Sashe 30
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Ema dake son sanar da Sa'ad ɗin wani abu ya matsa nesa da Hambali sannan yace "Oga, ai tun za'a kawo ta na faɗi wasu ƙa'idoji da ya kamata a kiyaye, misali shan abu mai zafi, zai taimaka wajen narkewar robar da wuri lokacin narkewar ta baiyi ba, shan abu mai sanyi ƙwarai kuma zai sa robar tayi gautsi ma'ana kamar bokitin robar da rana ta daka, shi ma dai Kaga fashewa ne a ƙanƙanin lokaci, magana ta gaskiya oga Hambali ba yana son ganin yarinyar bane dan wani abu, yana son ganinta ne dan ya killace ta a wannan asibitin tamu a ɓangaren mahaukata."
Da ƙarfi Sa'ad ya furta "Me? Mahaukata ? Saboda me to?" Duk yayi tambayar yana barin madafar tare da nufa falo kai tsaye ya bar Aisha da tunanin wane irin sakaci ne ya sa shi zubar da abincin, a asiirinci Ema yace "Yallaɓai, yau na ji yana waya game da wata cigiya da ake yi a gidajen telebijin na wata yarinya da ake nema jika ga Saheeb Ahlan, koma wacece yake waya da ita ina kyautata zaton bata da kyakyawan nufi akan yarinyar nan da nake da tabbacin ita ce wannan ƴar da ake nema da tsabar kuɗi miliyan biyar ga wanda ya san wata masaniya a kan ta, Oga, ka yi wani abu dan ka ceci yarinyar nan, rabata da iyayen ta ya isa haka, ka da a sake salwantar da rayuwar ta ta hanyar mayar da ita mahaukaciya tuburan, dan Allah ka yi wani abu a kai."
Da maÉ—aukakin mamaki Sa'ad da yayi mutuwar tsaye yace" *Saheeb Ahlan*? Ita jikar shi ce?"
Cike da tabbaci Ema yace" Ƙwarai yallaɓai, na tabbatar da haka, dan shi kanshi bai sani ba saida ya ga Labaran nan yasa aka sake binciko masa cikakken sunan ta, akwai ayar tambaya ga duk wanda ya kawo ta gidan marayun nan, dan kuwa yayi anfani da sunan ta na asali wanda ya san ko ba jima idan ta girma za'a gane wacece ita da wannan sunan ahalin."
Da ɗaure kai Sa'ad ya dinga shawagin a falon musamman da Kaka hankalin ta ke kan telebijin yace" Ahlan fa a Niger suke, ta ya aka yi dogon zango da ita ƙasa mai nisa haka? "
Da rashin tabbas Ema yace" Hakane yallaɓai, nasan kuma zasu yi iya yin su ne dan ganin sun nesanta ta da gidan ahalinta."
Ƙwarai bakin shi so yayi ya ce ma Ema _" Kar ka damu, yarinyar na tare da ni duk wannan lokacin."_
Amma kuma jin wani irin haɗari dake tattare da rayuwar yarinyar mai sarƙaƙiyar gaske, sai kawai ya basar cike da izza da isa yace" Shikenan, zan duba na gani."
Bai tsaya sauraren abinda zai sake faɗa ba kawai ya yanke kiran tare da dawowa madafar nan hankali tare da mugun sauri, shi kan shi bai san me ye ba, amma dai daga ƙasan zuciyar shi yake jin rudun na sake hauhawar masa. Yana shigowa Aisha ta ɗauki bokitin ruwan za ta juyesu a banɗakin dake ciki, wata damƙa ta ji an ma hannun ta ba zato da ta sa ta saurin sakin bokitin ta kalli wanda ya riƙe ta.
A razane ta sa ɗaya hannun ta ta riƙe wanda ya riƙeta da shi cikin Muryar ruɗu tace "Abbu... Yaya, ka yi haƙuri wallahi zan dinga cewa Yaya, kar ka dakeni ka ji Ab...Yaya."
Ɗora yatsan shi yayi à bakin shi yace "Shiiiii! Je ki ɗauko gyalen ki zaki rankani wani guri."
Wani kallon yan shaye-shaye ta mishi tace "Na raka ka? Ni É—in?"
Sakin hannun nata yayi yace "E, ko ba zaki je ba?"
Ɗan ja baya tayi tace "Abbu ai b..." Kallon da ya mata ya sa ta kame bakin ta, tako ɗaya ya ƙara yi ya zo inda take, da sauri ta ja baya shi ma kuma ya bi ta har saida ta haɗe da ƙofar banɗakin dake rufe, hannayen shi ya buɗe tare da dafe bangon yana kallon tsakiyar fuskar ta. Sosai ya haifar da kusanci a wannan zaman nasu wanda ya gagareta samun numfashi mai kyau, dan gaba ɗaya numfashin shi ma a cikin fuskar ta yake sauka.
Wani narkakken kallo yake bin fuskar ta ta da shi yace "...
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*14*
Wani narkakken kallo yake bin fuskar ta ta da shi yace "Ke wai baki da wani tunani ne sai na za'a miki lalata?"
Lumshe idanun ta tayi da É—an firgici tace "Lahhhh! Ni wallahi ba haka bane Abbu."
Bakin nata ya ƙalla da ta furta Abbu da shi, leɓen ta na sama baƙi sai na ƙasa kuma kalar Pink da sirkin ja shi ma kuma ba ƙwarai ba, ba tare daya ɗauke idanun nashi daga bakin ta ba da ya ke jin wani abu mai kama da haɗiyar yawu a maƙoshin shi cikin wani siririya kuma tattausan murya yace "To me yasa baki yarda ki tafi da ni ba?"
