Sashe 140
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jabir da ya dafe kan shi yana sanye da baƙa siɗik ɗin singlet da wandon shi tree quater ya ɗan ɗago da ƙyar ya kalle shi, shi fa tun damuwar jiya ce da ya kwana da ita take ta damun shi, ya yi kuka har da marin kan shi saboda maganganun da ya tuna Jibril yayi akan ta har da ma na jiyan, amma shine Aliyu ke masa wani zancen banza kuma haka? Banza yayi da shi har ya miƙo mishi farantin sistem ɗin da cokali da bred ya ɗan fara tsakura, kujerar dake fuskantar Jabir ya zauna yana ta kallon shi sai wasar baki yake.
Hakan yasa Jabir aje farantin kan teburin din dke tsakiyar su ya kalle shi murya a daƙile yace "Ya aka yi? Me kake so na yi maka Aliyu?"
Ƙara faɗaɗa murmushi Aliyu yayi cike da ƙaunar Jabir ɗin da ya ga har ya fahimci akwai abinda yake so ya mishi, gyara zama yayi yace "E to, dama fassarar wata aya nake so ka ɗan tuna min?"
Ɗaga idaun shi ya sake yi ya kalle shi da suka masa nauyi suka ƙanƙancewa, duk da yana jin kamar ba gaskiya bane, to amma bai isa ya ce ƙarya yake bai manta ba, dan mu'ijiza ce ta Alƙur'ani wanda yake rubuta shi ma ka ga ya wata aya a cikin wata sura da zaka ga yaro ma ya haddace ta a sauƙaƙe amma ta ɓace mishi ɓat, sai kawai ya sake ɗaukar farantin yace "Ina jin ka?"
Da farin ciki Aliyu da dama ya gaa shiryo maganganun shi tun jiya a peper saboda yasan mutumin nashi yasa ya fara faÉ—in "Yawwa, ina faÉ—a kana fassarawa dan Allah, a hankali a hankali yadda zan gane da kyau, idan zai yiwu malam tafsirin ayar nake so sosai."
Kallon shi kawai Jabir ke yi yana cin abincin shi sannan ya fara faÉ—in " A'uzubilahi mina shaiÉ—anir-rajim."
Yana shirin ci gaba Jabir da a daƙile yake maganar saboda ciwon da kan shi ke yi masa yace" Ina neman tsarin Allah daga sheiɗan abun jefewa."
Kallon shi Aliyu yayi sai ya fahimci kenan dai tafsirin zasuyi? To ba damuwa a je a haka, sai yace" Aramma, tafsirin aya ta talatin da bakwai nake so a cikin suratul Ahzab?"
Numfashi Jabir ya sauke tare da aje farantin nan yana maida nutsuwar shi ga Aliyu yace " _Wa iz taƙula lillaziy an'ama-Allahu alaihi_, tuna, lokacin da kake faɗawa wanda Allah ya yi wa ni'ima, *ma'ana Zeid bin Haris da Allah ya ma ni'imar shiga addinin musulunci*, wa an'amta alaihi, _kuma kai ma ka masa ni'ima_ *daga bauta ka ƴantashi ya zama ɗa*, amsik alaika zaujaka wattaƙillah, _ka riƙe matar ka, kuma ka ji tsoron Allah_, *ma'ana lokacin da Zeid ya kawo ƙarar Zeinab bintu Jahash kan tana masa ba daidai ba*, wa tukfi fi nafsika _kana ɓoye wani abu cikin ran ka_ mallahu mubdihi _kuma Allah zai bayyana shi_, wa taksha-nass; _kana tsoron zantukan mutane_ wallahu ahaƙƙu an takshahu, _Allah shi ya fi cancanta da ka ji tsoron shi_, *a ƙarƙashin tafsirin wannan ayar akwai hadisin Nana Aisha uwar muminai dake cewa da akwai wata aya da Annabi Muhammad (SAW) zai ɓoye bai ambata ba to da wannan ayar ce*, falamma ƙada Zeidu minha waɗaran _lokacin da Zeidu ya biya buƙatar shi da ita sai ya sake ta_, zawwajnakaha _sai muka aura maka ita_ li kaila yakuna alal'mu'uinina harajun fi azwaji ad'iya'ihim, _dan kada muminai su samu ƙunci a cikin auren ƴaƴan da suke mayar ƴaƴan su_, iza ƙaduu mihunna waɗarann, _idan har sun sadu dasu bayan aure_ wa kana amrullahi maf'ula _lallai al'amarin Allah abun zartarwa ne_."
