turo baki tayi sannan ta sake sadda kan ta ita dai ba ta ce komai ba, ɗauke kai yayi daga gare ta yana faɗin" Bani na kar zomon ba, ciki ne naje nayi kuma."

Da azama Mama ta kai masa duka a baki ya goce yana dariya, harara ta wanka masa tana cewa" Marar kunya fitsararre, ɓace min da gani malam."

Matsowa yayi kusan su yana faÉ—in" Mama, bari kiga haÉ—in da nake mata take samun lafiya."

Yayi maganar yana shiga falon su, jim kaɗan ya fito da kofi a hannun shi, garin hulba ne da ya tafasa a ruwa ya ta ce ya miƙo mata yace" Gashi ki sha?"

Karɓa tayi ba gardama ta yi bismillah ta kifa kan ta, jim kaɗan ko ta shanye ta aje kofin, kama hannun ta yayi a hankali suna takawa har suka shige ɗaki ya zaunar da ita, shima kusan ta ya zauna ya ɗauki kwalban man hulba ya cika cokali ƙarami ya bata shima ta shanye, duban ta yayi yace "Kwanta sai na shafa miki zabada (jibda)."

Kwance tayi kan kujerar ya ɗauki jibda ya shafe mata jiki da ita sannan ya rufa mata zane, cike da tausayawa yake kallon fuskar ta yana shafa kwantaccen gashin ta baƙi siɗik, inda Maa ke kallon su tana faɗin "Ikon Allah, a ce mutum ba shi ba maganin bature, ai ko kin raba kan ki."

Murmushi Sa'ad yayi yace "Mama paracetamol idan kwali za ta sha ba zai mata maganin zazzabi ba kona minti ɗaya, amma yanzu Kinga nan? In sha Allah zuwa azahar ta fara dawowa hayyacin ta tana addabata da ƙiriniya."

Duk da ita kaÉ—ai tasan me take ji, hakan bai hana ta É—an ture shi daga kusan ta ba tace" Abbu ka daina."

Murmushi yayi ya ci gaba da shafa kan ta yace" To na daina Æ´ar Abbu."

A hankali ta fara lumshe idanun ta, maganar da yayi take tunani akan ta, ba wai hulba da su man zeitun da alayyadi na mata aiki kai tsaye bane, ƙwarai sun fi karɓan jikin ta, amma kuma shine warakar ciwon ta, kulawar da yake bata idan aka ce kan ta kawai na ciwo, yadda yake ɓarin jiki da kai da kawo duk dan ta samu lafiya, hakan ke matuƙar ɗaɗata ga ƙasa, shiyasa ko bata jin daɗin wasu lokuta take daurewa saboda shima shiga tashin hankali yake.

Har bacci ya fara É—aukar ta taji yana faÉ—awa Mama "Mama, ki zauna da ita nan zan je na dubo Abban ta da suka shigo É—azu, da tare zamu tafi kuma gashi ita bata jin daÉ—i."

Da farin ciki Mama tace "Dan Allah? Ziyara suka zo mana kenan? Shine ba ka faÉ—a ba?"

Murmushi yayi yace "A'a Mama, neman aure ne suka zo, zan je mu gaisa da su saina dawo."

Da sauri Aisha ta buɗa idanu ta kalle shi tace "Abbu, nima zan je, mu tafi tare dan Allah na ga Mamie, wallahi jikina yayi sauƙi sosai."

Girgiza mata kai yayi yana miƙewa taye yace "A'a ƴar Abbu, gaskiya ba zaki à wannan halin da kike ciki ba."

Da sauri ta tashi zaune da zumuÉ—i tace "Wallahi Abbuna na warke, ka gani? Zan iya tafiya ma f.."

Katse ta yayi da "A'a Eesha, ba zaki je ba gaskiya, salon ki sa Maman mu tayi ta min kallon tuhumar me na miki ko? Gaskiya a'a."

Marairacewa tayi tace" Allah ba zan yi koma da zata gane ba."

Kallon Mama yayi yace" Mama, dan Allah ki zauna ba zan jima ba nima."

