← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 168

Sashe 157

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin ya fito ya nufi ɗakin da kayan shi suke ciki ta yunƙura, da gaske fa jikin ta da komai nata ciwo yake, haka a daddafe ta nufi ban ɗaki da niyyar tayi fitsarin da take ji ya cika mata mara, idan ta sauke shi sai ta je ta dafa ruwan zafi masu yawa dan ta gasa jikin ta, da ƙyar ta kai ban ɗakin ƙafafun ta na rawa saboda haka Jabir ya sagar mata da ƙafafu su ba a tsaye ba su ba kwance ko zaune ba. Tana shiga ban ɗaki da sauri ta zauna kan watar dan yin fitsari, wani irin masifaffen zafi ne ta ji ya ziyarce ta tare da jin kamar wani abu zai fito ta gaban ta, tsabar zafin da ta ji ya sa take wasu zafafen ƙwalla suka ziyarce ta, haka kuma duk tsigar jikin ta ta tashi saboda abun ƙwarai ne, a razane ta miƙe tsaye saboda jin kamar tsugunnen ne ba zai gyara ta ba, tsaye tayi tana tunanin me ye kuma wannan? Sai kuma ta saje daurewa ta zauna saboda fitsarin dake neman biyo ƙafafun ta, tana duƙawa dai wannan abun ne da ya sa dole ta sake miƙewa tsaye.

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Ummu ta dinga faɗa a haukace tana daddafe bangon ban ɗakin daga tsaye kamar wacce ke naƙuda saboda jin fitsarin nan na taho mata daga tsaye da wani irin zafin da ita kam ba dan duniya ce tayi ittifaƙin babu ciwon da ya kai na naƙuda, to da sai ta ce akwai gaskiya, dan gashi tana ɗanɗana yanzu haka, abun da ya bata tsoro shine fitsarin fitowa yake irin tsir-tsir ɗin nan kamar yana tsartuwa alamar dai baya fita da kyau, kamar za ta ciji bango haka take ta matse shi, sai da ta ji zafin ya ƙaru fiye da baya da sauri ta yi niyyar duƙawa gaba ɗaya ƙasa ko wai hakan zai fi sauƙi... *Cak*! Ta dakata tana rarako idanu saboda ganin jini na biyo fitsarin ta, haba ai sai ta buɗe muryar ta ta ƙwala ƙara da faɗin "Aaaaaaaaaa! Wayyo Allahna, na shiga uku, Jabir, wayyo Allahna."

Yana tsaye gaban fridge yana shan ruwa ya ji wannan ihu, da gudu ya saki robar ruwan ya nufi ban ɗakin, bai jira komai ba ya tura ƙofar, yana ganin ta tsaye ba kaya jikin ta sai kuma ya shiga ƙarewa ban ɗakin kallo da tunanin ya ga abinda ya tsorata ta, ganin ba abinda idanun shi suka gane mishi sai ya kalli Ummu da sai bayan tayi kwaroronton da kiran sunan shi ta gane ita ce fa, shi ma kuma shi ne fa, shiga yayi ban ɗakin yan faɗin "Lafiya Kulsum? Daren alhamis ɗin nan sai ihu kike min a kai, ki kasa barina nayi salati yadda ya kamata, me ya faru yanzu kuma?"

Wani mugun kallo ta watso mishi tare da niyyar ƙwalla masa harara, sai Jabir yayi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin "Wallahi Kulsum kina hararata zan sake ɗorawa kaina wani wanka a tsakiyar banɗakin nan, kuma jaraba ki gani."

Da sauri ta maida akalar duban ta wani iri tana turo baki kamar yarinya tace "To ba kaine ba..." Sai kuma tayi shiru, hakan yasa ya sake matsawa kusan ta yace "Ni ne me? Ban ishe ki ba?"

