← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 168

Sashe 89

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran da Nabila ta mata ya katse mata tunanin da take yi ta É—aga, cikin matsanancin kuka Nabila ta furta "Aunty Ummu, aunty Ummu."

Take hankalin ta ya watse, tunanin damuwar ta ya gushe, da kulawa ta furta "Nabila, ke ce? Lafiya? Me ya faru? Me aka miki?"

Cikin kuka Nabila ta sake cewa "Ni ce aunty Ummu... Dan Allah ki taimaka min?"

Hankali tashe Ummu ta sake faÉ—in "Nabila, kuka fa kike? FaÉ—a min me ya faru? Me aka miki?"

Cikin tsananin kuka Nabila tana share idanu tace "Aunty Ummu sun kore ni, sun wulaƙanta ni, sun ce bana da tarbiyya da mutumci, ni kawai gida zan dawo, aunty bana da kuɗin mota, dan Allah ki taimaka, ina so na zo gida wajen ki yau."

Lumshe idanu Ummu tayi tace "Hasbunallah wani'imal wakil!"

Shiru tayi na sakanni kafin tace "Kina ina Nabila?"

A taƙaice ta furta "Agadez."

Cikin rarrashi Ummu tace "Shikenan, karki damu, bari na bayar a ciro miki ticket, komai dare za ki zo gida yau in sha Allah."

Cikin kuka tace "To aunty, nagode."

Da sauri Ummu tace "Sannan, ki riƙe katin ki da kyau, zan tura miki kuɗin da zaki sha ruwa a hanya, kin ji?"

Wani Sabon kuka Nabila ta fashe da shi tace "Aunty an sace komai nawa, shiyasa na kira ki da wata wayar, sun kwashe komai aunty, har..har sarƙar ki ma."

Cikin kulawa Ummu tace "Subhanallah, amma dai babu abinda ya same ki ko?"

Girgiza kai Nabila tayi tace "Babu, idan na zo zamuyi magana aunty, kaina ciwo yake sosai."

Da haka suka yi sallama Ummu ta manta da matsalar ta saboda neman Khamis da tayi ta tura shi ya ciro ticket ɗin, da kuma taimakon shi aka samu abokin shi dake aiki a wurin tura kuɗi Nabila ta samu kuɗi a hannun ta kashh! Ba jimawa ta hau mota dan dawowa garin ta, kuma har lokacin ba ta daina kuka ba sboda abubuwa dayawa dake ta zuwa mata ƙwaƙwalwa.

********************

Tun la'asar ciwon marar nan ya sake tsananta gare ta, a daddafe tayi sallah ta canza kaya, wuya tayi wuya sai gashi da kan ta ta ba Kuwailat wayar ta tace ta kira Baban ta ce za ta tafi asibiti, kafin ta kira shi ɗaki ta koma ta saka pad kamar wata mai jinin haila saboda tun jiyan nan take yoyo wanda ba ta jin daɗi haka ko kaɗan, fatan ta ita dai ba wata gagarumar matsala bace, yana bata OK ta sa kai ta fita a motar ta zuwa asibitin kuɗin. Bayan cika ƙa'ida da sharuɗai dai ta samu ganin likita daf da magariba.

Tsura mata idanu ya yi, tun yana kallon ta da gilashi har ya cire ya aje shi gefe, jim kaÉ—an ya fara É—an lashe baki yana tausasa kallon shi gare ta kamar mai son jawo hankalin ta, ba yarinya bace ita, kuma sarai ta gane me kallon shi ke nufi gare ta, amma ba ta san matsalar ta ce ta jawo yake mata wannan kallon ba.

HaÉ—e fuska tayi sosai, ba dan rashin kunya ba ya kalli kamar ta yasan dai ta girme shi, amma yana mata wannan iskancin? Mtsssss! A É—an kausashe tace "Ina ji likita, sauri nake, ina da abun yi."

Muƙut! Ya haɗiye yawu tare da gyara zama, alƙalamin hannun shi ya fara wasa da shi cike da shaƙiyanci yace "Madam, matsalar ki ba babba bace idan kika ɗauki mataki, ba wani abu yake damun ki ba, kuma ba ciki bane kamar yadda kika ce kina tunani, kawai dai hanyar fitar ruwa ce ba'a buɗe ba."

Yatsina fuska tayi tace "Ban gane ba? Fahimtar da ni?"

Saida ya wulwula idanu sannan ya sake gyara zama cikin raɗa yana tsare fuskar ta da kallo yace "Kin gane, kamar dai kwalbatin da ya cika da ruwa, sai kuma aka toshe ƙofofin da zai iya ambaliya, Kinga ai an cutar da shi, dan cikin biyu za'a yi ɗaya, imma ya yi bindiga ya fashe ya shafi gidan kowa, imma a bashi hanya ya wuce."

Da irin hassala ta nuna kan ta tace" Zauren ce ka min, nufin ni ce kwalbatin?"

Cike da shaƙiyanci likitan ya sake tausasa murya yace" Madam, kin fi kwalbati, dan ke alamu ya nuna ƙorama ce, ƴar talatin fa ce, shekarun haɗari ga mata kenan, Madam, mafitar ki ɗaya ce, ko ki samu mai fito da ruwan nan, k..."