Kallon Aisha yayi da ta fara haÉ—e fuska yace" Ina abincin tarban su da kika girka?"

Haɗe hannaye tayi a ƙirji ta turo baki ba ta ce mishi komai ba, hakan yasa ya sake gyara tsayuwa yana kallon ta, abinda yake so kenan dama suyi dan su rabu ana hushi, dan haka da irin gadarar nan yace" Ba dake nake ba kika min shiru? Ka ji min lukutar yarinyar nan, nace ina abincin yake."

A ɗan hassale ta kalle shi tace" Ban sani ba mana Sa'adu, ka duba ai gidan ba baƙon ka bane."

Jinjina kai yayi tare da nuna ta da yatsa yace" OK, shikenan to, idan kuma na duba ban gani ba ina zuwa zan rufe ki da duka, da kika raina mutane."

Da kallo Mama ta bishi tace" Ba zaka kuskura ka taɓa min ƴa ba Sa'ad, an je an faɗa din kuma."

Suna nan ya fito da manyan kwado har biyu ya nufi hanyar fita ko kallon Aisha bai yi ba wacce ya hanga ta gefen idanu sai kumbura take ita ya ƙi tafiya da ita.

********************

Dake ta ji bai sa makulli a ƙofar ba, su Aliyu na fita ta buɗa ƙofar ta faɗa ɗakin shi, zaune ta same shi bakin gado ya dafe kan shi, saida ta ji ba daɗi sosai saboda kar dai a zo bai da lafiya, ga kuma wannan damuwa da ya saka wa ran shi da tasa ko kallon ta ya daina.

A hankali ta ƙarasa ta zauna kusa da shi, cikin sanyayyar murya tana kallon shi tace "Abban Kuwailat, dan Allah ka daina damuwa da abinda na aikata, na yarda na aikata maka kuskure, kayi haƙuri ba zan sake maimaita kamar sa, na rasa sukuni tunda ka juya min baya a gidan nan, gaba ɗaya ni da Kuwailat mun zama kamar wasu marayu, dan Allah kayi haƙuri ka ji."

Ba tare da ya ɗauke hannun shi daya dafe kan shi ba cikin wata sarƙaƙƙiyar murya yace" Na kasa yarda ke kika aikata haka Ummu, kamar dai dama jirana kike yi? Ummu me kike nema daga gare ni? Me kika ce min kina so ban yi miki shi ba? Wace soyayya ce bana yi miki ke da ƴar ki, hatta matata ta farko Ummu bana jin ta a zuciya kamar yadda ke da kika shigo gidan nan jiya nake jin ki, amma ki rasa dame zaki saka min sai wannan?"

Fashewa tayi da kuka saboda zuciyar ta sai harbawa take da sauri, maganganun shi sun mata kama da na wanda yake ƙullace da ita, wataƙila hannun da suka haɗa da Jabir ya sa yake jin haushin ta haka? Dan ta san Alhaji Sagir ai zai gaya masa duk dan a sama mata mafita. Hakan yasa Ummu tunanin wannan ɓacin ran ne ke damun shi, sai kuwa ta sauka daga kan gadon ta durƙusa gaban shi cikin kuka tana faɗin "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi tallahi Abban Kuwailat ban yarda shaiɗan yayi galaba a kai na ba tsakanina da Jabir, yana riƙe hann..."

Da wani irin mugun yanayi ya É—aga kan shi ya kalle ta, mamaki ne fal a fuskar shi da kuma kamar firgici haka, dole Ummu tayi shiru saboda kallon da yake mata da babu rahama a cikin shi, cikin É—aga murya a tsawace yace" Ban gane tsakanin ki da Jabir ba? Me ya faru tsakanin ki da Jabir É—in? Ummu me kuka aikata ke da É—ana Jabir?"

Ƙyaƙyabta idanu ta fara yi tana girgiza mi shi kai, hakan ya sake hassala shi a mugun tsawace har yana miƙewa tsaye yace" Dake nake magana Ummu, me ya shiga tsakanin ku?"
Chapter 103 · 0% Book details