Ƙasan kafafun shi ta harara tana ayyana _"Na bi ƙaniyar da gudu."_ Sannanbta girgiza kai alamar a'a, cikin muryar kuka tace" Wallahi fitsarina da jini yake fita Jabir, kuma kaga ai ni ba yarinya bace kuma ba budurwa ba, Jabir na shiga uku wallahi, gaskiya ni tsoro nake ji."

Cike da kulawa ya gyara mata tsayuwar ta yana kallon ƙasan nata, e ƙwarai akwai alamar jini amma ba fa sosai ba, shine take cewa wai fitsarin fita yake tare da jini, cikin nutsuwa ya tallabo fuskar ta yace" To bari na miki wankan, sai muje asibiti ko? Dan kin ga wallahi bana fatan wani abu ya samu hanyar hutun nan nawa."

A gatse ta kalle shi tace" Ban gane ba? Ka manta ka min alƙawarin ba zaka sake yi ba daga yau? Kuma ni wallahi b zan je asibiti ba."

Da mamaki yace" Me ya sa?" Cikin turo baki tace" Allah kiyaye wallahi ba zan je ba."

Jinjina kai yayi yace" Shikenan, yi wanka ki fito sai na miki addu'a."

Har zai fita tace" Dan Allah ka taimaka min da ruwan zafi, wataƙila idan na zauna a ciki na ji sauƙi."

Jinjina kai yayi yace" Angama *aunty Kulsum*, gaskiya ban ji daÉ—in wannan abu da ya faru ba." Juyawa yayi ya fita ya bar ta a daddafe tana jiran ya kawo mata ruwan É—umin...

*Washe Gari*:tun Ummu tana nonnoƙewa tana nuna bata yarda da sakin jikin ta gaban Jabir ba har dai da abun ya fi ƙarfin ta ta saki jiki yake kulawa da ita, da gaske har yanzu kuma idan za ta yi fitsari sai tayi hawaye saboda masifar zafi, gashi ba yadda bai yi ba suje asibiti tun jiya ta ce sam, idan ta je ta nuna shi matsayin mijin ta? A ce ma ita ta masa fyaɗe ko? Dan haka ta ƙi yarda sai da safe ne ya siyo mata maganin da ta lissafa masa, Ibu da kuma Amoxi ta ce za ta ji sauƙi, sai dai har yanzu da rana ta hantse ba wani sauyi, hakan yasa har Jabir yayi niyyar yin sallah juma'a a gida yau saboda ai sabon aure yayi shari'a ta bashi dama, da lafiyar ta ƙalau ba zai ƙi zuwa ba, amma da ya zama duk motsi sai ta ce washhh! Sai ya bata lokacin ta kawai.

Yanzu haka da hannayen shi yake ƙidaya salatin Annabi da ya saba yi kafin ya tafi masallaci sau ɗari, bayan wanda yake yi daren juma'ar, Ummu na kwance kan kujerar da yake inda ta miƙe ƙafafun ta kan cinyoyin shi, hakan yasa har yake ɗan mamatsa mata ƙafafun nata, cikin shagwaɓa tana kallon shi tace "Wallahi bana so ina jin fitsari, amma kuma kamar da gayya sai zuwa min yake."

Kallon ta yayi ya sauke numfashi yace "Maama, zaki barni nayi salatin nan kuwa?"

Ɗan taɓe baki tayi tace "Ni kuwa me zai hana? Kamar wata arniya."

Kawar da kai tayi ba ta sake cewa komai ba, hakan yasa yace "Maama, bari na shiga cikin gida na faɗawa Hajia, wataƙila ta san maganin matsalar."

Da sauri ta tashi zaune tace "A'a a'a, Jabir ai kaga abin nan da ya faru tsakanin mu ne kawai, dan haka kar mu bari kowa ya ji."

Kallon ta yayi kawai ya kawar da kan shi, sai kuma ya ɗauie ƙafafun ta daga jikin shi yana tashi tsaye da cewa "Me za ki ci na dafa miki da kaina?"

