Sashe 139
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Alhaji yayi yace" Duniya Hajia dama abinda mutanen cikin ta suka fi ƙwarewa kenan a kai? Jiya malam ya faɗa min saboda irin hakane ubngiji ya haramta yin adopté (ban san haka da hausa ba), dan kuma ya tabbatar mana da bbu gado a irin wannan tarayya, sai aka fara zartan da hakan ga Annabinmu fiyayyan halitta Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Hajia, ni daga gareni wallahi har cikin raina nake son ƙulla wannan alaƙar, ban taɓa tunanin hakan a raina ba, amma dare ɗaya sai ubngiji ya saka min hakan tare da wani irin ƙarfin guiwar tunkarar kowa game da zancen, jiya banyi bacci ba wallahil'azzem ina tunanin abubuwan nan, idan kowa ya nutsu sai ya ga dam dai abinda zai faru kenan shiyasa duk abubuwan da suka faru a bya suka faru, sannn nayi sallah raka'a biyu kan abinda na ji na saka a gabana, cikin ikon Allah sai naji nutsuwa ta sake sauko min har ma naji dole yau na zo garin nan, dan sai nake ganin kamar mutuwa za ta iya shiga tsakanina da wannan abun alkairin da na ƙudurta a raina."
Numfashi Mamie ta sauke tana kallon Alhaji Kabir tace "Sai na kasa tantancewa, shin Jabir ne ya fi dacewa da Ummu a yanzu? Ko kuma dai kai da ka fara rayuwa da ita tun asali?"
Murmushin jin daɗi Alhaji yayi ya ɗan girgiza kai yace "A yanzi shi ya fi dacewa da ita, ni daga yanzu *uba nake a gare su*, idan har komai ya tabbata, to zan karɓawa ɗana auren ta da izinin Allah."
Sabeer ne ya sake cewa "Fahad, tunda abokin ka ne, kai za sake binciko mana halayen shi da bamu sani ba, dan n..."
Kallon shi Fahad yayi ya katse shi da faɗin "Gaskiya fa tsakani da Allah zan gaya muku abinda na sani a kan Jibril, amm wallahi ya ce min ya tuba kuma kunga ni ai na jima bn zauna garin nn na lokaci ba, sai nayi tunanin da gaske hakane, amma fa gaskiya Jibril ya ɗanyi harkar mata, shaye-shaye dai ne ban sani ba dan ban taɓa gani ba."
Wata harara Sabeer ya watso mishi yace" Ka san da haka tun farko shine ka ƙyale mutane? Mu ai daga bayanan ka ne mukayi aiki, tunda kasan ba ɗan nan bane shi."
Turo baki Fahad yayi yana kawar da kai da gungunin _" Ni fa shiyasa bana son harka da Sabeer ɗin nn, shi ya cika zafin kai, yana min irin haka kuma hayaƙin kaina tashi yake."_
A zahiri kuma bai ce komai ba shi dai yana sauraren su Yaa Bilal na faɗin kawai a kira Ummu a gaya mata? Wasu kuma na a'a a ƙyale ta har da safe, sai Mamie da tana buɗar baki tace" Ni kam na san halin auntyna wallahi da kafiya, ni kam da ɗaurawa akayi daga baya mun bat haƙuri, lokacin ba yadda zata yi ai tunda an ɗaura, amma idan aka ce sai ta amince ko?..."
Sai ta jinjina kai kawai, Mama kam dariya ta fara yi tunda Mamie ta fara magana saida ta dire sannan tace" Ke da baki gama karantar ta ba kenan, ni ai ƙa'ida ne idan nace yi sau ɗayata ce a'a to sai na kusa saka hannu sannan take yin abun, idan ba haka ba ita gani take to tana babb da ita tunda ta ce a'a a bar ta mana? Kuma har yanzu haka muke da ita dan Ummu akwai wani abu wai shi taurin kai."
Dariya duk sukayi, hakan yasa nan fa suka dinga shawarta yadda zasuyi tun daga kan Jibril, zuwa ga Bban Jabir da Alhaji ya ce a bar shi zai mishi magana da safe, zuwa ita kan ta Ummu da suka ce kawai a tafi a haka har a É—aur auren ta ji daga baya saboda gudun matsala, sai kuma shi ma gogan mai gayya mai aiki wato mai taya *Abban shi kishi*, wanda yake can cike da farin cikin Abba zai dawo da Maama ya ga ta tsiyar tara maza kala kala.
*Zuwa* safiya duk wani wanda ya kamata ya ji wannan abu ya ji har da iyayen Jibril wanda Yaya Bilal ne ya faɗa musu a nutse cewa hakan ba zai yiwu ba, sun sake bincike sun gano wani abu da shi Jibril ke aikatawa wanda gaskiya su basu sami tabbacin ya daina ba, ya dai basu haƙuri da kuma yi musu fatan alkairi, ɗaya a ciki bai ga laifin su ba, inda sauran ke ganin iskanci ne mana, me y hana su ce haka tun da wuri? Sai yanzu da lokaci ya matso duka kwana huɗu ya rage? Kawai dai dan sun ga Jibril bai da abinda suka tara ne, a haka dai suka rabu suna ta kumbura fuska, sai wannan ɗayan dake ta ƙoƙarin faɗa musu Jibril fa rayuwar shi yake yi a waje, amma su idan sun gamsu su bashi nasu ƴaƴan mana tunda suna da, sai kuma suka tsaya kame-kame da faɗin ai ba wannan maganar ake yi ba yanzu. Abba Jabir zuwa su Anna duk wanda ya ji ƙumewa yake da farin ciki, sai Abban Jabir ne ma da yasan sun yi magana da Alhaji akan Kuwailat sai yake mamaki har ya tambayi Alhaji "To kuma Alhaji wanda da ɗiyar ce ka bashi, kuma ka faɗa min wannan shekarar kake so ta kammala sai ayi bikin su, ya kenan kuma yanzu?"