Cikin nutsuwa ya sake gyara zama yace" Aliyu, daɗi ke akwai ubangiji ya ce ka yi ka aikata, ka duba wata buwaya ta Allah, Zeid ya sake ta, kuma sai aka tura shi ya nemo auren ta da kan shi, Zeid na cewa daga lokacin da Annabi y faɗi buƙatar sa ga Zeinab, wallahi sai ya ji kamar bai taɓa zaman aure da ita ba, kawai sai ya fara kallon ta a cikin jerin iyayen su muminai, wannan biyayyar ta sa sahabbai suka mana dintinkau har yau muka kasa cimmusu, lokacin da ya je ya sanar da ita rigima irin ta iyayen mu mata sai ta sa Zeinab fadin wai sai ta nemi zaɓin Allah a kai, shin Aliyu a duniya akwai wani alkairi ne bayan fiyayyen halitta? Wanda farin cikin mu duk sanadin shi ne, daga ƙarshe dai Ubangiji da kanshi ne ya ɗaura auren a sama ta bakwai kuma mala'iku ne shaida, a ganina ba wani aure da zai sa ka ji alfaharin kasancewar ka yi shi bayan wannan auren, ita kan ta Zeinab tana faɗawa matan Annabi haka lokacin da suke tsokanatar ta, kaga kenan duk yadda zaka riƙe ɗa maganar wai ɗan ka ce bata taso ba, baka da gadon shi bai da gadon ka, haka kuma zai iya sakin mata ka aura kai ma zaka iya saki ya aura, ama a yanzu wannan zamani da muke ciki idan haka ta faru za'a kira wanda yayi hkan ne da butulu, ma ci amana, koma dai menene kada zancen mutane ya damu mutum, saboda akwai misali a Alƙur'ani kuma ga shugabanmu fiyayyen halitta haka ta fara faruwa, to me zai sa kayi baƙin ciki idan haka ta so faruwa a kan ka? A zamanin nan akwai wanda yaron shi bai isa ya kalli ƴaƴan sa da sunan soyayya ba, wani kuma tunda na maka komai a rayuwa, to iyalina sun haramta gare ka daga matan har yaran, wa ye zai iya yin hali irin na magabatan mu? Ko ba irin na su sadaukarwar ba, a ƙalla dai a kwatanta yin haka."
Murmushi Aliyu yayi yace" Hakane Jabir, Allah ya ƙara mana imani da koyi da su."
" Ameen Ya Hayyu ya Qayyum." Cewar Jabir yana ɗaukar abincin shi, sai Aliyu kuma da yace" Sai dai fa a wannan ƙarnin la an samu wanda ya kwatanta irin hakan."
Yana cin abincin yayi murmushi yace" Wa ye wannan?"
Ido Aliyu ya tsura masa kafin ya furta" Abban mu ne, *Abban ka* Alhaji *Kabir Saley*, ya nema maka *auren* maaman ka Aunty Ummu."
Da ƙarfi Jabir y ci birki saboda wata muguwar ƙwarewa da yayi, a gigice ya shiga yin tari ba ƙaƙƙautawa, da ƙyar ya ɗauki ruwa ya sha sannan ya ya fara kwanta masa, saida ya ɗan nutsu ya zubawa Aliyu idanu cike sa tausayin yaushe hka ta fara faruwa da shi? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! A Saudia ya haɗu da su? Ko a Misra da suka je? Ko nan Madina ne? Dama fa an ce ana kamuwa da aljannu wajen karatun nan, amma shine basu taɓa nunawa ba sai yanzu? A hankali ya aje farantin nan ya muskuta da niyyar tashi ya ɗaure Aliyun ya msa ruƙiya, ina lafiya malam guda ba lafiya? Amma sai Aliyu ya tabbatar masa da lallai fa aljanu gare shi ta hanyar rigan shi miƙexa tsaye yace "Kana ji ko? Ka riga da ka faɗi abubuwan da suka dace a fassarar da ka min yanzu, kada kayi tunanin abinda mutane zasu faɗa, ka ji tsoron Allahn ka kawai Jabir, Abba ya ga kafi cancanta da aunty Ummu, shiyasa ya je har can yayi maganar auren ku, kuma wallahi ko baka yarda ba Jabir kana *son Maaman ka*, kayi tunani da kyau sannan ka faɗa musu matsayar ka, amma ka tuna wani abu, idan ka ƙi amincewa to auren ta zai tabbata da wanda ka tabbatar jikin ta ne kawai yake so, idan kuma ka amince to ko baku son juna nasan zaku zauna lafiya dan zaku mutumta junan ku, idan ka yi shawara ka kira ni sai na kira Abba nima na sanar da shi."
Juyawa yayi zai fita sai kuma ya dakata ya juyo ya sake kallon Jabir da yayi mutuwar zaune yana kallon Aliyu kawai da mamakin har haka abun yayi ƙamari wai? Ko dan sun jima basu kwana tare bane shiyasa har aka samu dandalin kafa shaiɗanci a jikin bawan Allahn nan? Cikin nutsuwa Aliyu yace "Ka da kace zaka kawo dalilin ƙin amincewar ka ta hanyar faɗin tsohuwar matar Abban ka ce, Jabir Abba ba Abban ka bane dan ba shi ya haife ka, ka da ka zama ɗaya daga cikin masu haramta halal saboda gudun zancen duniya, kar kuma kama kanka babban zalincin da ruhi ke wa gangar jiki, ma'ana hana zuciyar ka abinda take so, hakan zai jigatar da gangar jikin ka ƙwarai, amma zan iya yarda da dalilin ka idan ka ce ta maka *girma ne a shekaru* ko kuma saboda ta *haifi budurwa*."
Yana faÉ—a ya fice daga falon ya bar Jabir da hangen bayan shi, da sauri Jabir ya É—auki wayar shi zai kira Abba ya gaya mishi maza maza su dawo ba lafiya a gida, dan wannan haukan na Aliyu zai iya saka shi tara mutane ma a É—aura masa aure da Hajia babba wata rana, ina dalili kai jama'a? Aliyu? Shine ke wannan maganganun da bakin shi? Astagfirullah! Astagfirullah! Gashi kuma ba cikakkiyar lafiya ba bare ya tirsasashi yin istigfari shima.
*Alhamdulillah.*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*

_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes