← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 168

Sashe 12

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya cika cikin shi fam da ruwa har yana jin suna taso mishi sannan ya zauna kan wani dakali dake zagaye da shukoki masu kyau ya rabka tagumi, ƙwarai daga yau dai ka ya bar gidan mahaifinshi kenan, zai shiga duniya ne kawai shi ma ya zama ɗan iska kamar yadda yake faɗa masa, zai je duniya idanunshi su buɗe sannan ya dawo ya gagareshi, tabbas idan har ya yi girman da ba zai daku a hannun Abbanshi ba, to shakka babu sai ya nuna kan mahaifinshi da bakin bindiga, idan kuwa ba haka to zai saka masa hawan jinin da zai zama ajalinshi.

Kuɗi yake so wanda zai hau mota, gashi kuma kuɗinshi suna hannun madame bai karɓo ba, ba kuma zai iya zuwa unguwar nan ba yanzu, zai jiras ne zuwa rana sai ya tafi, lokacin dai tabbas Abbanshi baya unguwar ma, yana karɓo kuɗinshi to zai faɗa garuruwan dake maƙwabtaka da garin nan ne, ba kuma za'a sake ganinshi ba sai bayan wasu shekaru.

Ɗan jinginar da yayi a bango yasa bacci ɗaukarsa saboda yanayin mai daɗin gaske, ga iska dake huro iskan shukokin nan dake fito da wata sanyayyar iska mai ƙamshi kala daban daban. Alhaji *Kabir* da dawowarsa kenan daga masallaci, dama kuma idan ya tafi baya dawowa gida sai gari yayi haske, wasu lokuta ya kan yi tattaki ne a cikin unguwar, wani lokaci kuma asibiti babba yake zuwa dan gaishe da marasa lafiya, yau ziyarar shi a maƙabarta yayi ta tun asuba, Shiyasa ya dawo har rana ta fito sosai.

Dake ta bayan gidan ne ya biyo inda Jabir ke bacci, tunda ya ganshi ya tabbatar mai gadi bai ganshi ba, dan baya barin baƙuwar fuska suna zama a wurin nan, har ya ɗan wuce zai yi tafiyar shi...sai kuma tunanin ko almajiri ne? Kuma ta yiwu yanzu ana can ana karatun safe a makaranta su, shi kuma bacci ya ɗaukeshi yasa ya dawo kaɗan ya tsaya gaban Jabir dake kwasar bacci.

A hankali ya mayar da carbinshi a ɗaya hannunshi sannan ya zura hannun ya daddaɓa guiwar Jabir, a tsorace ya farka tare da tashi tsaye zunbur yana zazzare idanu, yanayin da ya tashin ya sake tabbatarwa da Alhaji Kabir Jabir almajiri ne, wataƙila haka malamansu suka saba tashinsu, cikin tattausan murya Alhaji Kabir cike da dattijantaka yace masa "Me kake anan baka je makaranta ba? Ko ba kwa karatun safe ne?"

Kame-kame Jabir ya fara yi yana ƙyaƙyabta idanu da mi-mi-mi da baki, cike da kulawa Alhaji Kabir ya sake cewa "Ko ba kwa karatun nan? Na ga yau ai Lahadi ce."

Madadin ya bashi amsa, sai kawai ya rusuna cike da ladabi da darajanta shekarun shi yace "Ina kwananku."

Ajiyar zuciya Alhaji Kabir ya sauke tare da faÉ—in "Na É—auka ba ka magana ai."

Ɗan sosa ƙeya Jabir yayi yana sadda duban shi daga kan fuskar dattijon mai cike da kamala da haiba yace "Ina yi, ban san me zan ce bane *Abba*."

Da mamaki Alhaji Kabir yace "Ba ka san me zaka ce ba? Ba ka zuwa makaranta kenan?"

Cikin saiɓi Jabir yace "Ni ba almajiri bane, islamiyyarmu ba'a nan take ba."

A nutse Alhaji ya shiga ƙare masa kallo daga sama har ƙasa, ɗan taɓe baki yayi ya zubawa fuskarshi idanu yace "To me kake anan?"

