← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 168

Sashe 46

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙasa yayi da kan shi cikin yanayin matsanancin tashin hankali ya sunkuyar da kan shi yana shasheƙar kuka har da hawaye, sosai Sa'ad ya fahimci abun mai girma ne kuma mai tayar da hankalin kawun na shi, dan haka ya miƙe tsaye ya rusuna gaban shi ya ɗora hannun shi a cinyar kawun cikin rarrashi yace "Kayi haƙuri kawu, barin matsalar nan a zuciyar ka ba shine maslaha ba face ya ci gaba da girmamar da damuwa a gareka, ka tattauna hakan da ni idan ka yarda zan iya taimaka maka da wani abu, dan Allah kawu, ka faɗa min abinda ya faru, wataƙila na taimaka sosai wajen fitar da kai daga matsalar nan, duba da nasan waye Hambali, kuma kawu sani na sosai ba sanin shanu ba.

Kallon shi yayi, sai ya ji zuciyar shi na samun nutsuwa da gamsuwa akan ya faɗa wa Sa'ad din abinda ya faru, nauyayyan numfashi ya sake saukewa sannan ya mishi nuni da ya koma ya zauna, kallon shi yayi yana share ƙwallar idanun shi sannan yace "...

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.

Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._

_Bismillahir-rahamanir-rahim._

*21*

Kallon shi yayi yana share ƙwallar idanun shi sannan yace "Shekara sha bakwai da ta wuce ai kun samu labarin haɗarin da maman Fadila tayi ko?"

Jinjina kai Sa'ad yayi cike da kulawa yace "E kawu, haÉ—arin da yayi sanadiyar rasa abinda yake cikin ta."

Shima jinjina kai yayi da gamsuwa yace "To wannan abu da ya faru shi ya ja komai, lokacin da Maman Fadila ta matsa min tana so taje Agadez bikin Yayar ta data haihu ban yarda ba, saboda lokacin tsohon ciki ne jikin ta wanda muke saka mata ran haihuwa a kowane lokaci, amma sai ta shiga damuwa da ɓacin rai wanda ni kuma bana son hakan, dole na haƙura na amince ta tafi tare da sauran ƴan uwan ta, sun isa lafiya kuma anyi suna lafiya har ma suka fara shirye shiryen dawowa, suna gobe zasu taho da sassafe da mukayi waya ta ce min zata je wajen kitso da lalle dan tana so ta dawo min kamar amarya, na bata izini ta tafi cikin farin ciki, tayi lalle da kitso har tayi wasu siyayya a hanya duk dan zata taho washe gari, amma Allah bai nufi hakan ya kasance ba, duk lokacin da na ga kiran Soueiba sai gabana ya faɗi da tunanin ta haihu ne, dan mahaifiyar ta ma da suka je saida ta kirani tayi ta faɗa me yasa na barta ta je a wannan halin? Hakan yasa nake saka rai dayawa da a kira a ce min ta haihu, amma wannan kira da aka min daf da magrib sai aka ce min idan na samu lokaci naje an mata aiki ne sannan abun bai zo da rai ba. Na shiga tashin hankali sosai Sa'ad na rasa inda zan saka raina, a lokacin ƙaramin ma'aikaci ne ni da albashina ba wani bane, gashi ina so na isa wajen matata akan lokaci, dole na ranto kuɗi na biya jirgi dan shi kaɗai zai kai ni gareta da gaggawa, na je...sai dai na samu Soueiba da raunika a jikin ta bayan aikin da aka mata aka ciro yaron, kasan me ya faru?"

