← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 168

Sashe 17

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saƙe tayi tare da ƙura masa idanu har da sakin baki alamar dai mamaki ƙarara, ƙwarai ta gane me yake nufi ta wani ɓangaren, amma ta wata kusurwar sam bata fahimta ba, shi da abokan shi? To su nawa? Ita sai ta kwana a ina? Tana mace su suna maza? Kuma yana ganin hakan ya dace? A hankali ta fara jin tsoron shi yana kamata, dan haka ta yunƙura da sauri ta miƙe tana kakkaɓe siket ɗin ta a baya tace "A'a ka bar shi, nagode sosai."

Hanya ta kama za ta raɓashi ta wuce, da sauri ya miƙe tare da riƙe babban kallabinta data rufe jikin ta da shi yana faɗin "To shikenan na gane, yanzu faɗa min nawa ne farashin?"

Juyowa tayi da mamaki ta sake kallon shi tace "Farashin me?"

Ba tare da fargaba ba ko kunya yace "Ina nufin farashinki?"

Sosai ya sake durmiyata tunani, ba ta san me yake nufi da farashinta ba gaskiya, dan haka ta zuba masa idanu kawai tana kallon shi, shi ma kallon fuskar ta yake yi musamman ma idanunta da shi suka fi mishi kama da na wacce ta sha babban abu mai bugarwa irin su giya haka, idan ko ba wani abu ta sha ba to tabbas gogaggiyar ƴan bariki ce dake fara jan hankalin abokin harƙalla da idanunta, sai kuma gashin dake kwance gaban goshinta, shi dai idan zai bata suna sai ya ce da ita *baƙar buzuwa*, dan duk da fatar ta mai duhu ce tana da kyau da kuma alamar yalwar gashi.

Da son nuna mata ƙwarewar shi a harkar nan ya sake cewa "To kinga? Ki faɗa min nawa zan biyaki a kowane kwana ɗaya? Sannan abokaina ma zaki iya samun wanda zai yaba, kinga kenan kin ƙara samun kasuwa ta dalilina."

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Aisha ta faɗa tana fizge kallabinta tare da ja baya, hawaye ne suka fara gangaro mata a kumatu tasa hannu ta share da mugun sauri ta raɓashi ta wuce ba tare da ta ce masa ci kanka ba, da kallo ya bita shi ma dan ba zai iya bin bayanta ba dan ta nufi hanyar titi ne dake da mutane, ƙugunta mai dirin kwalbar koka cola ya dinga bi da kallo da jin takaicin rasa ta da ya yi.

*******************

Bai taɓa sanin ya iya murmushin nan da ake cewa malalacin murmushi ba sai yau kuma yanzu ya tabbatar bayan jin wani zance daga wajen mahaifin nashi, ba tare da ya daina murmushin nan ba ya kalli mahaifin nashi da matsakaitan idanun nashi tare da kai yatsar shi yana shafa girar shi cr ɓaren daman shi wanda hakan ɗabi'ar sa ce, bai ce da shi ƙala ba har saida ran mahaifin nashi ya sake ɓacewa ya gyara tsayuwar shi yace "Da Kai fa nake magana *Sa'ad* ka min shiru? Ka san dai ba ƙarya za'a maka ba ko, idan har ka san kana sana'ar da bata dace ba ka daina tun wuri, dan ikona bai isa ya hana ka fuskanci hukunci ba idan har aka kamaka da laifi."

Tsaf! Take ya haɗiye wannan murmushi da yake yi tare da gyara tashi tsayuwar shi ma yana fuskantar shi, duk da ran shi ya ɓace ne kuma martani ne yake son mayarwa, amma ɗabi'arsa ce sanyin murya ta yadda wanda bai san shi sosai ba zai yi gardama idan aka ce maka Sa'ad na faɗa ko hargagi, cikin tattausan muryar shi mai sanyin da bata da maraba da ta wata macen yace faɗin "Iko? Iko gareka dama? To ai dama ban ce ina son taimakon ka ba? Idan an kamani dan Allah kar ka nuna ka sanni, *Ibu* (Ibrahim, sunan mahaifin nashi) na ɗauka duk sana'ar da na fara kai ne sila, to me ye kuma yanzu na tsare ni kana min wannan maganganun? Ko ka manta lokacin da duk na roƙeka hatta da abun goge baki sai ka min gorin rashin sana'a? Zan zauna ne talauci ya kasheni?"

Gemunshi da ba yawa gare shi ba illa kewaye bakin shi da ya yi zuwa kumatu ya shafa sannan ya ci gaba da faɗin" Idan an kamani kar ka nuna musu ka sanni, ni zan yi ƙoƙari na fito da kaina, idan kuma matan ka ne suka zugoka a kaina to ka faɗa musu wallahi su fita a harkata, idan ba haka ba zan musu ba daɗi."

Wayoyin shi dake saman gajerar katangar dake ɗauke da kullaye masu shukoki ya ɗauka babba da ƙarama tare da raɓawa zai wuce dan ɓangaren ƙofa ɗaya ce ta shigowa kuma dole sai ya bi ta gaban mahaifin nashi zai iya fita, hakan yasa Alhaji *Ibrahim* ɗin ya riƙe damtsen shi dake ɗaure tamau cikin matsatsiyar rigar shi mai dogon hannu ta kayan motsa jiki, dakatawa yayi sukayi ido huɗu da sauri kuma ya kawar da kanshi yace "Zan fita."

