Sashe 45
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuɗi ne a ciki ba ko naira ko cfa ba, dollar ce ya aiko mata ba tare da ko gajeran saƙo ba, rashin sanin me kuɗin ke nufi? Me shirun shi ke nufi da ita yasa ta faɗawa kan kujera ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, saida ta ci kuka abun ta ta ƙoshi ta shiga ɗakin ta, *niyya* ɗaya ta sata shiga a wannan lokacin, shine zata tattara kayan ta ta tafiyar ta, to amma Abida fa, wacce ita ce mai laifin? Sannan kullum Habaici take mata ita ta iya takonta, sannan ba zata yarda ta ƙare a asararriya ba kamar ita, dan haka ma ta nemawa kanta mafita. Abubuwa uku suka sa ta canza wannan ƙudirin, *na farko* shine: Abida da zata bari gidan ta ci karen ta babu babbaka, na *biyu* kuma ba ita ce mai laifin ba Abida ce, na *uku* ma bata so asirin Abida ya tonu yanzu, dan Abida makira ce ta ƙarshe, dan haka dole sai tayi taka tsantsan wajen kawo ƙarshen tuggunta, idan da haka ba zata sake ruftawa da ita a banza, dan haka sai ta sa kowa ya san wacece ita sannan idan ma barin gidan ne su bar shi tare.
********************
Hankali tashe Hajia *Soueiba* ta dinga bubbuga ɗakin Sa'ad kasancewar basu da wani ɗa namiji babba da zai iya taimaka musu, Fadila ita ce babbar ƴar desu bayan wacce suka fara haifa ta rasu, shi ma d ai hankalin nashi ne ya tashi dan daga jin bugun ƙofar yasan ba lafiya ba, ai ko y ana buɗewde cikin kuka take cewa "Sa'ad muje dan Allah ka taimaka min mukai Alhaji asibiti."
Da sauri ya juya bayan shi ya kalli agogo data nuna mishi ƙarfe 04 saura kaɗan, sai kuma ya sake kallon ta da girmamawa yace "Me ya samu kawun? Bashi da lafiya ne?"
Cikin rashin nutsuwa tayi gaba zata wuce tana faÉ—in "Daga ya shiga ban É—aki zaiyi alwala ya yanki jiki ya faÉ—i, muje da sauri dan Allah?"
Bai ƙara ɓata lokaci ba ya fito daga ɗakin tare da jawo ƙofar ya rufe ya bi bayan ta, dake mutum ne shi mai tsayi amma babu jiki, dan damuwa ma duk ta ƙara zabge shi ya fita hayyacin shi kamar wanda baya ci yana ƙoshi, haka Sa'ad yayi jarumtar tallabar shi da ƙyar ya saɓa a kafaɗa suka kai shi mota, Fadila ce ta buɗe muu mota dan basu da mai gadi sannan ta rufe duk gidan ta koma ciki dan kula da gida da ƙannenta biyu kamar yadda Hajia Soueiba ta bar mata sallahu kafin su ga abinda hali ya yi.
A taƙaice said yayi *kwana huɗu* asibiti, anyi sa'a da ya farfaɗo babu shanyewar ɓarin jiki, dan haka likitocin suka sake jan kunne kan a tsananta kula da shi, duk da ba gari ɗaya bane saida mahaifin Sa'ad da Hajia suka zo duba shi, a ranar Alhaji ya koma Hajia kuma ta kwana biyu sannan ta tafi, har lokacin gaisuwa kawai ta haɗata da Sa'ad, sai Fadila data kula tana shiga lamarin shi sosai shi kuma yana share ta, ta ji a ranta cewa zata iya yin wani abu a kai, ko ba komai tana son Sa'ad kuma tana ƙaunar sa da shiriya sosai, amma har ta tafi babu wanda ta faɗa ma ƙudirin nata bare a sani.
Sosai yake kula da shi tamkar shi ya haife shi, yana wuni gidan tare da shi yana taimakawa Hajia Soueiba wajen jinyar shi, yana kuma ganin mutane kala kala dake zuwa waje shi dubiya, a hakane kwana tara da faruwar wannan abu da dare ya fita masallaci tare da autan gidan *Marwan*, yana dawowa ya tarar da baƙon da bai taɓa tsammanin wani a jihar Maraɗi ba ma ya san shi bare a nan ɗan garin da kawun shi ke aiki, ganin *Hambali* a gidan nan ya matuƙar kiɗima shi da jefa shi a lisafin me ya haɗa kawun shi mutumin arziki da Hambali? A ina suka san juna? Me ye tsakanin su? Damuwar kawun na da alaƙa da Hambali ko sana'ar shi? Ya shiga ruɗani sosai fiye da tunanin mai tunani, har saida ya samu dakali ya zauna ya dafe kai, dan baya so ma su haɗu da Hambali bare kawun ya san shi ma ya san shi.
*Ƙara* duban shi sosai Hambali yayi cikin nutsuwa yace "Alhaji Hisham, me yasa ba zaka manta da abun nan daya faru ba ka fuskanci gaba kawai? Ni banga abun ɗaga hankali a ciki ba, laifi aka maka ka kuma ɗauki fansa, to sai me? Me ye na damun kanka har kana neman ka kashe kanka a banza, bayan kuma iyalinka suna buƙatar ka a raye, ko manta da haka ne?"
Kanshi na kallon ƙasa ya girgiza kai a sanyaye yace" Ba zan iya mantawa ba Alhaji Hambali, abinda na aikata a baya sharrin sheɗan ne da ruɗin zuciya, hukunci na yanke cikin hushi wanda yanzu shi ke barazanar kawo ƙarshen rayuwata, me yasa na yi haka? Me yasa na cutar da wacce bata ji ba kuma bata gani ba? Me yasa na zalince ta? Bayan kuma bata san komai ba ma daya faru? Me yasa zan ɗauki fansata a kan ta?"