Idanunta na kallon ƙasa bakin ta har rawa rawa yake tace "To ai ba daidai bane ko?"
A hankali, ya fara manta me ye alaƙar shi da ita, dan haka ya sake matsawa har saida ya ji tsinin dogon hancin ta ya taɓa na shi hancin, sai kuma ya ɗan wara idanun shi sosai a hankali ya matsa kaɗan yana cewa "To ai ni *Abbu ake kirana ko*?"
Kallon fuskar shi tayi a wannan lokacin, sai kawai ta saki murmushi har da rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tana faÉ—in "E mana, Abbu."
Jin numfashin ta na yin sama kuma ya ƙi yin nesa da ita yasa ta ɗan kallon haɓar shi dake kewaye da wani matsakaicin saje da gemun da ya zagaye bakin shi gaba ɗaya, da gaske numfashin ta neman ƙwacewa yake, tubarkallah Abbun nata akwai tsayi ga kuma wani sirri da kayan jikin shi suka bayyana wato ƙwanji da murɗaɗɗiyar sura, duk zaman ta da shi bata ganshi sanye da shadda ba, zallar kayan shi yadi ne irin masu kyau ɗin nan da tsada, sai yake musu mabambamta ɗinkuna, wasu dogon hannu wasu gajere, ɗinkuna dai kala-kala kamar wani mai tallar kayan sakawa, cikini ɓarin murya tace "Abbu ɗan matsa mana, ba kyau fa haka ko kaɗan, ai ni ƳAR riƙon ka ce."
Karo na farko a zaman shi da yarinyar da yaji ta saka shi dariyar da har saida haƙoranshi biyu na gaba masu ɗan tsayi suka fito waje, ja baya yayi dan sai zuciyar sa ta raya masa ai hakane ɗin, dafe ƙugun shi biyu yayi yana ci gaba da murmushi yace" Kin yi karatu?"
ÆŠagowa tayi daga bangon banÉ—akin da mamakin tambayar shi tace" E Abbu, na yi."
Ba tare daya daina kallon ta ba yace" Nawa kike ci a jarabawa?"
Cike da fari da idanu wai ita za ta faɗi ƙoƙarin ta tace" jimilla 88 cikin ɗari."
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa yace" Uhum! Amma kuma shine ƙwaƙalwar ki ta kasa gaya miki ni ban isa zama Abbun ki ba?"
Turo baki tayi gaba tare da kawar da kanta b tace komai ba, numfashi ya sauke sannan yace" Muje to, asibiti za ki rakani."
Da mamaki tace" Asibiti, baka da lafiya ne?"
Iska ya feso dake nuna gajiyawar shi da kuma ƙaguwa, ita ma da ta ji bai bata amsa ba sai tace" Oho! Na gane, kenan baka da lafiya ne Abbu, Shiyasa kwana huɗu baka zo ba Hajiata duk ta damu."
Sai kuma ta kama hanyar barin madafa tace" To muje na gayawa Hajia zan kai ka asibiti."
Kallon ta ya so yayi na mamakin ƙarfin halin ta, shi har shine za ta kai asibiti dan bai da lafiya? Wai me yarinyar nan take ji da shi ne? Alamu nuna mi shi suke tana da son barkwanci dama ce kawai bata samu ba, to amma a kan shi ne za ta yi barkwancin nata? Lamari na sheɗan da ba tsoron Allah a ciki, sai ya wani ja idanun shi ƙasa kaɗan da bayan ta ya dire su akan ƙugun ta.... Ya salam! Ya salam! Ya salam! Abinda ya samu kanshi da ambatawa kenan a ƙasan zuciyar shi, bugo ƙofar da ta yi ne ya dawo dashi hayyacin shi har ya zabura ya juya ma ƙofar baya yana zaro ido kamar barewar da ta kubto daga hannun zakin da ya damƙi wuyan ta. To wai! Shi abun mamakin ma anan shine, yarinyar can dake da ɗan matsakaicin jikin can, ita ce ke da wata irin2 dirarriya ƙira haka wacce ta dame ta Fanta da kwalbar sprit? Sai fa da ta juya ne ya ga wani shafaffen cikin ta daya fitar da surar shi tamkar ta sabon wata, hakan ya fito da wani irin ƙugun ta da bashi da tudu sosai, amma dai ƙirar... Kai hasbunallah wani'imal wakil, anya kuwa a ƴan matan da ya gani ya taɓa haɗuwa da mai irin waccen zubin? Anya kuwa *ƴar shi*...?
********************
Azabar wahalar da ta kai mata karo ne yasa cikin zafin nama ta ɗaga hannu ta tabki Uzei ɗin dake goye a bayan ta tana ta kuka wanda ita kan ta zafin ranar da suka dame ta ne take ga kuma yunwa, wannan tiƙar da ta mata yasa ta ƙara fashewa da mugun kuka wanda duk mai sauraro zai gane an ma yarinyar wani abu ne, cikin faɗa da masifa Bara'atu da ta rasa ina za ta sa kanta ta ji daɗi ga bokitin da ta ciko da ruwa tana tafe suna zubar mata a jiki ga zufa saboda ranar da ake ƙwalawa yasa duk tayi wata kala kamar wacce ta fito daga daji. Kamar wata zararriya tana tafe take faɗa wa yarinyar goyen cewa "Wallahi Uzei zan ci ubanki idan baki min shiru, ina dalili ina mafari, abun duniya ya damu mutum ke ma kuma ki addabeni da kuka? Da wane zan ji to? Kukan ki na masifa ko bala'in dake kaina."