Sashe 123
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Narai-narai tayi da idanu, ta kalli Alhaji da shi kuma yake kallon Jabir da mamakin ƙarfin halin shi, sannan ta kalli Aliyu da shima har da karkace kai yana kallon Jabir ɗin, take taji idanun ta suna neman kawo ruwa saboda saurin kuka da take da shi, ba dan komai ba sai dan jin wai Jabir, Jabir dai, Jabir dai yaron nan ne ke kora mata wannan kashedi haka mai kama da gargaɗi, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wai me yasa Jabir yake abu kamar dai bai san manya bane? Da gasken gaske harara ta watsa ma Jabir karo na farko a rayuwarta, ga idanun ta da suka cika da ƙwalla, hakan yasa Jabir dake kallon hararen da mamaki yake hango wasu abubuwa na daban a cikin idanun nata.
Cikin rawar murya kamar zatayi kuka tace *"Na san da haka tun kafin a haife ka, kuma ai ba tsirara na fitowa ba, sannan wuyana rufe yake da mayafi, ban ce ka kalli can ba bare ka gani, kar ka sake min irin haka ni ba tsarar ka bace."*
Shi kam sai ya ma manta da akwai wasu bayan shi da ita, ita kawai yake kallo wani sabon yanayi na sake hauhawar masa na ɓacin ran akan me za ta ƙi karɓan gaskiya? Hakan yasa shi saida ya tako kus da Aliyu ba tare da ya rusuna duban shi kan ta ba yace" *Abba ma yayi ba daidai ba zan gaya mishi gaskiya, kenan sheɗan fitsari yake miki a ka Maama? Wace sura kika karanta kafin haihuwar tawa?*"
Duk dauriyar Aliyu saida ya tintsire da dariya yana rufe baki, Abba kuma kallon su kawai yake da wani sahihin murmushi a fuskar shi yana jinjina kai, da yanayin jin haushi tna jin kamar ta mare shi tace" Kai ai kasan na karanta dayawa kafin ka yi wayo, ka daina min rashin kunya Jabir."
Sama da ƙasa ya kalle ta, sai kawai ya taɓe baki yace" Ni dai na gaya miki kar ki sake fita babu rufi a jikin ki, dan ubangiji zai ƙona ki, ni da Abba kuma ai ba zamu so haka ba."
Sai kawai ya juya zai bar wurin ya kalli Abba dake ci gaba da kallon su yace" Abba, kai ka gaya mata da kan ka, dan gani take ta haifi kowa anan, bayan bata wuce *a zaneta ba* saboda *ƙuruciya*."
Ko waiwayowa bai yi ba ya shige cikin gidan ya bar Ummu na share hawaye, Alhaji ta kalla da ya sauke ajiyar zuciya tace" Kana ganin shi ko? Dan na bar gidan ka shine zai dinga min rashin kunya?"
Saida ta shige mota ta rufe ta tayar sai kuma ta leƙo ta kalli Aliyu tana ƙara share hawayen ta tace" Kuma ka faɗa masa kada ya sake kirana Maaman shi, dan ɗan baya wa uwa fitsara."
Saida ta tayar musu da ƙura Aliyu ya sake sheƙewa da dariya yana kallon Abba da shima dole ya murmusa yana faɗin" Jabir, wa ya faɗa maka ana ma uwar auta haka? Ita fa ganin ta take ta haifi duniya."
Da sauri Aliyu ya wuce ciki yana fadin" Bari 'a je na sanar masa da saƙon nan." Da dariya Abba ya bishi da kallo dan ya san akwai daru a gaba kam, amma kuma ya birge shi ba kaɗan ba, to ai san girman Ummu ya sa take ganin kamar Jabir bai isa ya mata magana yadda ya mata ba, bayan kuma gaskiya ya faɗa mata sannan a nutse da ladabi.
Aliyu na shiga ya haɗe da Jabir tare da Hayat suna gaisawa, saida ya bari Hayat ya tafi sannan ya riƙo hannun Jabir yana kallon shi yace "Malam, ya haka wai ? Me yake damunka ne? Maaman ka ce fa yau ka wanke haka tasss?"
Yatsina fuska yayi yana ciro wayar shi yace "To sai me? Gaskiya f de ba za'a faÉ—a mata ba ita?"
Sai kuma yayi ƙwafa, wai yaro? Kuma ta ce aka haife shi? Shine za ta ce ta karanta sunan nan kafin a haife shi? Shi ɗin? Nawa take ɗauke da ita wai? Nawane duka shekarun nata? Wata ƙwafar ya sake yi ta jin haushi ya fara danna wayar shi, Aliyu kuma da murmushi yace "Na sani, amma ai sai naga kamar kana jin haushin ta kake magana, sosai fa ka cizga maama."