Saida ya sauke numfashi kafin yace "Hutawa ne nake, ina jiran rana tayi ne zan tafi amso kuÉ—ina dan na biya kuÉ—in mota sai na tafi."

Jinjina kai Alhaji Kabir yayi yace "Ohh! Dama kai ba É—an garin bane?"

Buɗa baki yayi zai bashi amsa, sai kawai yaji ruwan nan da ya tatila suna neman taho mishi ta baki, hakan yasa ya ɗanyi shiru yana kallon Alhaji, da ya ga ya tsare shi da idanu kamar mai tuhumarsa, sai ya ga ai bai kyautu ba yana magana kuma yana ƙyaleshi, dan haka ya Buɗa bakinshi yace "A'a, nan ga..rin...Bab..ana yak..."

Da sauri ya matsa gefen hanya ya duƙa ya shiga amayo ruwan nan da ya ɗirkawa cikinsa, hakan ya tayar da hankalin Alhaji Kabir ya bi bayan shi yana masa sannu da tambayarsa daa bashi da lfy? Ba tare daya ɗago daga durƙushen ba ya dafe kanshi kaɗan ya furta "Jiri ne kawai nake gani, lafiyata ƙalau."

Da son jama'a da taimaka musu yasa Alhaji Kabir tallabo hannun Jabir ya miƙar dashi tsaye, ba tare daya sake shi ba suke takawa zuwa inda ƙofar shiga gidan take yana cewa "A'a, kana ganin jiri ina lafiya take, muje ciki sai ka faɗa min inda zaka je, ta yiwu yunwa ce ke addabarka, dan duk abinda ka amayo babu abinci, zallar ruwa ne kawai."

Suna zagayo ta ƙofar gidan mai gadi dake zaune yana sauraren radio ya taso da sauri yana masa sannu da zuwa da kuma faɗin "Alhaji baƙo kayi? Ko dai almajiran nan ne masu zuwa ta bayan gida suna cirar mana mangwaro da Lemun tsami?"

Ba tare da ya saki hannun Jabir ba yace da shi "A'a Ilya, nima anan na gan shi zaune, da alama bashi da lafiya, kuma dai ya ce shi ba almajiri bane."

Sai kuma ya nufi ƙaramar ƙofar zai shiga yana cewa "Bari na shiga da shi ciki, har da yunwa ke damunshi ma."

Take musu baya mai gadin yayi ya buɗe musu ƙofar sannan ya rufe yana addu'ar Allah ya sawaƙe, suna shiga katafaren filin tsakar gidan Jabir ya kalla dake ɗauke da ɓangarori guda huɗu kuma maka-makan da suka bayyana akwai girma da ɗakuna a kowane ɓangaren. Ɗan satar kallon Alhaji Kabir yayi da ya ga ya ja birki shi ma yana kallon ɓangarorin kamar yau ya fara ganinsu.

Alhaji Kabir kuma ba komai ya saka shi tsayawa yana kallon su ba sai son gane ɓangaren da zai nufa da Jabir ɗin ya samu kulawa ta abinci da hutawa kafin ya san wanene shi kuma daga ina yake sannan ina zai nufa? Hajia *Lubabatu* ita ce babba a gidan, mata ce mai dattako da kawaici, a ƙalla akwai yara maza da mata da suka tashi a hannun ta wanda shi yake bata riƙonsu saboda bata taɓa haihuwa ba, *Khamis* shine yaro na ƙarshe ɗan abokinshi da ya kawo shi yake karatu anan, yayi alƙawarin daga shi ba zai sake haɗata da ɗan kowa ba, duba da za ta ga kamar dna bata haihuwa e ake bata riƙon har wanda ma basu haɗa jini da su ba.