Da azama ta miƙe tsaye tana huci, kallon shi take a kausashe sosai tace" Wallahi ba dan a aikin ka na same ka ba, da na tsintsinkawa fuskar ka mari, banza da bai san darajar mace ba, ka dinga bu irin na mutane mana, amma wannan ai halayyar alade ka ke yi."

Ƙasa da sama ta harare shi tare da ɗaukar katin ta da jakar ta da makullin mota zata fice tace" Kare kawai, kuma! Allah ba zai barka haka ba wallahi, komai daren daɗewa sai an wa wacce ka fi so a rayuwar ka haka."

A ƙufule ta fita daga ofishin nashi, tana kaiwa daidai ciriddor da babu mutane ta durƙushe ta fashe da wani irin kuka marar sauti...

*Jabir* da shima fitowar shi kenan daga gurin wani likita da suka san juna ya kuma yi alƙawarin kawo masa ziyara ne ya tsaya cak, bai gane wacece ba dan fuskar rufe take tsakanin guiwowyin ta, amma dai ya ji ba daɗi duba da mace ce a wurin tana kukan wata matsala, gashi kuma alamun ta ya nuna mai aure ce, dan haka kuma ba ya so ya mata magana tunda bai san ta ba.

A hankali yake takawa kamar mai sanɗa zai wyce, sautin takalmin mutum da Ummu ta ji ya sa ta saurin ɗago kai ta kalli inda take jin sautin, suna haɗa idanu da Jabir da mamakin ya aka yi ya zo nan? Ta san kuma sai ya tambaye ta, dan haka ta zabura ta miƙe tsaye ba tare da ta juya ba kawai ta kama hanya da sauri dan bata so ya mata wata magana. Tun miƙewar ta tsaye makullin motar ya faɗi da niƙab ɗin ta dake rataye jikin hannun jakar ta, mamakin ganin ita ce da kuma yadda ta fita ya sake tabbatar masa da matsalar dai kenan? A hankali ya tako ya ɗauki makullin da niƙab ɗin sannan ya fita shi ma.

Jikin motar ya same ta tana ta duba jakar ta, har ya tsaya gefen ta yana kallon yada take neman makullin a rikice hannayen ta sai ɓari suke bata san yana tsaye ba, ya gane ba zata iya tuƙi ba, sai kawai ya furta "Gashi nan, mu je."

Daga haka bai sake cewa komai ba, motar kawai ya buɗe ya shiga tare da tayar wa, kallon shi tayi, karo na farko da ta ji halin shi bai mata ba, ita ce zai wani cewa wai gashi nan, Muje? Kamar wani mai iko da ita? Tsaye tayi tana kallon shi ranta duk ya sake ɓacewa, inda Jabir kuma ke ta kallon hanya ynajiran ta shigo kuma yayi niyyar ba zai sake mata magana ba sai dai su kwana wurin nan.

Tsamukar da marar ta ta sake yi, da kuma jin kamar jini ya bulbulo ta gaban ta yasa ta dafe marar ta cije leɓe, a hankali ta shiga takawa har ta buɗe baya ta zauna idanun ta a rufe, waina idanu Jabir ya yi sannan ya tayar da motar suka bar harabar asibitin.

Yadda idanun ta ke rufe haka ta ke hango likitan nan yana mata kallon iskanci da maganganun da basu dace ba, shaf sai ta manta tare da wa take ta fashe da kuka na ƙunar rai da takaici, a hankali Jabir ya ji jikin shi na tsuma, tsigar jikin shi na tashi saboda yadda take rera kuka, nutsuwar kuma da gaske neman ƙwace masa take yi, dan haka yayi gaggawar taka birki a inda ya dace ya yi shiru, ita ma jin ya tsaya sai ta dakata da kukan sai shasheƙa take, sun jima haka kafin cikin nutsuwa ba tare d ya juyo ya kalle ta ba yace "Maama me ke faruwa?"

Irin a hassalen nan tace "Ba komai."

Tana kallo ya gyara madubin mota dake tsakiya har saida ya hango fuskar ta a ciki, ba alamar wasa ya sake cewa "Da komai, me yake faruwa?"

Har runtse idanu take tsabar bala'i tace "Ba komai na ce maka, dan Allah ka kai ni gida wajen Mama, ko ka bani na je."

Numfashi ya sauke yace "Abba ya san za ki je can?"

Saida ta fashe da wani marayan kuka tace "Bai sani ba, Jabir can nake so zuwa wajen Mamana."

To shi kam ba za'a yi haka da shi ba ba, dan haka tsaf ya tuƙa motar zuwa gidan auren ta ba gidan Mama ba, tana kula da haka ta sake gyara zama ta ce "Jabir gidan Mama, sabon gidan su."

A daƙile ya amsa da "Na sani, tunda Abba bai sai ba bai kamata ki je ba."

Kam bala'i! Kam bala'i ! Me Jabir nufi? Ko Dai bai gane ta bane? To amma ba ta yanayin daɗi gaskiya, dan haka ba ta tanka mishi ba kawai ta ƙyale shi suka isa gidan. A wannan dare dai ta ci kuka kamar za ta mutu, sai dai ta yi niyyar za ta je gida ta faɗawa mama abinda ke faruwa, dole ne wannan.
Chapter 89 · 0% Book details