← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 168

Sashe 163

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun jima suna hirar nan kafin Abbu ya shigo da sallama riƙe da takardu a hannun shi, wurin da ya tashi ya sake komawa ya zauna yana kallon Ummu tare da nuno ɗaya daga cikin takardun hannun shi wanda alamu ya nuna ciro su ne yayi daga cikin enveloppe dan gata ma a hannun shi yace "Ummu Kulsum, riƙe wannan..."

Ya faɗa yana miƙo mata ɗaya, miƙewa tayi a nutse ta je gaban shi sannan ta rusuna ta karɓa cikin ladabi, komawa tayi ta zauna tana sauraren Abbu da kuma kallon shi yana faɗin "Wannan takardun wata restaurant ne da Hajia da kuma Abbu Allah jiƙan shi da rahama suka baki kyautar ta tun lokacin da aka haife ki, restaurant ɗin na nan gefe da babbar asibiti mai sunan *Halal food*, tana shigo da kuɗi sosai, na san zaki zama babbar Hajia."

Duk da cikin sigar zolaya yayi maganar, kuma mutanen dake wurin sun dara, amma sai farin ciki ya sa Ummu zubo da hawaye tana sake kallon takardun da kuma Abbu ɗin, shima yana cikin dariyar ya sake miƙo mata wasu takardun da enveloppe ɗin gaba ɗaya yace" Wannan kuma ƙaramin kanfanina ne dake Niamey, a ƙarƙashin kanfanin ana sarrafa abubuwa da dama wasu kuma ana shigowa ne dasu amma da sunan kanfanin wanda yake mallakin ki ne ke da Eesha, ko ita ban faɗawa ba saboda nayi alƙawarin sai ranar da na gan ku dukan ku, ranar da aka ɗaura auren ki na so yi miki wannn kyautar, amma yadda abubuwa suka zo ya sa Allah bai nufa ba sai yanzu, ana ci gaba da kula miki da dukan su, sai dai a gobe ɗin nan zan tabbatar dake a matsayin shugaba a wannan wuraren biyu, da fatan zaki kula ki kuma yi gadon Abbun mu wajen jajircewa akan abu."

Hajia ce ta fara taya ta murna da mata addu'a sosai da fatan alkairi sannan Mama Nuriyya ma, haka ma Jabir da kusan farin cikin shi ya so fin na kowa a wurin tare da jero addu'o'in Allah yayi riƙo da hannun ta ya bata ikon iyawa, cikin jin daɗi Abbu ya kalli Jabir yace "Jabir, zan iya cewa aiki kai ya sama, ina roƙon da ka kama mata kula da wannan wurare ka tayata alkintawa."

Cikin ladabi Jabir ya amsa da "In sha Allah Abbu, Allah ya bamu ikon gudanar da su kamar yadda kukayi a baya." Da ameen suka amsa kafin su sake taɓa hira har dare yayi sannan suka fito zasu tafi.

*Alhamdulillah.*
[12/09 à 12:12] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*75*

Daf da ƙofar gida suka haɗu da Fahad tare da Jibril, shigowar Fahad ɗin kenan Jibril ya tare shi yake faɗa masa matsalar da yake ciki, tunda aka fasa auren shi da Ummu mahaifiyar shi ko gaisuwar shi bata amsawa, shine ya zo ya lallaɓa Fahad ya je gidan su ya faɗa mata ba laifin shi bane, amma ta ɗauki damuwar fasa auren ne ta ɗora laifin a kan shi saboda kawunan shi basu sanar da ita gaskiyar lamarin ba saboda sanin bata da lafiya cikakkiya.

Bai yi tsammanin zai ga ko da Ummu ba bare ita da Jabir, tunda ya gansu ya tsura musu idanu yake ta kallon su, musamman ma Jabir da yake ma kallon tsana saboda ganin wani shaƙiyin kallo da yake mishi har ɗaga girare yake yi yana wani murmushi, saida suka zo daf da su sukayi misabiha shi da Fahad dake faɗin "Aramma, har kun fito kenan? To kenan ni raina ni kayi da ba za'a je nawa ɓangaren a gaishe ni ba."

Murmushi Jabir yayi amma bai ce komai ya ya miƙawa Jibril hannu saboda bin ƙa'idar shari'a, amma idan ta shine wallahi ba zai taɓa kallo shi ba, da ƙyar Jibril ya bashi hannu suka gaisa ya na ɗan satar kallon Ummu dake magana da Fahad.

Cike da son ƙularwa Jabir ya kalli Ummu tare da zagaya hannun shi ta ƙugun ta ya shafo jigidar ta ita kuwa jigidar tayi sautin dake nuna an taɓa ta, ga jikin shi ya matsota duk da tana ta sinne kai wai ita kunya, cikin nutsuwa Jabir ya kalli fuskar ta yace "Kulsum, ki gaishe da *abokina* mana?"