Ɗan tsaki Hambali yayi irin na jin haushin nan sannan yace" Ai fansar da ka ɗauka ta dace da muhallinta, tunda wanda kayi dan shi yana fama da wannan raɗaɗin har yanzu, ko kasan ahalin Ahlan suna fuskantar ƙuncin rayuwa da rashin walwala saboda abinda ka aikata?"
Cikin ƙunar zuci da dana sanin kuskuren nashi ya ɗago ya kalle shi a kausashe yace" Ba dan taimakawar ka ba, ni nasan da ban iya aikata komai ba ga wannan iyali, Hambali, zan iya cewa tarayya ta da kai asara ce, bata ƙare ni da komai ba sai dana sani, ka sani ina ta neman afuwar Allah akan abinda na aikata, ina nan kuma ina bibiya har sai naga na sake dawo da wannan farin cikin da na zama sanadiyar dakushewar shi ga ahalin arziki kamar wannan, kai kuma... Ka sani lokaci ne zai maka nashi hisabin, kai da ƴar ka duk zaku girbi abinda kuka shuka da yardar Allah."
A hankali ya miƙe tsaye jiki ba ƙwari yayi tsaye yana kallon shi yace" Na roƙeka daga yau kar ka sake zuwa gidana, dan bana son sake wata mu'amala da kai."
Da mamaki Hambali ya tashi tsaye yana kallon shi yace" Hisham, ni kake kora a gidan ka? Har kake cewa baka son sake ganina?"
Kallon shi kawai yayi bai ce uffan ba dan bai da lokacin ɓatawa, jinjina kai yayi cike da gargaɗin nan tare da miƙewa tsaye yace" Shikenan, zaka san ni ka wulaƙanta, ka sani na taimake ka a lokacin da ka nemi taimakona, ba biyana kayi ba bare ka raina min wayo, kamar yadda babu wata riba da naci dangane da hakan."
Ya juya zai tafi Alhaji Hisham yace" Kai ko ka ci riba, ko ka manta kai ka kawo shawarar yadda za'a yi? Sannan kaima kayi hakane dan farin cikin Æ´ar ka da son zuciyar ka, Alhaji Hambali, kamar yadda na faÉ—a maka tarayyata da kai asara ne, dan ai daga baya na fahimci kawai anfani kayi da ni wajen cimma burinka a wajen mutanen wannan gida."
Yana gama faɗin haka shi ma ya juya ya shige ciki ya bar shi nan, da kallo Hambali ya bi shi sai da ya ɓacewa ganin shi sannan ya nufi inda motocinshi suke da masu tsaron dake take mishi baya.
Har suka fita daga gidan basu haɗu da Sa'ad ba, saida ya ga fitar su ya tashi ya shiga ciki, a saman kujeran cin abinci ya hangi kawu na cin abinci, Hajia ya ma sannu da hutawa ya yi hanyar nufa wajen kawun, Fadila ma da fara'ar ta na son ɗaukar hankalin Yayan nata t mishi sannu da zuwa, da murmushin yaƙe ya amsa mata ya wuce inda zai tafi kawai.
Yana zuwa daga tsaye yace "Kawu, ina so zamuyi magana?"
Kujera ya nuna mishi yace "Bismillah Sa'ad."
Saida ya ja kujerar ya zauna sannan ya kalle shi yace "Lafiya Sa'ad ? Me ya faru?"
Ba alamar wasa ko kaÉ—an ya kalle shi shi ma yace "Kawu, dama kasan Hambali ne?"
Da mamaki ya kalli Sa'ad É—in tare da cewa "Hambali kuma?"
Jinjina masa kai yayi yace "E kawu, wanda na gan ku tare, kuma yanzu ya fita daga gidan nan."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya aje cokalin abincin shi tare da ture farantin gaban shi ya fuskanci Sa'ad sosai sannan yace "Na gane wanda kake magana a kai, na san shi Sa'ad, hasalima zan iya ce maka na san abubuwa dayawa a kan shi, kuma ban san abubuwa dayawa a kan shi ba."
Da yanayin shiga damuwa da ƙanƙance idanu har da saurin maganar da yake yi idan ya shiga tashin hankali ko ɓacin rai yace" Amma kawu me ye haɗin ka da shi? Hambali fa ba mutumin arziƙi bane."
Da mamaki sosai kawun ya kalle shi yace" Sa'ad, ka san shi ne? Ya aka yi ka san ba mutumin kirki bane?"
Ɗan maƙale kafaɗa yayi da rashin gaskiya yace" Kawu na san shi ne kawai a bakunan mutanen gari, amma dan Allah kai me ye ya haɗaku ? Kawu ina tsoron abinda zai iya zama shine silar haɗuwar taku?"
Numfashi kaxu Hisham ya sauke ya sake duban Sa'ad da yadda yaga ya rikice sosai sai yake ji a ran shi kamar tsantsar kulawa yake bashi, dan haka a tausashe yace" Sa'ad, shekaru sha bakwai da suka wuce na aikata wani kuskure da a yanzu ya zamar min tashin hankali da barazana a rayuwata, da na sani da ban aikata abinda Hambali ya izani na aikata ba, da na yi dogon tunani da ban bi abinda zuciyata ke raya min na aikata ba a wannan lokacin, amma bayan na *raba hanta da jini* sai na kasa samun sukuni, har yau da nake maka maganar nan bana da kwanciyar hankali, bana isashen bacci, bana cin abinci cikin salama duk saboda tunanin *ina yarinyar take*? Me take yi? Hannun wa take? Na gari ko mugu? Shin ta mutu ne? Wani abun ya cinyeta tun a inda muka jefar da ita...?"