← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 168

Sashe 127

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kallo ya ma Aliyu mai kama da harara sannan ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya fito ya saka takalmin shi, ɗakin da matashin nan ke kwana ya buɗe dan ya san akwai faranti ko da guda ne, sai yayi sa'ar samo biyu manya kuma wanda ya san ya fi ƙarfin cin abincin mutum biyu ma, juyowa yayi zai fito kawai ya ji wata magana da ta tayar masa da hankali, Jibril ne da Yusuf tsaye ƙofar ɗakin suna hira, wanda tsabar buƙatuwa zuwa ga Ummu da ɗaukar hankali ta sa Jibril kasa haƙura ya jawo Yusuf yake mishi maganar.

Tamkar wanda ya shekara bai sha ruwa ba kuma ya gansu kusa da shi yake faÉ—in "Wallahi Yusuf nake gaya yarinyar nan haukacewa nake idan na ganta, wata irin sha'awar ta ce ke damuna, tunda na zo garin nan fa na kasa kallon kowace mace bare ma na É—an rage zafi, ita kawai nake gani a idanuna, sannan hancina wannan turaren nata yake jiyo min kowane lokaci, uwa uba kuma... Ya Allah, wayyo... Ahhhhhh!"

Yusuf da ya san waye Jibril kallon shi yayi yace" Uwa uba kuma me? Jibril naga wannan ai kamar ba kalar kayan ka bace, sannan ka dube ta da kyau ai ba yarinya bace."

Saida ya lashe leɓen shi da ya fara bushe mishi tsabar jaraba yana wani gyara tsayuwa har da ɗan riƙe hantsa yace" *Jigidar ta*, wallahi sautin ta ke mugun tayar min da hankali, wannan cacas cacass... Wow! Wallahi tsigar jikina har tashi take yi, matar nan, na san ba kalata ba ce, amma kana ganin ta kasan t..."

Tsabar tashin hankali ne ya sa Jabir sakin farantin hannayen shi da ya ɗauko yana duba su, bai san idanun shi sunyi ja ba saboda ɓcin rai da tashin hankali saida ya fito yana kallon su Yusuf ya ga kowanen su da yanayin mamaki a fuskar shi, bai san duk abinda yake ji wasa bane game da Maama sai yanzu da yake jin wannan maganganun ɓatan cin a kan ta daga bakin yaro kamar wannan da bai wuce tsarar su ba ko ya ce sun girme shi da shekara biyu zuwa uku. Kallon fuskar Jibril yake da kyau da son gano kamar dukan da ya kamata ya ma fuskar shi wanda zai zubo da haƙoran shi waje, amma kuma... Ba haka Allah ya ce ba, sannan bai da dalilin fara dukan nashi tunda ba shi ya halicce shi ba.

Dan haka ya gyara tsayuwa yana sake sauke numfashin da yasan idan bai fara sauke shi ba za'a samu matsala wajen fitowar amon muryar tashi, a ɗan rikice muryar shi har rawa take ya fara faɗin "Wataƙila za ka ji na shiga rayuwar ka, amma maganganun nan da kake faɗa akan mace da ubangiji ya halicce ta da daraja basu dace ba, kai musulmi ne, nasan kuma kasan aikata alfasha haramun ne, wani aikin ba sai mun aikata ba ubangiji yake bamu ladar sa ko ya rubuta mana zunubin shi, iya niyyar mu ta wadatar ta kaimi ga halaka, abubuwan nan da kake faɗa niyya ce da ka gama ɗaurata a zuciyar ka sannan kake furtawa a baki, tun kafin aje ko ina bakin ka zai bayar da shaida akan abinda ke zuciyar ka, da a ce mala'ikan mutuwa zai ɗauki ran ka a nan inda kake tsaye, za ka tafi ne da niyyar aikata babban laifin zina, bayan haka abokina, ita mace ce da ta killace kan ta take kuma mutumta kan ta, ka darajta ta ko dan kasancewar ta mace mana, dan nasan idan ƴar uwar ka ce aka ma haka ko ƴar ka ba zaka ji daɗi ba."

ÆŠan tsaki Jabir ya ja tare da juyawa zai bar su, kai shi har farantin ya fasa kawowa su zo su É—auka da kan su, aikin banza kawai! To amma sai ya gano ashe dai da rabon ya huce takaicin shi inda ya dace ne madadin wanda bai san hawa ba bai san sauka ba, tunda gashi Jibril ya tari gaban shi cikin zafin kai na matasan da basu san kunya ba cikin kaushin murya yace "Kai a wa malam da zaka nemi shiga abinda bai shafe ka? Akan me zaka dinga haÉ—a Æ´an uwana ko Æ´ata da wannan maganar da ni kawai ta shafa? Wa ye kai ? Ina ce tunda muka zo nan bayan gaisuwa ko kallon inda kake bana yi, to me zai sa ka shiga harka ta?"

