← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 168

Sashe 98

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*46*

Da wuri ne sosai, hakan ya sa ta same shi gida ko fita bai yi ba, yada ta shigo tana sharar hawaye riƙe da rigar ta doguwa da take jin ta mata nauyi da yawa yasa kawai Alhaji Kabir ya fahimci Ummu ba ta cikin nutsuwa irin wacce ya san ta ciki, ko sallama ba ta yi ba fa, shi à yadda ya gani ma kamar ba ta gan shi ba, dan neman shigewa tayi ciki saida ya miƙe tsaye yace "Daga ina kike?"

Cak! Ta tsaya tare da juyawa ta kalle shi, saida ta sunkuyar da kan ta cikin wata irin raunanniyar murya tace "Na fita ne, amma ban jima ba, ka yi haƙuri sanar da kai ba."

Yadda ta yi maganar da haƙurin da ta bashi yasa shi jin nutsuwa a zuciyar sa, sai kawai tausayin ta ya mamaye masa zuciya, abin ka da wanda kake so, a hankali ya matsa kusa da ita, kafin ta ankara ya rumgumata jikin shi cikin rarrashi yana faɗin" Ummu, me ye matsalar ki ne wai? Kinga yadda duk kika shigo a gigice? Sai ka ce fa wacce na ke zanewa cikin dare."

Dama a raunane take, ita kan ta tausayin kanta da kan ta take yi, kuka kuma ta jima tana yin shi har ta gode Allah, sai kawai ta fashe da kuka tare da sakin jakar ta tana cimimiye shi, a nutse yake daddana bayan ta yana shafawa, Ummu da ta fara jin abun kamar wasa yake mata sai ta fara rage sautin kukan ta, a hankali ta fara kame ƙafafu, shi kuma take ya fahimci hakan daga gare ta, sai kawai ya ɗago kanta daga jikin shi ya kalle ta yace "Amaryata, muje ɗaki ne?"

Duk da abu ne da take so, amma sai ta sunkuyar da kan ta, kama hannun ta yayi zuwa ɗakin ta, duk da yasan ba kwanan ta bane yau, amma dai ya fahimci har da nesa da sukayi da juna ya ƙara ta'azzara halin da take ciki.

Lallai ta kai maƙura, dan kuwa duk wata taɓawa da ya mata sai ta ji ambaliya daga ƙasan ta, tun tana kukan jin daɗin ƴar wasar da ta samu yana yi da ita, har ta fara kuka na tsananin buƙatuwa da son ta ji yana jijjiga jikin ta, sai dai yana shiga jikin nata ba jimawa ya kawo, sa'ar ta ɗaya wasa da ta samu yau har ta yi nasarar tsiyayyar da wasu ruwan. Alhamdulillah.

*A* yammacin wannan ranar Alhaji Sagir ya zo da kan shi dan jin me ke faruwa? Saboda saida ya haɗu da Alhaji Kabir amma ya nuna masa komai fa lafiya lau, dan haka yake ganin kar a zo Ummu ce ke cutuwa su tauye ta. Tunda aka ce mata yana sallama ta san me ya kawo shi, sai dai tayi niyyar ba fa za ta faɗa ba, kawai za ta bar hakan a matsayin Ƙaddarar ta, wataƙila kawai tanadin da ubangiji ya mata.

Sai dai Kashhh! Alhaji Sagir da ya zauna yana faɗa mata "Ummu ba ki min adalci ba idan har baki faɗa min matsalar ki ba, ni na ɗauka sanin na isa ne ya sa har kika tako kia zo inda nake, to amma me yasa za ki ɓoye min? Kar jin nauyina ko kunya tasa ki cuci kan ki, idan kuma kin gagara faɗa min, to zan je wajen mahaifiyar ki na sanar da ita kina cikin matsala amma kin kasa sanar da kowa, wataƙila ita idan ta zo kya sanar da ita."

A dole ta dakatar da shi da sauri da cewa" A'a, zan faÉ—a, b sai Mama ta sani ba, bana so ta san me ke faruwa."

Gyara zama yayi yace" To ina jin ki."

Hijabin ta ta ƙara jawowa ta rufe fuskar ta, kan ta na ƙasa sosai tana kallon carfet, cikin kunya da ladabi cikin siririyar murya tace" Dama.. Ni ce ban da lafiya...to naje asibiti...kuma....na faɗa masa komai, amma sai ya...faɗa min girma ne ya zo masa yanzu, ba zai...iya komai ba, amma wai...nayi haƙuri tunda suma su Hajia Atika duk haƙuri suke yi,... To ba...ba."