Hajia *Asiya* kuma, mace ce mai saɓanin halayen Hajia Lubabatu, bata da kara, bata da kawaici, bata da sani baroe sabo, tun farkon farawa da ya so bata riƙon *Saudat* sam ta ce bata yarda ba, to da wane za ta ji? Nata yaran ko na wasu? Hajia *Atika* kuma, bata da lokacin nata yaran ma bare na wasu, ma'aikaciya ce kuma ƴar kasuwa da ita dai harkokin ta kawai ta sani a gaba, dan haka ma ba ya jaraba tafiya da Jabir can ba ya ce ta bashi abinci ya ci sannan ta samo mishi kaya a cikin ko da na *Hayat* da yasan zasu kai tsara da wannan yaron.

Dan haka kawai ya karkata akalarshi zuwa ɓangaren margayiya *Aminatu*, wanda yasan da tana raye bai da matsala dan wannan, amma duk da haka zai kai shi wurin wanda a yanzu ke ɓangaren wato *Ummu Kulsum*, dan sak halayen da take nuna masa a ƴan kwanakin nan irin na margayiya Aminatu ne, duk da dai yasan tana fama da kanta sakamakon jiya dai ya lallaɓata ya samu buɗe budurwarsa, amma yasan ba za ta gagara ciyar da baƙonshi ba tunda ya ba Hajia Lubabatu saƙon a kawo mata abinci, zuwa yanzu kuma yasan zai tarar da an kawo mata ɗin.

*WANI GARI*

A tsawace manajan (manager) ya sake nunosu da yatsa yana jadadda musu "Wallahi ba zai yiwu ba, ku gaggauta fito da ƴan matan nan biyu da suka ɓata tun kafin yallaɓai ya samu wannan labarin, dan in har ba'a samu ba to ina mai tabbatar muku kafin a koreni a nan ni zan fara korarku, dan shakka babu kuna da masaniyar inda yaran nan suke."

Cike da bayar da tabbaci wani dattijo yace" Yallaɓai, ka yarda dani, wallahi ban san komai a kan ɓatan yaran nan ba sai dai ko idan abokin aikina da yayi aikin kwana."

Wanda ya faÉ—a tare da nuna shi ne ya zabura ya kalli tsohon yace" A'a, ya zaka ce haka? Ko aikin kwana nayi ai naga har dare dai muna tare da kai, kuma nima ba san komai ba da ya faru gaskiya, sai dai ko su masu kula da É—akunan Æ´an matan."

Manyan mata ne a shekaru ɗayar kuma har da ƙiba, ganin duk an kallesu yasa matsakaiciyar faɗin" Wallahi yallaɓai nima ban san komai ba gam..."

Kafin ta ƙarasa ɗayar ma mai ƙibr tace" Nima kuma haka, yallaɓ.."

A tsawace manajan ganin suna neman haukatashi bayan kuma shi yasan zai fuskanci hukunci mai tsanani wajen mai gidansa yace" Ku dakata."

Ɗaya bayan ɗaya ya dinga nunosu da yatsa yana cewa" Wannan ba shine na farko ba da ƴan mata ke ɓacewa a wannan gidan *marayun*, ku sani wannan ba abu bane da hankali zai ɗauka, idan muka sake maganar nan ta fita wallahi kaf ɗinmu gwamnati zata sa a rufemu, dan haka tun muna shaidar juna wanda duk yasan da hannunshi a ciki ya fito ya faɗa, ni kuma nayi alƙawarin sassauci da kuma rufa masa asiri, dan wannan ba abu bane da zamu bari ya fita gari har ƴan jarida su sakomu gaba."

Kallon kallo suka dinga yi wa junansu, sai kuma kowa ya taɓe baki ya kawar da kai alamar shi dai fa ba shi bane, jinjina kai yayi da ya fahimci me shirun su ke nufi sannan yace" Shikenan, kuje..."

Sai kuma ya gyara tsayuwarshi yace" Zan wa aminina magana ya min bincike akan lamarin kasancewa rasa jami'in tsaro, ku sani idan har binciken sa ya zaƙulo min ɗaya daga cikin ku, to haƙiƙa zan tsaya ne tsayin daka wajen ganin an rataye mutum, dan har da ɓatan ƴan mata *goma sha shidan* da suka ɓace a cikin shekara uku kacal zan sa a yi."
Chapter 12 · 0% Book details