Da fa irin tashen balagar nan da son wayance abun kunyar da ya aikata ya ɗora yatsar shi a ƙirjin Jabir yana daddagawa da cewa" Dan Fahad ka zo nan nima haka, kar ka shiga rayuwata kamar yadda taka bata dame ni, dan h..."

Ba tare da ya gama faɗa ba Jabir da shi ba wai abinda yake mishi bane yanzu ke ƙona masa rai kamar kalaman da ya faɗa akan Maama, Wa'iyazubillah! Har yana jin sautin abar nan kenan shima? To wai shi wannan abar me ye anfanin ta ne fisabilillah? A cireta mana a huta, amma mata da neman jaraba kala kala, duk hanyar da za'a kasa zaman lafiya sun san ta, gashi shima wannan yana jin sautin abar nan har yana faɗawa wani kuma, ya salam ! Ya salam ! Shi kam ana ɗaura masa aure sa Kuwailat ai umarni na farko shine ta cire wannan jarabar daga kumkumin ya gaskiya, dan baya son tashin hankali a rayuwa wallahi.

A ɗan zafafe ne Jabir ya sa hannu ya tura Jibril da nufin ya ɗauke yatsan shi daga kan shi, kamar da wasa Jibril sai ya ji wannan hankaɗa da Jabir ya masa tamkar shirya ta yayi dama sai ko ya zube ƙasa daɓas saboda rashin sanin hakan zai iya faruwa da shi a lokacin. Sh kan shi Jabir bai yi tsammanin zai faɗi ba, amma kuma da ya ga Jibril na kiciniyar tashi a haukace da nufin a shaƙo Jabir ya buga shi ga ƙasa, dan ai gaba ɗaya suffar Jabir irin ta masu laushin nan ce dan halittar shi ma a tausashe take da tattausar tsokaci da ke rufe da tattausar fata.

Amma iko na ka Allah sai Jabir ya sunkuyo kan Jibril tare da sake saka hannu ya mayar da shi zaune daɓas tare da ɗaga murya a tsawace kuma a kausashe ya furta "...

*Alhamdulillah.*

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*60*

Da É—aga murua a tsawace kuma a kausashe har da nuna Jibril da yatsa yace "Ka zauna a wurin nan malam, ban ce ka tashi ba magana nake maka."

Sai kuma ya nuna kanshi yana ci gaba da faɗin "Babu daɗi ne irin haka ni kake suffanta *tawa uwar* da duk banzayen kalaman da suka fito daga bakin ka? Kaga ban san ka ba nima, kuma ban so sanin ka ba duk zaman nan da mukayi, kai ka fara *shiga rayuwata* saboda ka *taɓo abu mafi mahimmanci a rayuwata* da ni a wurina *tafi komai*, ta ya kyi wautar tunanin zan iya yin shiru bayan kana aibatata? Bari kaji malam, nasiha kawai na maka saboda haƙƙi ne da yake kaina a kan ka wanda ubangiji ne ya ɗora min ba yadda zan yi, *ka ɗauke idanun ka a kan ga*, idan ba haka ba *komai nake jin zan iya aikatawa a kan ta*. "

Ɗagowa yayi daga sunkuyarwa da yayi tare da raɓa Jibril zai fita, a matuƙar haukace Jibril ya miƙe tsaye dan kuwa har Aliyu da wasu biyu daga ciki da suka ga abinda ya faru sun fito suna tsaye suna kallon su, wannan ya sa Jibril cin alwashi har ya bi Jabir da kallo yace "Ita a wa ɗin ka? *Budurwa*? Ko *ƙanwa*?"

Cak! Jabir ya tsaya ya lumshe idanu, wani nauyayyen numfashi ya sauke yana so ya saita nutsuwar sa, a saiɓance ya juyo ya zuba idanun shi da har yanzu jajir suke akan Jibril, a wani irin daƙile yace " *Maamana ce*."

Wani shaƙiyin murmushi Jibril yayi na jin daɗi sannan yace "Da kyau, to ka ji da kyau, wannan abun da ka min ya sa na ci buri akan Maaman ka, kuma burina zai cika ko ta wace hanya, kai baka san waye ni ba, amma ka je Zinder ka tambaya wa ye *Jibril MC*."

Wani malalacin murmushi Jabir yayi ya ɗan kaɗan kan shi kaɗan haka sannan ya taɓe baki tamkar wanda ba ya so Jibril ɗin ya ji me zai faɗa yace" *Mu zuba mu gani*."
Chapter 127 · 0% Book details