Rintse idanu tayi sai hawayen da take riƙewa suka sauko kan kumatu, shiru tayi na sakanni tana sauke ajiyar zuciya. Komai ya fahimta a ƙanƙanin lokacin, ba kuma komai ya birge shi da yarinyar ba sai yadda ta sakaya zancen tayi alkunyya ta ƙi faɗan komai gatsau, sai dai duk babba mai tunani idan yayi nazari zai gane me take nufi, ƙwarai ya ji ya ƙara tausaya mata, kuma ya ji Alhaji bai kyauta ba da maganar ta yi haƙuri, ta yi haƙuri ma kamar ya? Da sha'awar? Wacce ubangiji ya halicci mutum da ita, ta ya ma ake haƙurin ta? Idan ma ana yi ai na ɗan lokaci ne, idan ba haka ba kuma za'a samu saɓani.

Shiru ya yi bai ce komai ba, dan ya fahimci ba iya zancen kenan ba, saida ta gama shasheƙar kuka ta sai ta nutsuwar ta sannan ta sake sunkuyar d kan ta tana share hawaye tace "Na gwada yin haƙurin ba tun yau ba, kasawa ne nayi har na sanar da shi abinda ke faruwa, ina so na manta da matsalar sannan na ci gaba da rayuwata, amma ciwo ya sakoni gaba, da naje asibiti kuma sai likitan ya nemi yi min lalata, ya ɗauka ko ni ɗin ƴar iska ce?"

Shiru ta sake yi na sakanni kafin ta ɗora da" Ba ma kallon duk wani abu da bai shafi addini ba a gidan nan, amma abun nan dake damuna ya sa na fara karance karancen abinda bai dace ba da kuma kallon finfinai, na jima da faɗawa halaka duk saboda ƙin ɗaukar matsalar da mahimmanci... Abban Na'ima..."

Ta Kira sunan da take kiran shi da shi tana kallon fuskar shi ta ɗora da" Ta kai ta kawo ko ya na kalli kusancin macen da namiji sai na ji a jikina, bayan na tuba daga aikata kallace kallacen nan, sai ga sheɗan la'anannen Allah har ya fara haska min Jabir wanda yake kallona a matsayin uwa kuma nake kallon sa ƙanena har ya ƙawata min shi a fuska, daga tsautsayi ya sa Jabir ya riƙe hannuna dan taimaka min akn ciwon da naji, sai kawai naji jikina na amsawa, to wannan wace irin halaka saboda Allah? A haka zan ƙare?"

Ta dire maganar da wani sabon kuka, kan Alhaji Sagir na ƙasa yana ta nazarin abun yana masa wani kallo a wata mahanga da ta dace da hankali da shari'a, a bakin shi kuma salati kawai da tasbihi yake yi, dan shi ya hango ƙiris ya rage yarinyar ta fara aikata ba daidai ba, ba wai zina tsakanin mace da namiji ba, mata ma ƴan uwan ta suna nan irin ta suke nema, ba kuma za ta musu wahalar shawo kan t ba, tunda a bakin gaɓa suka same ta ƙarasa jan ta kawai za su yi.

Cikin nutsuwa da yi ma matsalar ta kallon basira yace "Na fahimta Hajia Ummu, wannan ma ai maganar banza ce, kiyi haƙuri ? Ta ya zai ce haka? Kamar dai ƙaramin yaron da bai san inda rayuwa ta dosa ba?"

Sai kuma ya jinjina kai yace "Shikenan, karki damu Hajia Ummu, zan same shi in sha Allah, daga nan gurin shi zan nufa, zan yi magana da shi, kuma in sha Allah za ki ga biyan buƙata."

Jinjina kai kawai tayi amma kuka ya hana ta magana, miƙewa yayi yana sake jadadda mata "Ki daina kuka fa, wallahi zan masa magana, ni ban ma san ya aka yi ya bari har haka ta faru ba da har wani ɗa iskan likita zai miki rashin ɗa'a, zan same shi muyi magana, ki daina kuka kin ji."

Cikin kuka ta amsa mishi da "Nagode, Allah ya tsare."

"Ameen." Ya faÉ—a yana fita tare da faÉ—in "A gaishe min da auta, ba zan tsaya jin rigimar ta ba yau."

Ba Ta ce da shi komai ba har ya fita daga falon, saida ta goge hawaye ta sai ta nutsuwar ta sannan ta miƙe ta ci gaba da abinda take yi kafin zuwan Alhajin.

*******************

Lokacin da Maama ta buga sammako ta fita ɗan nata na kwance, ba wai baya tafiyar shi Saudia ba, shi tun yana rayuwa gaban mahaifin shi ba zai iya tuna ranar da har rana ta fara fitowa yana kwance ba, yayi sallah tun asuba dan jam'i ma ya samu, amma wai yana dawowa ya koma ya kwanta saboda matsananciyar kasalar da ya tashi da ita bayan mummuna kuma wani ɗaɗɗatan mafarkin wai yana tare da mace.... Anya kuwa ma a rayuwar sa ya taɓa irin mafarkin nan? Bai taɓa yi ba, to me yasa sai jiya? Kawai dan ya riƙe hannun Maaman shi? Saboda dai tsabaro fitina irin ta ɗan lis?
Chapter 98 · 0% Book details