← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 168

Sashe 40

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan yasa shi miƙewa yana duba ƙofar dan ya ga me ke faruwa, Aisha ma cikin sanɗa ta dinga bin bayan shi har ta fito tsakiyar berandar Hajia. *Bayan* motar dake jiniya wasu jibga jibgan motoci guda uku suka take mata baya, dake akwai wajen ajiye motoci kuma ko Sa'ad da ya shigo waje ya baro ta shi motar, hakan yasa motocin suka layu wata na bin wata, masu tuƙin motar ne suka fara fitowa suna buɗe ƙofofin baya, cikin nutsuwa da dattako mutanen ciki ke fitowa... *Sa'ad* yana sauke idanun shi akan dattijon da fuskar shi ba ɓoyayya ba ce ko a telebijin saboda muƙaman da ya taka wato *Saheeb Ahlan* ya sa shi rarako idanu ya ji gaban shi ya faɗi, a take kuma ya juyo inda ya san ya baro Aisha, amma sai ya ganta à farfajiya ita ma tana kallon mutanen da mamakin su kuma su waye? Wane irin zuwa ne wannan kusan magariba haka? Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tarie da lumshe idanu ya ayyana _"Shikenan, yau zan rabu da ita."_

Alhaji Ibrahim ma a tunanin shi ko baƙi yayi haka da babu sanarwa, bai jima da dawowa gidan ba yana shirin shiga wanka sai kawai ya fasa ya fito, ai kuwa ganin dattijon da shi kan shi ya san shi amma fa a telebijin sai ya sukwano da sauri ya nufo su da kuma mamakin jin ta yiwu ɓatan kai sukayi, amma a fara gaisawa kafin su san me yake tafe da su.

Kafatanin ahalin gidan ne a tafe dan kawai su gasgata abinda aka faÉ—a musu cewa an samu Eesha a wannan gidan, shin da gaske? Eesha dai ta su? Kamar zai yi ruku'i a gaban Alhaji Saheeb haka Alhaji Ibrahim ya rusuna yana gaishe shi da mishi sannu da zuwa, saida ya gama mishi sannu da zuwa sannan sukayi musabiha da su Yaya Bilal da Abbu Mukhtar har ma da Sabeer, nuni ya musu da hanyar shiga ciki yana faÉ—in "Bismillah, ku shigo ciki."

Cike da dattako Alhaji Saheeb yayi murmushi yace "A'a ka bar shi, na san ai kana mamakin ganin mu warhaka gidan ka, hakane?"

Da ladabi Alhaji yace "Gaskiya ne Alhaji, ina fata dai lafiya? Dan nafi tunanin ko ɓatan kai kuka yi."

Dariya yayi cikin nutsuwa yace "Ko kaɗan, ba ɓatan kai muka yi ba, shasalima tare muke da waɗanda suka kawo mu nan."

Jinjina kai yayi da gamsuwa yace "Ma sha Allah, to mu shiga ciki sai mu tattauna ko?"

Ƙara dakatar da shi yayi da cewa "A'a fa, ba sai mun shiga ba, dama mun zo ne akan wata muhimmiyar magana, nema muka zo, dan haka idan bamu samu abinda muka zo nema ba zamu yi wani wajen ne dan ci gaba da nema."

Da mamakin furucin dattijon ya É—an kalle shi na sakanni sannan ya rusuna yace" To Alhaji, zanyi fata a ce kun samu abinda kuka zo nema a nan É—in, farin cikina ne hakan."

Gyara tsayuwa Alhajin yayi ya kalli Hajia Radiya dake kusan shi sannan ya kalli Alhaji yace "Wani bayani aka bamu kan cewa *Eesha tana gidan nan*."

Da wani sabon mamaki Alhaji Ibrahim ya kalle su dukansu sannan ya maimaita kalmar "Eesha?"

A tsanake Alhajin ya jinjina mishi kai alamar e, girgiza kai yayi da yanayin rashin sani yace "Kuma a gidan nan Alhaji?"

