← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 168

Sashe 74

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro idanu Nabila tayi ta kalle ta, sai kuma tayi murmushi tana gyara tsayuwa cike da kunya tace" Ah haba dai Mama, ai ba zamu yarda muyi ciki, ina shan magani kuma shima yana kulawa ta hanyar anfani da kor..."

Mama Nuriyya dake ma Nabila kallon kamar Æ´ar da ta haifa tunda tana da Æ´an mata ne tayi saurin daka mata tsawa da" Ke? Wa ya tambaye ki?"

Hajia da ta kyaɓe fuska alamar za ta yi kuka Yaya Bilal ta kalla tace" Dan Allah kira shi a waya ya fitar min da ita daga gida."

Da ladabi ya jinjina kai ya ciro waya ya kira lambar Fahad ɗin, ta jima tana ƙara saida ta kusa tsinkewa ya ɗaga, a taƙaice ya ce da shi" Ka sauko ƙasa kana da baƙuwa."

Da tsananin mamaki Fahad dake sharar bacci yace" Baƙuwa kuma? Daga ina? Wacece? Ko dai baƙo?"

Saida ya saci kallon Nabila sannan yace" Nabila ce."

"Nabila?" Ya faɗa da ƙarfin gaske tare da zabura ya tashi zaune yana sake maimaita "Beelata dai?"

Kafin ma a bashi amsa ya yanke kiran ya taso daga shi sai wando tree quater ya sauko daga saman, tunda ya fara tako matakala Nabila ke kallon tana murmushi har ya zo tsakiyar su yana kallon ta shi mamaki ne yake kashe shi na yadda ta zo bata sanar da shi ba.

Duk zuba musu idanu sukayi, Nabila kuma da fara'a tana kallon shi tace "Barka jariri."

Satar kallon Yaya Bilal yayi da shi mamaki ne suke bashi, Fahad kuma farin cikin shi ɗaya ba Abbu Mukhtar bane da zai dinga mishi kallon da shi da kan shi zai ji kamar yayi fatan mutuwa, Sabeer kuma, da shine ai da tuni ya kashe shi da mari, Beela kuma da tuni ya karya mata ƙafa ya watsar à ƙofar gida, cikin raɗa yace mata "Me ya kwo ki nan Beela? Ya zaki zo gidan mu kai tsaye? Baki san akwai kuraye bane?"

Saida ta kalli Hajia da Yaya Bilal sannan tace "To nima ba kurayen na baro can ba, kuma kasan da su ai, magana na zo muyi sannan na fito da kai daga kurkukun da aka saka ka."

Juyawa yayi ya kalli Hajia, sai kawai ya kalli Nabila ya É—an yi gaba yace "Muje waje za mu yi magana."

Ɗaukar jakar ta tayi tare da kallon su dukan su tace "Sai anjiman ku." Sai kuma ta kalli Hajia ita kaɗai da duk tayi kamar bata hayyacin ta tana kallon su tace "Mama dan Allah kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai."

Tana faÉ—a ta bi bayan Fahad suka fita farfajiyar, Yaya Bilal na ganin fitar su ya zaunar da Hajia yace "Mamie, dan Allah kar hakan ya É—aga miki hankali, zan É—auki mataki akan abun nan, ki masa addu'a kawai."

Bai jira Cewar ta ba ya fita shi ma dan uzurin gaban shi, Mama Nuriyya ce ta zauna kusa da ita tana rarrashi. Fahad kuma suna fita ya dafe ƙugu cike da masifa ya fara faɗin" Nabila da uban wa muka yi da ke zaki zo nan? Tunda muke na taɓa zuwa gidan ku kai tsaye haka? Ya zaki ja min wata jarabar?"

Tsaki tayi da irin abun bai dame ta ba ta zauna kan akwatin ta tace" Ka ga dan Allah samo min abinci na ci, wallahi yunwa nake ji kamar masifa, ban ci komai ba tun jiya."

Harara ya maka mata sannan ya juya a fusace ya koma falon, yana shiga duk da ya gan su zaune bai kula kowa ba ya wuce madafa, jim kaɗan ya dawo ɗauke da flate shaƙe da lafiyayyan abun ci, yana zuwa ya miƙa mata, kallon hannun ta tayi da tasan yana buƙatar ta fara wankewa, amma dake ba ruwa kusa sai kawai ta kawo wandon Fahad dake jikin shi ta goge hannun sannan ta saka ta fara ci tana faɗin "Jariri, ashe à wannan fadar kake rayuwa? Gaskiya ku masu kuɗi sosai, shine dan munafunci ka kasa mayar da ni sarauniya kake yafata min canji kawai."

Cike da takaici da fargaban zuwan Abbu Mukhtar ko Sabeer dan shi su kaÉ—ai yake shakka yace "Nabila, me ya kawo ki?"

Kallon shi tayi tace "Na gaya maka ai."