Kallon Jibril É—in Ummu tayi a karon farko kenan, haÉ—e fuska tayi saboda ita ai bata san cikakken abinda ya faru ba, za ta yi magana sai kuma Jabir yace "Ko da yake, barshi ma kawai, kin san muryar ki *sirrina ce*."

Sai kuma ya saketa tare da kallon ta yace "Je ki ina zuwa."

Jinjina kai tayi a ladabce sannan ta fara takawa, tuni Jabir ya maida hankalin shi kan Jibril yana so ya ga abinda zai saka shi huce haushin shi akan shi, Jibril kuma da bai san target ɗin Jabir akan shi ba sai kuwa ya bi bayan Ummu da kallo har ma da shagala da mantawa da yana tare da wasu... A wani gadarance cike da jarumta da tafasar zuciya Jabir ya shaƙo wuyan rigar Jibril da duka hannaye biyu ya dawo da kallon Jibril ɗin zuwa fuskar shi, a kausashe yake kallon shi cikin kaushin murya Jabir da har jijjiga Jibril ɗin yake yace "Ya zama na ƙarshe a rayuwar ka da zaka sake raka matata da waɗannan ƙazaman idanun naka, kayi kuskure a rayuwar ka Jibril, da ka bari na san abinda yake ranka game da *macen da nafi so* a faɗin duniyar nan, wannan zaren kuma da kake burin ganin kalar shi har ma ka taɓa, ka sani ya maka nisa saboda yanzu ya zama *abu ma fi daraja* a gare ni, ni kaɗai ne yanzu nake da dama a kan ta fiye da kowa, idan baka daina kallon ta da wannan gurɓatacciyar aƙidar taka ba, shakka babu zaka *rasa idanun ka*, kuma ka rubuta ka ajiye dan zan aikata maka hakan ba tare da nadama ko dana sani ba."

A wani tsiyace ya tunkuÉ—a shi baya sannan ya kalli Fahad dake kallon su wallahi kamar yau ya fara ganin su, ba maganganun Jabir bane suka fi É—aukar hankalin shi kamar yadda ya aniya jijjiga Jibril ka rantse yana gaba da shi, murmushi ya ma Fahad yace" Sai gobe, zamuyi magana."

Bai ko sake duban Jibril ba ya wuce zuwa hanyar fita, cike da takaici da baƙin ciki da kuma nadamar rayuwa Jibril ya bishi da idanu, a ce lalacewar shi ta kai har wannan yaron yna masa haka akan matar shi? Gyara wuyan rigar shi yayi ya ɗanyi gyaran murya sannan ya juya a fusace ko sallama bai ma Fahad ba ya wuce, jinjina kai Fahad yayi yana mamakin dama haka Jabir yake? Kai shiyasa aka ce idan ka ga lafiya to saka mata ƙota, yanzu ɗan Jabir ɗin nan ne ke da wannan masifa haka? Da wannan mamaki ya shiga cikin gida, duk da ya samu Nabila na ta fama da laulayi, ama dake ta kula shi sai ya dinga bata labarin abinda ya faru.

*WASHE GARI*

Dake asibitin kuɗi za su je a nutse saida suka gama ziyarar su daga gidan su Mammie zuwa gidan su Anna, ko ina tarba suka sami tare da yi musu nasiha da su zauna lafiya, sai Hajia Mamie da ta mata tsarabar lallen hausa mai yawa da mahallabiya da miski fari da ja dan kowane da anfanin shi, sannan ta haɗa mata da sahihin iccen magarya da kuma iccen dukkhan, Ummu dai karɓa tayi tana mamakin Hajia Mammie ɗin, kafin ta ranƙwasheta a kai ta murɗe mata kunne tana faɗin "Saura idan kun je can ɗin ki zubar min da abu ɗaya a cikin kayan nan, wallahi da akan uwar ki Nuriyya zan huce, sannan ki ci gaba da kama jikin ki da kuma kula da mijin ki, ubangiji ne ya wanke ya baki dan haka ki kula, kinga dai yana ganiyar ƙuruciyar shi ne, sannan ya san falalar dake cikin ƙara aure, wallahi duk ta inda kka gaza sai dai kiji ana miki buɗa a cikin gida, dan irin su Jabir ba zasu juri ɓacin rai da horon wahala a gurin mace ba kullum, sannan kinga lallen nan? Nasan kin iya anfani da shi ta hanyoyi da dama, daga kan gyaran fata, gyaran farji, rigakafin ciwon ƙafafu, rigakafin sanyin dake shiga ta ƙafafu, sannan kuma ado ne, haka kuma wannan kan naki mai yalwar gashi ki dinga kulawa da shi, kin ji ni?"

Jinjina kai Ummu tayi tana son ta sakar mata kunne tace" Naji Mammie, zan yi in sha Allah."
Chapter 163 · 0% Book details