Kafin wani cikin su ya bashi amsa Hajia ta fito daga ɓangaren su Mama da ta shiga duba jikin Sauban dan yau suka dawo daga asibiti, hangen su tsatsaye kamar ba lafiya ba ga tarin mutanen da alamun su ya nuna mata manyan mutane ne yasa ta nufowa wurin dan ta ga ɗanta tare da su, tana zuwa cike da dattijantaka tayi sallama suka amsa sannan suka gaisa, kallon Alhaji Ibrahim kawi tayi ya fahimci kallon nata, cikin nutsuwa da ladabi yace "Hajia, wata suke nema wai Eesha, shine ban gane ba."

Murmushi Alhaji yayi yace "Ina ga zaku fi fahimta idan kuka ji daga bakin wannan..." Y faÉ—a yana É—an juyawa bayan shi, hakan yasa wani jami'i da suke tare da su dan kare lafiyar su y jinjina kai alamar fahimta tare da juyawa da sauri ya fita waje... Jim kaÉ—an sai ga shi tare da DG wanfa yayi shiga cikin manyan kaya har da hula.

Sa'ad na ganin shi kuma saida ya kalli Sa'ad É—in dake nesa da su ya mishi wani bahagon murmushi sannan ya ci gaba da tafiya, da sauri Sa'ad ya tunkare su gadan gadan tare da kallon Aisha da har lokacin take tsaye yace "Maza shiga ciki."

Ba tare da saɓa umarnin shi ba ta juya za ta shiga, sai kuma ta ɗan yi jim tare da tsayawa tana ƙara gyara tsayuwar ta da leƙa bishiyar mangoron da take ɓoye mata fuskar wani matashin dattijo da ta so ganin wani abu a tare da shi...

Take bakin ta ya buɗe, idanun ta suka firfito waje, gabata ya yanke ya faɗi haka ma jikin ta ya ɗauki rawa, ba tare da Sanin tana saɓa umarnin Sa'ad ba ta shiga takowa a hankali kamar wacce ƙafafun ta ke mata ciwo. DG na ganin Aisha na tahowa da sauri ya nuna musu it da yatsa a gigice yace "Yawwa gata can, ita ce waccen, wallahi ita ce."

Cak! Ta tsaya inda tsoro ya mamaye ta ganin ana nunota kuma kafatanin kowa ya kalle ta... Raɓa tsakanin Mukhtar da Abida Nuriyya tayi tana baza idanu sosai tana ƙara kallon ainahin kamar *mijin ta Mukhtar* akan ƴar tasu, abu ɗaya da ya bambamta Aisha da mahaifin ta shine idanu ta fi shi kasancewar ta mace kuma irin idanun nan ne masu charme, haka kawai halittar take.

Sannu sannu take tunkaro Aisha har ta zo kusan ta, haka shi ma Abbu Mukhtar bayan ta ya biyo yana kallon kamaninshi a fuskar yarinyar, tana zuwa ta tsaya gaban ta da fuskar alhini da kuma hawaye dake kwaranya a idanun ta, hannu ta kai ta shafi kumcin Aisha tana murmushi tace "Eesha, ke ce kika girma haka?"

Aisha dai mamaki ne a fuskar ta da son sanin me ke faruwa da ita ne da take jin kamar tana ƙaunar mutanen nan har ma da musu *haukan so*? Musamman wannan matar da taji wani abu da zata iya cewa da *jinin jikin ta ne* ke fizgar ta zuwa ga matar da son ta rumgume ta, Mukhtar ma na zuwa tallabo haɓarta yayi ya ƙurawa fuskar ta idanu, sai kawai wasu hawaye suka kwaranyo mishi, da mugun ƙarfi ya jawo Aisha jikin shi ya rumgume kamar za'a ƙwace mishi ita.

Liƙe idanu Aisha tayi gam gam saboda matsar da yake mata ba kaɗan bace, suna haka Aisha cikin sanyayyar murya tace " *Abbu* na kasa numfashi."

