← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 168

Sashe 159

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye yayi a ƙafafun shi, amma sai yayi saurin dafe gadon saboda wani irin yanayi da yaji kamar zai kayar da shi, saida ya saita nutsuwar shi tare da gyara kayan jikin shi duk da dai kallo ɗaya za ka mishi ka fahimci halin da yake ciki, musamman ma ƙasan shi da abun yayi muni sosai, haka a daddafe ya fita daga ɗakin, Ummu na satar kallon shi har ya fita sannan ta miƙe da sauri ta shiga ban ɗaki dan tayi wanka bata so ya same ta, a gaggauce ta fito ta koma ɗakin ta ta rufe ƙofar da makulli sannan ta jingina a ƙofar ta rintse idanu tana sauke numfashi kamar zaki ne ya biyo ta, sannu sannu ta shiga tariyo abinda ya faru tsakanin ta da Jabir.

*Yana* buɗe ƙofar ya hangi Fahad har ya fara tafiya zai koma da kwando na kwanuka a hannun shi, buɗewar da ya yi yasa Fahad juyowa ya dawo yana faɗin "Haba alaramma, ina kuke ne haka? Ai na ɗauka ba lafiya ba da na ji shiru."

Wani kallon jin haushi Jabir ya dinga jifan shi da shi har ya zo ya tsaya kusa da shi, ganin bai ce mishi komai ba ya sake cewa "Lafiya ko malam? Wane abu na faruwa ne a ciki?"

Cike da ƙufula Jabir ya ɗaga msa kai alamar e yace "Sosai ma, majalisi muke a ciki, me ya sa ka katse ni?"

Da mamaki Fahad yace "Malam, dama yanzu kuna nan falo kuna majalisi amma kuka barni nayi ta buga ƙofa?"

Cikin jin haushi Jabir yace "Akwai dokar da ta ce dole sai a falo za'ayi majalisi ne?"

Sai lokacin Fahad ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya ƙyalƙyale da dariya yace "Kai! Subhanallah! Malam kar dai na katse maka hanzari?"

Da sani irin yanayi kamar zai mari Fahad ɗin amma a nutse dan wallahi baya jin daɗin jikin shi sannan yace "Sosai ma, babban katse hanzari ma, daf nake da antayo mai sunan *sadiƙul masduƙ* duniya, amma ka dakatar saboda hassada da kake min, Fahad me na maka? Me ka zo yi mana yanzu cikin tsakiyar daren nan?"

Cikin muryar dake nuna zolaya Fahad yace "Ayya! Ka gafarce ni dattijo, naji ɗazu ka nemi abinci ne da za'a ba wa Mansur, shiyasa nayi tunanin to ko dai ƴar tawa tsayayya take maka ne, shiyasa na kawo maka abincin sannan na ce ka miƙo min ƴar nan in zazabga mata mari ta gane har yanzu akwai sauran hayaƙin nan a kaina, tuba ne nayi saboda ba kyau amma halin na nan ban manta ba."

Jinjina kai Jabir yayi a tausashe yace" Na ji, yanzu dai ka tafi Fahad, ina bata wani horon ne, gobe da rana ka dawo sai ka mata hukuncin, tunda ai kaga kai Baban ta ne ba zan hanaka ba."

Jinjina kai Fahad yayi yana ta ƙaarewa Jabir kallo ya miƙo mishi kwandon yace" Gashi to, sai da safen."

Girgiza kai Jabir yayi yace" Up um, ka tafi da shi, *ƴar albarka* ta dafa min na ci na ƙoshi, Alhamdulillah."

Wani shaƙiyin murmushi Fahad yayi yana jinjina kai sannan ya juya yace" To shikenan, sai da safe."

Cike da tsarguwa Jabir yace" *Siriki*."

Juyowa Fahad yayi ya dawo ya tsaya, hakan ya sa Jabir cewa" Sai naga kana ta min wani kallo irin na Æ´an iska, lafiya? Ko dai zargin kake ina wa Æ´ar taka wani abu ne a ciki?"

Da sauri Fahad ya girgiza kai yace" Ah haba, wannan tunani ma ai saɓo ne, kai da na san ɗan ne ita kuma maama, ko ba haka ba."

Ɗan murmushin yaƙe Jabir yayi yace" E mana, kai ai ka fi Aliyu fahimta, shiyasa na fara tsanar Aliyu, saboda kallon zan wa maama lalata yake min."

Faha dake ta dariya a ɓoye ne yace" Ni ma ai na fara tsanar Aliyun nan, dan gaskiya abu yake irin na marasa tsoron Allah, to amma abun da ya ɗan ɗaure min kai dattijo, kai da bakin ka kace mahaifiyar Siddiƙ na nan zuwa amma ba maaman ka ba, to ya akayi haka kuma?"

Ɗan taɓe baki yayi fuska a haɗe yace" Canza shawara kawai nayi, akwai wasy tsare tsare ne da nake ta yi akan Siddiƙ din, idan na ce na jira nan da shekara hakan zai ɗan taɓa shirin karatun da na masa, shiyasa kawai ƴar ka zata kawo min, wacce za ta zo bayan ta sai ta kawo su *Khadija* da su *Umar* in sha Allah."

Da mamaki Fahad dake ta tiƙar dariya yace" Jabir, wai nufin ka ƴar tawa ba zata ishe ka bane? Ahalinmu fa akwai jatumta."