A hassale Alhajin yace "Me kake nufi kenan Sa'ad? Ka fi ƙarfin a faɗa maka gaskiya? Duk abinda zai same ka dole ne ya shafe ni tunda ni na haifeka, sannan matana da kake magana ka daina saka su a ciki dan basu san komai ba, na faɗa maka aminina ya gaya min abinda ake zarginka da shi, sun kuma tabbatar min idan har gaskiya ne za su hukunta ka daidai da kowa."

Juyowa ya sake yi yana kallon fuskar shi, kamar ma karanta wani abu a fuskar shi sai kuma ya kalli hannun Baban nashi dake riƙe da damtsen shi ya furta" Hannuna?"

A hankali Alhaji Ibrahim ya janye hannun shi daga na Sa'ad ɗin yana ƙara gyara tsayuwar shi, Sa'ad na takawa ɗaya biyu ya sake cewa" Ban gama magana da kai ba."

A ƙufule ya dakata tare da juyowa ya zuba masa idanu kamar zai fashe da kuka yace" Wai me yasa kake son takura min? Za ka je harkokin ka har kayi wata biyar ko shida ba kya ƙasar nan, amma ranar da duk ka zo ta kaina kake farawa."

Cikin É—aga murya Alhaji Ibrahim yace" Yes, dole ne na fara ta kanka."

"Saboda...?" Sa'ad ya tambaya cike da izgilanci, a take Alhaji Ibrahim yace "Saboda kai ne É—a namiji babba a gidan nan, dan haka dole zan saka maka ido."

A nutse ya saki wani murmushi tare da takowa ya tsaya gabanshi yace "Ibu, kana da abun dariya wallahi, to ina jinka? Me kuma na sake yi?"

A tausashe kamar mai tsoron faÉ—in abinda ke bakin shi Alhajin ya ce "A cikin gida ne, sun faÉ—a min har yanzu ba ka daina kawo musu mata ba, bana so Sa'ad, bana son ka na kawo min mata cikin gida."

A hankali ya girgiza kai tare da É—aga girar sa É—aya yace "Rayuwata ce fa..."

A ƙfule Alhaji ya katse shi da cewa "Ni kuma gidana ne nan, dan haka nace bana so ka sake kawo min mata a ciki, na gaya maka..." Ya ƙarashe da nuna shi da yatsa, murmushi Sa'ad ya yi tare da ɗaga kafaɗu yace "Me kake ci na baka na zuba Ibu? Bai fi kwana ƙalilan ba na kammala ginin gidana ba nima, ina kammalawa sakan ba zan sake yi a cikin gidan ka ba, kuma idan na tafi na tafi kenan sai ranar da ka neme ni."

Yana gama faɗa ya juya a hassale ya nufi inda ƙofar fita take yana ta ƙoƙarin saƙala abun sauraro a kunnen shi saboda ya saba in dai zai fita gudun nan na yamma sai ya saka abun sauraro yadda hayaniyar ababen hawa bata damun shi.

Da kallo Ahaji Ibrahim ya bishi har ya fita daga gidan, ajiyar zuciya ya sauke tare da fara takawa zuwa nashi ɓangaren, bai san yaushe za su shirya da ɗan nashi ba? Bai san yaushe zai fara masa kallon uba ba? Shi da mahaifiyar sa ma bata gidan nan saim ya ce ko dai matanshi ne suka shiga tsakaninsu, abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya san yana da laifi tun farko shi ma, amma me yasa Sa'ad ba zai gane ya fahimci kuskurenshi ba kuma yana so su sulhunta? Me yasa ba zai sake bashi wata damar ba su fahimci junansu? Amma matsayin shi na babba ɗa kuma namiji a ce haka na faruwa tsakanin su? Ai Sam bai dace ba, idan ya faɗi ya rasu wa ye zai kula da gidan nan? Gashi ƙannai gare shi masu tasowa da masu wayo, komai da yake ai suna kallo kuma wasu za s iya koya daga gare shi, dan an ce daga n'a gaba ake gane zurfin ruwa, hatta sunan da yake kiran shi da shi Ibu sai da Mujahid ya fara kiran shi haka mamanshi dai tayi gaggawar dakatar da abun. Amma haka Sa'ad yake kallon shi gatsau yana kiransa da Ibu, sunan da tun da ƙuruciya ne ake faɗa masa shi.

Yana shiga tunkarar ɓangaren shi ya fara jiyo hayaniyar da ta saka shi girgiza kai yana ambaton "Uhum ! Na dawo ba, na zo garin ba."

Ba tare da wani sassarfa ba ya ci gaba da takawa har ya hango matan na shi su uku tare da tsohuwar mahaifiyar shi da alamu ya nuna rabon rigimar take amma abun ya ci ƙarfin ta, saida ya ƙara matsawa kusa da su ya fara fahimtar akan me ake faɗan kuma wacece silar tayar da rigimar.

Isowar shi daidai da Hajia Uwani dake ta cira tana kumfar baki kamar za ta daki Hajia Zarah duk da kuwa shekarun ta da ma kasancewar ta matar shi ta farko, amma faɗi take "Da kunnuwana na ji ki ai kina masa gulmar Sa'ad, shikenan yaro kamar ba gidan ubansa ba, ku da yaran ku sai kuyi abinda kuke so, amma shi da yayi sai ya zama laifi, burinku kullum shine ku ga shi da ubansa ba sa ga maciji, to na gaji da munafurcinku, wallahi aka kuma sa min yaro gaba sai na ci uban kowa a gidan nan, idan ya so a koreni tunda ni da ɗana ai ba ƙaunarmu ake ba dama."
Chapter 17 · 0% Book details