Jinjina kai yai yace "Shikenan, yanzu ki je ki samu taxi ki ce ya kai ki duk hôtel ɗin da ya sani, idan kin sauka zan kira ki faɗa min zan je na same ki can."

Saida ta juya mishi baki sannan tace "Ban da kuÉ—i, kuma ina so na je salon ma, wannan kitson ya ishe ni."

Wani huci ya sauke yace "Nima ban da kuÉ—in."

Sama da ƙasa ta kalle shi tace "Ƙarya kake, ai na daina yarda da kai yanzu wallahi idan ka ce baka da kuɗi tunda na ga gidan ku."

Saida ya sake maka mata harara yace "Shikenan, bari na samo miki wajen Hajia, amma fa ni bana da kuÉ—i, ai kinsan ba neman su nake, dayawa da nake kashe miki satar su nake yi, haram ce kike ci."

Juyawa yayi a sukwane, cike da shaƙiyanci tace "Nake ci? Kake ci dai, kuɗin da kake bani ina ci nima ba ci na kake ba, ka ji ƙaramar ɗan iska kai."

Juyowa yayi ya harare ya ja tsaki yace "Ƴar wahala."

Sama da ƙasa ta harare ita ma tace "Wahalallu dai." Ta faɗa tana ci gaba da cin abincin ta dake ɗauke da nama kuma gashi ya mata daɗi sosai.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*36*

Yana shig falo kusa da Hajia ya zauna cikin rarrashi saboda kallon tuhuma da take mishi yace "Mamie, dan Allah ki bani wasu Æ´an kuÉ—i zan ba yarinyar can ne ta tafi, ni ban da ko sisi a jikina."

Kamar za ta fashe da kuka tace "Fahad, yanzu wannan rayuwar ka ga tana gyara ka ko? Yanzu idan mahaifin ka ya same ta gidan nan fa? Ba kai ba har ni ba zan ji daÉ—i ba."

A tausashe yace "Mamie ai shiyasa nake so na sallame ta ta tafi kafin ya shigo."

Gaskiya ya faÉ—a, dan haka tace mishi "Je ka É—akina ka É—auko min jaka ta akan gado?"

Da farin cikin samun yadda yake so ya tashi ya nufi ɗakin, Mama Nuriyya dai na kallon su bata tanka musu ba, saida ya dawo da jakar sannan ya bata, kuɗin ta ciro isashi ta bashi, da fara'a ya karɓa yace "Nagode Mamie."

Da sauri ya sake fita daga falon, yana zuwa ya same ta tana cin abincin, karɓe farantin yayi ya bata kuɗin yace "Karɓi, maza dan Allah tashi ki tafi Nabila, bana so Abbu ya shigo ya same ki, idan kin isa ki kira ni zan zo."

Miƙewa tayi tana hararren shi tace "Ka ji haushi Fahad, ni kake ma rowan abincin gidan ku, kai arrr wallahi."

Bai kula ta ba saboda kuɗin da ta karɓa tana dubawa, murmushi tayi ta saka su cikin bras ɗin ta sannan ta ja jakar ta tna faɗin "Jariri sai ka zo, nayi kewar ka fa."

Har ta ɗan wuce sai kuma ta juyo ta dawo, da mamaki yake duban ta har ta zo kusa da shi, bai ankara ba kawai ya ji hannun ta a dokin shi bakin ta kuma cikin nashi baki, kamar wata mayunwaciya cike da shaƙiyanci ta kamo harshen shi ta tsotsa kamar za ta cire mishi baki tana murza dokin shi sannan ta sake shi ta mishi murmushi, ɗaga mishi gira tayi sannan ta koma ta ja jakar ta ta tafi.

Kallon ta yake yana lashe leɓe, ta tsokano shi, ji yake kamar... Cike da shegantaka ya sake lashe baki yace "Wow! Shegiya Nabila."

Saida ya ga ta fita daga ƙofa ta biyu ya sauke ajiyar zuciya, yana juyawa dan komawa ya sauke duban shi kan Mama Nuriyya da ta ga komai, suna haɗa idanu kawai ta kawar da kan ta tare da saurin nufa nata ɓangaren tana mishi addu'ar shiriya, Fahad kuma ko a jikin shi sai ma shigewa falon da ya yi, duk da ya ga Hajia zaune tayi tagumi bai tsaya wajen ta ba ya haura sama dan ya shirya kafin Nabila ta kira ta faɗa mishi masaukin da ta samu.

*******************

Tun daga nesa Ummu da ta taho take jiyo hayaniyar dake tashi daga falo, tun kafin ta shiga ta gayyato murmushi a fuskar ta sannan ta cire takalmin ta, cikin sanyayyar murya ta rangaɗa sallama, daga ciki suka amsa mata sannan ta shiga ɗauke da kyakyawar tasar furar nan, kallon duk mutanen ɗakin tayi da fara'a à fuskar ta tace "Sannun ku da hira, kuna ta shan hira abun ku?"
Chapter 74 · 0% Book details