Murmushi tayi tana sunkuyar da kan ta, hakan yasa Jabir cewa "Kulsum, ina jin ki?"

Kallon shi tayi a nutse tace "Jabir, da gaske ne abubuwan da ka faÉ—a min jiya?"

Ƙanƙance idanu yayi ya yi tsugunno na maza gaban ta ya riƙo hannun ta yace "Me yasa kika kasa yarda dani Kulsum? Duk abinda na faɗa miki abu ne da ya faru kuma yake ci gaba da faruwa, tun jiya da na shiga jikin Maamana, sannan maamana tayi bacci mai nauyi akan ƙirjina, sai duk abubuwan da nake ji suka sake ruɓanya, Kulsum, na yarda ke *ƙaddarata* ce, dan jiya bayan faruwar abinda ya sake haɗani da ke, sai na ƙudurta a zuciyata baki taɓa zma da wani ba bayan ni, ina so ke ma ki manta da rayuwar da kikayi ta baya, dan bana so ko a furuci naji hakan daga bakin ki, *ina da kishi a kan ki*, ba zan so a kirani marar adalci kuma butulu ba, nima kuma ba zan so na dinga jin wani abu mai kama da kishi da mutumin da ba dan ya sadaukar min da ke ba, to da ban san gararin da rayuwata za ta shiga ba."

Sai kuma ya miƙe daga tsugunnon ya shafa kumatun ta yace" Kin gane?"

Kamar gaula haka ta jinjina masa kai alamar e, dan haka ya sake cewa" Me zaki ci?"

Girgiza mishi kai tayi tace" Zan dafa da kaina, ba aikin ka bane shiga madafa."

Murmushi yayi shima yace" Na sani Kulsum, amma na yanzu ni nake so na dafa, saboda ai jinyar ki nake."

Wayar shi ce ta shiga kururuwa ana kira, É—auka yayi yana ganin sunan Aliyu ya furzo iska sannan ya sake duban ta yace" Ina ji Maama."

Cikin fara'a tace" Duk abinda ka iya girkawa."

Dariya yayi yace" Gatse kike min? Ko kuma ƙalubalantar na iya girki kike yi?"

A tausashe tace" Ko ɗaya, na dai baka zaɓi ne."

Jinjina kai yayi ya nufi hanyar fita yana faÉ—in" Za ki gani ko."

Saida ya fita ya É—aga kiran Aliyu, daga wajen Aliyu ne ya fara faÉ—in" Wallahi Jabir baka da mutumci, yanzu ni zan dinga kiran ka kana share ni? Shikenan dan kayi aure sai ka fara raina min wayo, ka manya gaba nake da kai ne?"

Wani irin numfashi ne Jabir ya sauke a nutse sosai yace" Toh! Da fari dai Aliyu naje na maka rashin mutumcin, aure ai ba wasa zbe da zai sa ka kasa ganin canji a jikina, maganar girma kuma ina ga yanzu haka auntyn taka ma tsoron kallona take, idan kuma aljanun ta ne suka koma kan ka, Aliyu kasan tsaf zan iya ɗaureka na maka ruƙiya, dzn ba ƙarfina kafi ba dan kawai ka fini shekaru, magana ta gaba kuma faɗa min me ya sa ka kirani? Ina wani aikin lada ne nan."

A amsakuwa Aliyu ya saka shi dan sua tare da Fahad ne dala sukayi niyyar ɓata masa rai, dan haka suke ta dariya kafin Aliyu yace" Duk naji Jabir, kuma nagde, amma ka sani kafin a min ruƙiya kai za'a fara yi wa, saboda kai ne tun jiya ka shige gida ɗaya da maaman ka kuma ka ƙi fitowa har rana tayi."

Taɓe baki Jabir yayi yana rumgume hannu yace" Ina ce dai ai uwata ce ko? To a faɗa min me zan fiya waje nayi? Bayan nan ɗin ya fi daɗin mutum ya sakata ya walala."
Chapter 157 · 0% Book details