Dariya Alhaji yayi kamar yana gaban shi yace "Wannan ba wata matsala bane, kaga dama ai daga ni sai kai sai Allah muka yi wannan maganar, kuma nima wani abu ne da na gani a idanun Jabir ɗin ya sa nayi wannan shawarar, to amma da na nutsu sai naga nafi hango wannan abun a idanun shi game da *uwar* fiye fiye da *ƴar*, Abban Jabir, wataƙila dama Jabir tun yana matashin shi yana jin wani abu akan Ummu, idan ma ba ya jin komai a kan ta, wallahi Allah ya riga da ya rubuta wata babbar *RUBUTACCIYA* ce a tsakanin su, za ka gane haka daga ranar da ni ban san shi ba, shi ma ba da niyyar zuwa gidana ya zo ba, amma ubangiji ya ja linzamin sa har zuwa ƙofar gidana, Allah ya sa ni ɗin nan dana fara auren Ummu ni ne zan taimake shi a rayuwa har ya dogara da kan shi, a wannan gaɓar idan na ce ba zan bari haka ta faru ba, to kenan faɗa zanyi da ikon ubangiji? Ni na isa na ja da hukuncin Allah ne? Bayan abun nan faruwa yake tamkar tarihi ne ke maimata kan shi, hakan ya faru tsakanin Annabi Muhammad (SAW) da sahabin sa Zeid bin Haris da kuma Zeinab bintu Jahash, duk da nan an samu saɓani ɗan ne ya saka Annabinmu kuma aura, mutane kuma nasan abinda zasuyi magana a kai shine na ma Jabir komai amma auri tsohuwar matata, to sai me? Ni wanene? Kuma da Jabir ne ya sake ta ni na aure ta ba wanda zai yi magana saboda ni babban mutum ne ko? To dan haka ni amincewar ku nake nema da kuma tayani tanƙwara yaran nan biyu da nasan dole su wahalar da mu kafin amincewar su, na ji nutsuwa sosai game da wannan abun, ban sani ba ko shine zai iya zama silar shigata aljanna, ko dan sheɗan dake ta ƙoƙarin nuna min *ta ya Jabir da ka ma komai, kuma shine zai dawo ya saka takalmin ka*? Wani sa'ilin kuma faɗa min yake a kunne *ya yaron da ka ma riga da wando, shine zai kwanta a shinfiɗar da ka tashi*? Da na ji haka sai nayi gaggawar korar sheɗan, na tuna a duniya kuma matan Annabi Muhammad (SAW) ne kaɗai aka hana wani mummini ko sahabi ko waliyi ya aura bayan wafatin sa, Ummu kuma ba zan hanata aure ba dole ta yi ko ba yanzu ba, to fargaban shine ni tun da ƙuruciya na iya sarrafata, shin yanzu wani wanda za ta aura zai iya shanye matsalolin da na san ta dasu? Shin wanda za ta aura zai zama mai mata uzuri? Zai iya sakata farin ciki? Sannan zai iya magance mata matsalar da ta raba ni da ita? A ganina, gwara a ce har yanzu Ummu tana cikin ahalina, ba wai zaman ya kusa dani nake so ba, amma dai a ce yau wni ne da na san shi sosai take aure, da Jabir bai da nutsuwa ba zan yarda ya auri matar da na saka ba, amma yaro ne mai hankali da nutsuwa da halin manya, ba Ummu da na samu tabbacin zai iya ji da rigimar ta ba tun ranar da yake mata magana a gabana kuma a gadarance, ko Hajia *Luba* ni zan iya aura mishi saboda zan sami nutsuwa ta shine zai iya kula da larurorin da take fama da su, dan haka matsayin ka na mahaifin shi kawai ka mana addu'a."
Cike da gamsuwa Abban Jabir ya musu addu'a ya kuma ba Alhaji damar yai magana da Jabir ɗin, murmushi Alhaji yayi yace" Na faɗawa aminin sa halin da ake ciki, na kuma saka shi ya fara share mana filin yaƙin da shi." Dariya duk sukayi kafin su shiga hira irin ta raha game da Jabir din suna hango yada zai yi tun kafin su mishi maganar.
*MARAÆŠI*
Awa biyu Aliyu ya samu kammala da ɗalibai ya nufi gidan Jabir da ya faɗa masa yau ko fita bai yi ba kan shi ne ke ciwo, saida ya siya mishi abun kari da ya buƙata da magani sannan ya wuce, cike da tattalawa da kuma neman tsokana yake mishi hidima yana dariya yana faɗin "Girman ka ne ai, zan maka komai wallahi, da girman kujerar ka *tonton Jabir*."