← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 168

Sashe 94

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*44*

Tare suka fito cikin shirin tafiya masallacin, yana gaba yana ta faman saɓa babbar rigar shi inda Ummu da Kuwailat ke baya tare da zagayawa zasu shiga motar, mai gadi da ya hangi fitowar su ne ya taho da gudu, gaisawa sukayi da Ummu kai tsaye kuma suka gaisa da Alhaji, sannan ne yake sanar da shi "Alhaji dama akwai wasu ma'aikatan wutan lantarki da suka zo ɗazu nan zasu yi aiki, sun ce an samu matsala ne da waccen dogon tsanin gashi kuma damuna ke tafe in sha Allah, to da suka zo ɗazu sun ɗauka ma aikin ba zai jima ba, amma sun ce gobe zasu dawo su ci gaba, da yiwuwar a share awa ashirin da huɗu, duba kuma da gudumuwar da kuke bayarwa, yasa suka ci to a sanar da kai, dan har a gidan redio ma an faɗa za'a samu ɗaukewar wutar wasu unguwanni dan jama'a su sani."

Da kulawa Alhaji yace" Asha kuwa! Ka ga kuma ban ji ba wallahi, Gwara da ka sanar da ni, hakan zai sa mu ankare kam."

Jinjina kai mai gadin yayi yace" Hakane Alhaji, kuma naga ai da generator."

Shima jinjina kai yayi yace" Hakane, in sha Allah ma zuwa goben zan tayar da shi."

Juyawa yayi a ladabce yana faÉ—in" To nagode, zamu É—an fita ne nan masallaci, sai mun dawo."

Da addu'ar a dawo lafiya ya bi su sannan suka fice, Ummu na jin duk abinda suka tattauna, ita a WhatsApp ta gani da sunayen unguwannin da aikin zai iya shafa, kawai bata sanar da shi bane dan bata son magana da shi. Haka suka É—auki hanya ba wata hira sosai tsakanin su, shine ma dai da ya fi damuwa da kar Kuwailat ta fahimci abinda ke faruwa har yake É—an cewa Ummu É—in "Kina ganin na tura Kuwailat tare da Hajia Atika da zata tafi umra azumin nan? Ko na bari ta tafi Hadj sai na zuba muku tare?"

Duk da ta ji daɗin hakan sosai, dan ba abinda zai kai a mata albishir ɗin tafiya ƙasa mai tsarki daɗi a rayuwarta, amma dai bata nuna farin cikin a fili ba tace" Gaskiya zan so na tafi tare da abata."

Farin ciki ne ya bayyana fuskar Kuwailat, dan gaskiya bata ga sakewar da zata yi ba tare da Maman su Zeinab, bata san me ta musu ba? Amma dai ba wanda take zuwa ɓangaren shi ta zauna bayan Hajia babba, dan haka ita ma take nesa da su, jinjina kai yayi yace "Shikenan, Allah ya kai mu."

Fuska a ɗaure Ummu tace "Ameen, Allah ƙara arziƙi."

Daga haka basu sake cewa komai ba sai shi da Kuwailat dake hira yana bata labarin ƙasa mai tsarki da abubuwan da za ta gani idan Allah ya ƙaddarar tafiyar ta, anan ne har yake faɗa musu mutanen da ya zuba ma zasu tafi, biyar a cikin dangi ne biyar kuma wasu daga cikin maƙwabta wanda suka rage bai biya ma ba.

Sun isa wurin wa'azin, kai tsaye wajen mata suka nufa dake sama suka zauna, tunda aka gabatar da malam da kuma mai ja baƙi wato *Alaramma Jabir Mu'az Mika'il*, lasifika aka miƙa ma Jabir da zai fara buɗewa da surar da malam zai yi tafsirin ta, amma a ƙalla saida ya ɗauki kusan sakan talatin saboda rashin sabo ganin ana haskawa ga kuma mutane da dama, a Saudia da Madina duk ba irin haka yayi ba, a cikin aji ne kawai dan a gwada shi wani lokaci kuma cikin masallaci ne a wani ɓangare na masallacin, yana fara a'uziyya bai kai ga bismillah ba masallacin ya sake yin shiru sosai tamkar babu mutane a cikin shi, dan ko sautin numfashi wani ba ya jin na kusa da shi. Haka kuma ya sa Ummu da suma sukayi shiru ta ji tsigar jikin ta ta tashi sosai, gabanta ya wani yanke ya faɗi irin a sanyayyen nan, wani irin yanayi ta ji tana samun kan ta da duk ta tsargi kan ta, hakan yasa ta sunkuyar da kai sosai tana ci gaba da sauraren suratu Aal'Imran, saida ya kai inda zai tsaya ya dakata malam ya fara wa'azi, wa'azi malam ke yi cikin nutsuwa da kamanta faɗin abinda yake daidai, inda Jabir ma ke nashi aikin, dan duk surar da ya buƙaci ya kawo haka zai jawo ta, abun burgewa ga Alarammomi bai wuce yadda idan aka ce su bayar da misali ba tare da an sanar da su surar ko shafi ko aya ba suke kawowa, haka Jabir shima ya kasance yana yi. Daga ƙarshe tafsiri yayi nisan da har saida malam ya dinga nusar da al'umma akan kallon abubuwan batsa da kuma sauraren abinda bai dace ba, tare da faɗa musu gaskiya ranar gobe kowace gaɓa dake jikin mu mai bayar da shaida akan muce kuma zata yi magana ita ma.