Ya tambayi Sa'ad da gaba ɗaya ya zuba mishi idanu yana kallo, girgiza kai yayi a hankali alamar a'a sannan ya ci gaba da cewa" Sai lokacin aka sanar da ni haɗari tayi a hanyar ta ta dawowa gida, wani mai mota ya kaɗeta, sannan...abin..." Sai kuma kuka ya so cin ƙarfin shi said ya dakata ya sauke numfarfashi kafin ya kalle shi yace" Abinda yake cikin ta ma buguwar da yayi ce ta zama silar fitowar shi babu rai, dan hoton da likitan ya nuna min na yaron ya nuna min yadda kan jaririn daga gefe ya faɗa sosai kamar zaiyi rame, ya tabbatar min ko da ya rayu zai wahala ne mu ma mu wahala, dan ba tabbacin ƙwaƙwalwar shi zata kasance cikin ƙoshin lafiya, abun takaici da baƙin ciki, abunda ya ɓata min rai har ya saka ni aikata abinda na aikata yanzu shine, babu wanda ya kaɗeta a wurin, yana ina? Wai sai aka ce min _"Kasancewar shi ɗan babban gida kuma babban mutum, zaman shi anan ba tsaro kuma labari zai iya yaɗuwa kan abinda ya faru, amma ya bar maƙodan kuɗin da za'a kula da lafiyar ta har ta warke."_ Wannan magana ce Sa'ad? Ka buge mata mai tsohon ciki, amma saboda rashin sanin darajar ɗan adam ka ce wai ba zaka ko tsaya ka duba ta ba? Wannan abu ya ɓata min rai ƙwarai da gaske, hatta kuɗin da aka yi ragowa na aikin ta Maman ta ta bani wai mu koma gida ban karɓa ba, kuma wallahi kuɗin sun isheni na ja jari, to amma fa ɗana na rasa da lafiyar matata. To a inda muka haɗu da Hambali shine zamu fita daga asibitin ya tsayar dani muka gaisa sai ya bani katin shi ya ce na kira shi zamuyi muhimmiyar magana, ban yi ƙasa a guiwa ba wajen kiran shi bayan na kaɗaita, daga yadda na fahimta baya ƙaunar wannan ahalin, sannan ƴar shi ma dake aure a gidan ba dan Allah take zaune a can ba, sannan alamu sun nuna ko ta ina Hambali yana bibiyar rayuwar mutanen nan ne, Shiyasa ma ya san da labarin wannan haɗarin, ya sake rura min wutar tsanar su da ƙiyayya, ya nuna min an ci zarafina ne dan ban da ƙarfi, dan haka zai tsaya min na ɗauki fansa, dama raina a ɓace yake, a hassale nake da abun har lokacin, sai ban yi tunanin komai ba kawai na amince, kasan me muka shirya?"

Sa'ad dai dake kallon shi girgiza kai ya sake yi alamar a'a dai, dan haka ya sake numfasawa yace" Alhaji Mukhtar Saheeb Ahlan, shine ya banke matata kuma yayi tafiyar shi, ashe a lokacin shima ta shi iyalin tsohon ciki ne da ita, dan a ranar da muka haɗu da Hambali yake ce min ta haihu dan a ranar da muka bar asibiti ranar aka yi suna, ya tunzurani kan mu sace ƴar shi shima sai ya ɗanɗani zafin rabuwa da ɗan da kake so, na amince da shawarar ɗari bisa ɗari, ya nuna min shi kawai taimaka min ne zai yi ya jagoranci abun, amma ni ne mai bayar da umarni kuma shugaban aikin, da jami'in da basu yi tsammani ba muka ɗauke yarinyar daga gidan dan lokacin ba wani ƙwaƙwaren tsaro kamar yanzu, lokacin... Lokacin da na kalli yarinyar dake ta kuka tana son mamanta, na ji tausayinta har na ce ma Hambali a mayar da ita kawai zamu ɗauki fansa ta wata hanyar, yadda ya hana a lokacin da yadda ya dinga nuna min, sai kawai na ji a raina shima dai akwai wata manufar a zuciyar shi game da haka, da amincewar mu aka yi nesa da yarinyar daga mahaifarta zuwa wata jaha da basu tsammani, madadin na samu salama na aikata abinda nake ganin na kyauta, sai na rasa nutsuwa daga lokacin, na nemi zaucewa saboda mafarkai da kullum sai nayi, ko dai naga yarinya na kuka, ko mace na ta kuka ko mutane dayawa ma, a lokacin da taimakon Allah dana Soueiba ne na fara dawowa hayyacina, dan saida malamai suka shiga lamarina, cewa suke jifa ce, ture ne, shiga gaba ne, amma ni nasan menene kuma na ƙi faɗa musu komai... Kwatsam watanni kaɗan da suka wuce na ga labarai ana neman wannan yarinyar, kayan da aka zayyana dake jikin ta lokacin ni nasan ita ce, to amma kuma *wa ya sace ta biyun*? Ya ake so iyalin nan suyi da rayuwar su? Shin ba'a san rasa ɗa ɗaya bama na iya sa mutum ya kauce hanya ko ya haukace? Bare kuma guda biyu? Ni ubangijin da ya bani shi ne ya karɓi abun sa, na kasa haƙuri da Ƙaddarar har na kauce hanya, ina ga su da yara biyu kuma mata, sannan basu ga gawar su ba bare ma su kwantar da hankalin su, shin ya ake so suyi ne da ransu? Ya mahaifiyar su take ji? Wane irin hawan jini ne zai kamata?"

Iska ya feso daga bakin shi tare da dafa kafaÉ—ar Sa'ad yace" ÆŠana, ka ji abinda na aikata, da le zaka iya taimaka min?"
Chapter 46 · 0% Book details