A É—an hassale ya kalle shi yace "Ka rabu da ni Aliyu."
Taɓe baki Aliyu yayu yace "Na ji, amma ta ce in faɗa maka kar ka sake kiran ta da Maama, dan ɗa ba ya raina Maaman sa."
Wani kallo ya ma Aliyu, sai kawai ya raɓa shi zai wuce yana faɗin "Ba sai ta faɗa ba ma, ni kaina ba zan sake ba, amma kafin na daina bata isa hana ni faɗa ba yanzu, wai ita me ye matsalar ta? Me take ɗaukar kan ta ne? Haihuwa tayi?"
Cikin jin haush yayi tsaki tare da wucewa yana ce ma Aliyu "Muje sabgar gaban mu dan Allah."
Karo suka ci da Ahaji da ya ji komai da ya faru, a taƙaice suka mishi sallama da sai sun dawo ya musu addu'ar Allah ya tsare.
*Alhamdulillah.*
[25/08 à 15:27] MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*58*
Cike da gajiya da zancen Mama ta sake riƙe haɓa tana faɗin "Yau ni naga ikon Allah ! Ke wai akan Jabir ɗin kike wannan hawayen? Dan ya ce ki daina saka gyalen?"
Kallon Mama tayi tana share hawayen, ita kan ta so take su tsaya tace "A'a mama, ni ba dan ya ce na daina bane, Mama yadda Jabir ke min magana kamar wani shi ya haife ni, wai har da ce min kenan sheɗan fitsari yake min a kai? Kuma wai ni yake cewa bai wuce a zane ni ba saboda ƙuruciya, Mama Jabir fa, ke la ai kin san nan yayi wasan ƙasa a tsakiyar unguwar nan ko?"
Galala Mama ta kalle ta, ko Jabir yayi wasan ƙasa, ita shekara nawa ne gare ta lokacin? Shekara fa uku ne tsakanin ta da Jabir, girgiza kai tayi ta miƙe tana faɗin" Allah ya kyauta."
ÆŠaga kanta tayi ta bi Mama da kallon ita yanzu ba ta ga wannan rainin wayon da ya mata ba? Shigowar Nabila da gudu gudu É—auke da kaya ya sa Mama dakatawa tana cewa" Ke lafiya? Me ye haka za ki shigo a haukace?"
Da fara'a Nabila ta kalli Mama sannan ta kalli Ummu tace" Mama, aunty Ummu kinyi baƙo a waje, ana miki magana."
Da mamaki dukan su suka maimaita" Baƙo kuma?"
Sai Ummu da ta É—ora da" Ni É—in?" Da zumuÉ—i Nabila tace" E mana aunty, tashi kije dan Allah, wallahi babban mutum ne."
Tsaki Ummu tayi tace "Kuma sai yace ni yake nema? Ke bana son iskanci?"
Kallon Mama Nabila tayi tace "Wallahi Mama da gaske ne, a ƙofar gida na gan shi ya ce gidan su Ummu Kulsum yake nema."
Taɓe baki tayi tana miƙewa za ta shige ɗaki tace "Ki ce masa ba zan zo ba, jaraba kawai, me zan masa? Yaushe la na fito daga gidan da za'a dame ni."
Da sauri Mama ta kalle ta tace "Ke! Zo ki wuce ki ga wanene."
Turo baki Ummu tayi cike sa shagwaɓa tace "Mama ban san fa ko wanene ba, kuma Kinga ma yaushe na fara zawarcin?"
A tsawace Mama tace "Ke bana son iskanci Ummu, zaki wuce ko sai na raka ki har wajen?"
Da sauri ta É—auki gyalen ta data aje kan kujera ta yafa zata fita tana ta kumbure kumbure, har ta kama hanya Mama tace "Da gyalen zaki kuma fita bayan É—an naki ya hana?"
Juyowa Ummu tayi, sai taji kamar maganar Maman ta fi ma sosa mata rai fiye da ta waccen ja'irin yaron, amma sai tayi shiru tunda ai gaba da gaban ta, ficewa tayi zuwa ga wanda ke neman nata a tsanake.
*Tsaye* ta samu dattijon jingine a motar shi cikin manyan kayan da suka ƙara mishi kamala, tana ganin fuskar shi ta sake tahowa a nutse tana gane inda ta taɓa ganin fuskar, tabbas shine wanda ranar suka gani zaune a shagon da suka siyo kayan kicin ɗin Nabila, a tunanin ta kuma kamar shine mai shagon duba da ranar yadda yaran shagon ke ta faman rusuna mishi.