Take Ummu ta ji kamar da ita ake, ta tsargu sosai sannan ta sake yarda ashe da gaske ne da ake cewa malamai na iya wa'azi su taɓo abu ka ji kamar da kai kawai suke. Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Ashe ta jima tana aikata saɓo? Ya aka yi ta manta da abinda ta karanta? Ya aka yi ta manta da abinda malam ke faɗa yanzu? Ya aka yi ma ta manta da abinda Alhaji ya faɗa mata cewa ta san me za ta yi da waya, dan waya da take gani za ta iya kai ta wuta kuma ta kai ta aljanna, dalilin da ya sa ma kenan yake ƙarfafa mata guiw akan grps ɗin su da suke abubuwan ƙaruwa da wayar da kan mata, wanda dalilin haka har suka buɗa grp na taimakon junan su da marayu da marasa ƙarfi.

*Kuka* ta ci sosai, har saida ta kusan ta ta yi tunanin ko karatun da sabon Alaramma ke ja ne, dan gaskiya matashin nan akwai murya, ga taushi ga zaƙi ga sanyi, Ummu kuma ita kaɗai ta san me take ma kuka, har dariyar da ta ji an ɗauka à masallacin yasa ta ɗaga kan ta, ba ta san me aka ce ba wallahi, amma sai ta ji na bayan ta na faɗawa wata da ita ma bata ji da kyau ba tana cewa _"Malam ne ya ce wai yana gabatar mana da sabon Alaramma da in sha Allah zasu yi tafsirin azumi tare, kuma wai gauro ne baya da mata, dan haka a cikin mu mu bashi ƴar mu mai nutsuwa da za ta iya ƙara zaburar mana da shi mu sha ruwan ayoyi, amma fa ba ƴar zamani ba wacce idan ta gaso shi daga gida zai zo ya yi ta ja mana ayoyin mata a wuta."_

Hakan bai sa Ummu murmusawa ba saida ta ji yanzu malm ɗin na sake faɗin" Hakane mana, wallahi duk muraja'ar shi idan ya haɗu da mace sai a hankali, haka zamu ga matashin zakin nan namu a gigice ya zo yana haɗa mana hadda wuri ɗaya, mu muna tafsirin kafiran ƙuraishawa shi yana kawo mana hadisin dake nuna butulcin mata ga mizajensu."

Murmushi kawai tayi, ita ba ta ma taɓa hasaso matar da Jabir zai iya aura ba, amma dai tana masa fatan samun ta gari kamar yada yanzu ɗin ma malam ke ta mishi addu'a da fatan alkairi dan sosai ya san Jabir, dan shi da za'a bashi dama zai iya bayar da tarihin Jabir ko zai zama izina ga matasan yanzu.

*********************

Yana daf da shiga falon yaji Hajia na magana a tausashe tana faɗin "Ka yi haƙuri Alhaji, ban so haka ta faru ba, amma zai fi kyau ka tafi da Fati gida, idan tana da wanda take so ko ya dace da ita ka aurar masa ita, Fahad ya ƙi yi mana biyayya, kuma gaskiya ni dama tun farko ban goyi bayan Alhaji da yake cewa zai aura masa ita dole ba, ko da Fahad bai gudu ba kamar yadda ya ce, zai iya takurawa Fatima da gallazawa kala kala, wanda kuma kaga hakan ba zai ma kowa daɗi ba, dan Allah kuyi haƙuri da ɓata muku lokaci da muka yi."

Jinjina kai Alhaji Abbas yayi cike da gamsuwa yace" Ba damuwa Hajia, nima saida nayi ƙoƙarin fahimtar da Alhaji haka, amma ya nuna Fahad ba shi ya haife shi ba, shi kuma irin wannan abun ba'a masa hawan ƙawara, yau idan muka aurar da shi ba ya so, ba wai dan Fati na ƴata ba, amma ina daɗi kuma kullum muna hanyar tara su yi musu sulhu? Ko kuma muna kokawa da matsalar su? Ai ba'a samu ci gaba ba a haka kuma, amma tunda ke kin fahimta ba komai, Allah ya zaɓa musu ma fi alkairi."
Chapter 94 · 0% Book details