Yatsina fuska Fahad yayi yace" To ai ina tsaka da fagen tantancewa ne ka katse ni ko? Mybe zuwa safe in canza shawara."

Dariya Fahad yayi ya juya yace" To saida safe, Allah baka sa'ar antayo mana SiddiÆ™ din nan a wannan shekarar."

"Ameen, nagode." Cewar Jabir yana jawo ƙofar da niyyar rufewa, sai kuma ya ji Fahad na faɗin "Allah kaimu safe lafiya, Aliyu zai sha labari."

Da sauri Jabir ya dakata yace "Siriki."

Juyowa yayi ya dawo inda Jabir ya fito daga cikin gidan gaba ɗayan sa, ba kamar duk hirar da sukayi yana daga ciki ba kula ya rufe jikin shi da rabin ƙofa saboda baya so ya fahimce shi, yana zuwa kusa da Fahad ya ɗan dafa kafaɗar shi yana faɗin "Kana ji Fahad? Kar ka faɗawa Aliyu, idan ya ji labarin nan uku zai saka ni, kawai ka faɗa masa da ka zo kayi ta buga ƙofa ka same ni kwance ma ulcerta ta motsa saboda yunwa, hakan zai sa ya ji tausayina ya ma ƴar ka wa'azi."

Jinjina kai Fahad yayi yace "To shikenan, amma dai idan na faÉ—i ba daidai ba ai zunubin a kan ka ne ko?"

Ɗauke hannun shi yayi daga kafaɗar shi ya kalle shi sosai yace "Fahad, ka bar ƙofar gidan nan kafin nayi shari'a da kai."

Nuna kan shi yayi da yatsa yace "Ni É—in?"

Da tabbaci yace "Kai ɗin mana, haihuwata ka yi...?" Sai kuma ya juy zai shige yana faɗin "Na ma lura son girman nan asali ya samo wallahi, to ita ma tana can za ta karɓi sakamakon ta, kai kuma je gurin matar ka." Fahad dai na dariya har ya koma gida haka Jabir ma ya dawo.

Ƙwanƙwasawa ya dinga yi amma Ummu tayi shiru, ta na ji amma tayi shiru tana kwance kan gado, saida ta ji yana ci gaba da bubbugawa ta taso, tsaye tayi bakin ƙofar da har lokacin yake ƙwanƙwasa mata a nutse kamar mai son saka ta bacci, jingina tayi a ƙofar sosai cikin taushin murya tace "Dan Allah Jabir ka tafi, bana son haka ta ci gaba da faruwa tsakanin mu, na roƙe ka ka tafi Jabir, sannan..."

Da sauri Jabir kamar zai yi kuka ya furta "Dan Allah Kulsum?"

Da sauri ita ma tace "Ka tafi Jabir, kar ka kwanta da sh'awata a ran ka, hakan zai sa na kwana cikin hushin ubangiji."

Haɗa kan shi yayi da ƙofa tare da dafeta da hannayen shi yace "Ba zan iya haka ma Kulsum, ko nayi ƙoƙarin cire hakan a raina ba zan iya ba, tunda nake a rayuwata ke ce mace ta farko da na haɗa jikina da ita, kowane haɗuwar jikina da naki a ƙwaƙwalwata yake zaunawa, ba zan iya dakatar da hakan ba, dan yanzu haka jikina a bayyane yake a matakin ƙarshen da ni kaina ya fara tsorata ni, ki buɗe ƙofar Kulsum, bana so ki kwana alhalin *ni ina begen ki*, ba zan bari mala'iku su tsine miki ba, dan zan kwana tsaye ina shaidawa ubangiji yafiyata a gare ki ne, dan Allah Kulsum, ki buɗe ƙofa kin ji."

Ummu ma jikin ta ne ya mutu sosai, inda ta ji kalaman shi na ƙarawa marar ta ɗaurewa, shauƙin sake kasancewa da shi na ci gaba da kamata, hakan yasa ta kama hannun ƙofar a hankali tare da murɗa makullin ta buɗe, sadda kan ta tayi ƙasa bata kalli ko da fuskar shi ba, shi ma a hankali ya dinga takowa har ya zo daf da ita bayan ya ƙare mata kallo, a nutse ya sa hannu ya shafo hannun ta sann ya tallabo haɓar ta, da sauri ta rintse idanu, cikin raɗa yace mata "Kalle ni mana maamana."

A hankali ta buɗa idanun ta da suka cika da ruwa, tana buɗewa kuma hawaye suka gangaro mata, da sauri ya sake tallabo fuskar ta da duka hannaye biyu yana girgiza mata kai, sai kuma ya zuro harshen shi a nutse tana kallo ya dinga lashe hawayen nata, kafin ya ƙurawa idanun ta ido yace " A duniya *hawayen ki* su suka fi komai ɗaga min hankalina, na jima da yin alƙawarin cewa in dai ina tare da ke ba zan taɓa bari ki zubar da su ko da a wajen farin ciki ne."

Da ɗan mamaki a fuskar ta na abinda ya faɗa cikin shaƙaƙƙiyar murya tace "Me ya sa?"

Ɗan murmushi ya ƙaƙaro tare da ɗaga kafaɗu alamar oho! Sannan yace "Ban sani ba nima, sai dai tun *ban san wa ye ni ba* nake jin *Ummu Kulsum* daban a ƙasan zuciyata, dan zamu zama *ma'aurata ne*? Ko kawai *haɗuwar jini ce*? Ban sani ba nima."
Chapter 159 · 0% Book details