Dariya ce ta kubce mishi tare da É—an sassauta mata sannan ya raba jikin shi da nata, kallon fuskar ta yayi yace "Kenan kema kinsan ni ne Abbun ki?"

Rarraba idanu ta fara yi, dan ita fa ta faɗi hakane saboda ai babba ne ba zata kira shi da kawu ba, kafin ta ce wani abu Mama Nuriyya ta sa hannaye biyu ta juyo da Aisha zuwa duban ta tana faɗin "Ƴar mu ce mana, wannan Eeshar mu ce, gashi ma kana gani..."

Sai kuma ta raunana kallon ta wasu sababbin hawaye na zubo mata tace "Eesha, Eesha..."

Sai kawai ta ruƙumƙume Aisha tana rera kuka kamar ranta zai fita tana ma Aisha wata matsa kamar za ta mayar da ita cikin ciki, shi ma Abbu Mukhtar ɗin haka ya saka su jikin shi dukansu ya ƙwaƙume suna ta kukan farin ciki...

Matsowa su Alhaji duk sukayi suna kallon su cike da tausayawa, inda Fa'iza ta kalli Abida da ita ma take kallon ta cike da tsana da takaici, dan suna zaune kawai ta ce wani ya kira ya ce an samu labarin Eesha, kuma ta hana su shaƙat ta ce a taho da gaggawa, Sam bata bata wata dama ta aiwatar da wani abun ba, yanzu haka hankalin ta a tashe yake, bata san me ye shirin Fa'iza a kan ta ba, idan fa niyyar ta tona mata asiri ne? Ai da ta sakata a damuwa babba kuwa, musamman ma yanzu da ta fara jin canji a jikin ta har take jin za ta je asibiti a duba ta, idan aka yi sa'a ciki ne da ita shikenan fa ita. Wani shu'umin murmushi Fa'iza ta mata, burin ta ita dama aga yaran, bata so ta tonawa Abida asiri yanzu da wuri haka har sai ta ga inda gudun ruwanta zai tsaya, dan take-taken Abida da wasu abubuwa da take gani, da kuma ganin matashin yaron nan har sau biyu a gidan su, jikin ta ya bata akwai abinda take shiryawa, dan haka zata zuba mata ido ta ga me take son isarwa, ta fi so ta mata *kamun kazar kuku*.

Mamaki ne yasa Hajia Kaka dake kallon wannan al'ajabi tace "Wai kun san Aisha ne?"

Hajia Radiya dake ta murmushi tana kallon Aisha ne ta kalle ta tace "Hajia, wannan yarinyar ina kyautata zaton Eeshar mu ce."

Da sauri Mama Nuriyya ta kalli Hajia Radiya tace "Mamie, ita ce, wallahi Eesha ce, da ita zamu tafi yanzu, ba zan bari ta sake suɓuce min ba."

Kamar suɓutar baki Sa'ad dak daf da Alhaji Ibrahim ya kalli Aisha jin an ce za'a tafi da ita yace "A'a, ba zaku tafi da it...."

Sai kuma yayi gaggawar yin shiru saboda kallon shi da jama'an gurin sukayi, a hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya runtse idanu, Yaya Bilal ne ya nuna Sa'ad ɗin da yatsa yace "Wanene wannan?"

Alhaji Ibrahim da ya ji kunyar abinda Sa'ad É—in ya yi a sanyaye yace "ÆŠana ne, shine ya taimaka mata ya kawo ta nan gidan."

Jinjina kai Bilal ɗin yayi ya matso kusan shi ya miƙo mishi hannu yace "Kayi ƙoƙari ƙanena, ka kyauta mana sosai."

Da ƙyar Sa'ad ya miƙa mishi hannu suka gaisa, Alhaji Ibrahim ne ya kalli Aisha dake kwanc kan ƙirjin Mama Nuriyya ta hana ta motsawa yace "Aisha, ashe ke ƴar babban gida ce?"
Chapter 40 · 0% Book details