← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 168

Sashe 36

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Alhaji Kabir yayi ya ɗauki kwandon ya miƙawa Mujittafan yana cewa "Da gaskiyar ka Mujittafa, ban san da haka ba ai da na sa ta maka girkin ka na musamman."

Dariya sukayi shi kuma ya amshi kwandon ya aje gaban shi sai dai bai sake taɓawa ba, dan fitsararshi ba ta kai ya buɗa kwanukan a gaban Alhaji Kabir ba, sun ci gaba da ɗan taɓa hira kafin Alhaji Kabir ɗin ya miƙe zai tafi, da sauri Ummu ta kalle shi sannan ta kalli Mama tace "Mama, ki mishi godiya fa, jiya ya kai ni naga sabon gidan da ya baku zaku koma, yanzu ma albishir ɗin n zo yi muku."

Da sauri Mama ta kalle ta, Luƙman da Mujittafa kuma farin ciki ne ya baibaye su suka shiga yi mishi godiya, ganin godiyar tayi yawa kuma ya gaya ma Ummu kar ta faɗa har sai ya tafi dan barin ta kafin ya dawo ya ɗauke ta yasa ya kamo hannun Luƙman ya ce ya raka shi, da ƙyar Mama ta buɗa baki ta mishi godiya saboda kukan da ya ci ƙarfin ta.

Saida suka fita Ummu ta matsa kusan Maman sosai tace "Mama, ki daina kuka mana, dama ya jima da gaya min yana nema muku gida matsakaici mai kyau, wallahi baki ga gidan ba ƙaramin mai kyau kuma duka a shafe yake da tiles, kuma Mama har da banɗaki a ɗakunan sannan ga wata a waje, gwanin sha'awa wallahi."

Kallon fuskar Ummu tayi, yarinyar dai da ta tsinta a tsumma tana ta kuka, ita iya girman ta ma ya isheta alfahari, amma gashi ta fara zuwa mata da abun alkairi irin wannan, shafa fuskar Ummu tayi cikin kuka tace" Allah ya miki albarka."

Da fara'a ta amsa da" Ameen Mama, nagode."

Mujittafa ma zumuɗin gidan ya dinga yi har Mama ta ƙara mishi abincin da Ummu ta kawo musamman da yake kiran a dai ƙaro mishi naman nan na zabuwa, dariya kawai suke yi har ya gama ya fita ya samu Alhaji da Luƙman ya shiga mamakin me suke tattaunawa haka a kai. Mama kua da ta watsa ma yarinyar ruwa ɗaki ta shiga ta ɗauko mata wando tare da jigidar da ta gyara ɗazu da yamma dan ta saka mata, tana saka ma yarinyar ganin bacci ne sosai a idanun ta yasa ta rumgume ta a ƙafafun ta, murmushi Ummu tayi ganin yarinyar fa ta kai shekara uku ko kusan huɗu ma, riƙo hannun yarinyar Ummu tayi tace "Ke ma ba zaki manta da Mama ba ko kuwa gobe za ki ga ahalin ki, nagartattun halayen Mama yasa ba ma iya mata butulci."

Sai kuma ta sake yin murmushi tace "Ya sunan ki?"

Cikin baccin da ya fara fizgar ta tace "Khaiyat (Khairat)."

Jigidar mai roba ta fara ƙoƙarin sakawa yarinyar, Ummu na ganin jigidar ta yi saurin riƙota tana cewa "Lahhhh! Mama, wannan jigidar fa mai kyau?"

Ita ma mama murmushi tayi tace "Wannan...?" Sai kuma tayi shiru na wasu sakanni, wannan ? Wannan jigidar? A ƙugun Ummu ta same ta tun tana jaririya, ta cire mata ita ne sanda ta girma duwatsun kuma suna warewa saboda ta musu girma, har ta mance da ita fa, la'ilaha illalah! Kallon Ummu tyi tace" Kina so?"

Da murmushi Ummu ta kalle ta tace" Tana da kyau Mama, dubi duwatsun fa, ni ban taɓa ganin irin su ba tun da nake, gasu da ɗaukar hankali kamar dai wasu na musamman da ba'a samu a ko ina."

Kallon tausayi Mama ta mata tace" To kinga, ki É—auketa kawai."

Kallon Maman tayi tace" A'a Mama, ba ta Khairat bace? Kuma ma ai b zata min ba."

Girgiza kai tayi tace" Ba Ta ta bace, ta jima sosai ina ɓoyeta, da a ƙugunki take girma yasa na cire miki ita, amma ki ɗauka tunda kina so."

Dariya tayi tace" Mama ai b zata min ba." Ƙin karɓar jigidar tayi tace" Ki samu wasu duwatsun masu kyau da zasu dace da waɗannan, Kinga sai ki samu wata robar da zata yi daidai da ƙugun ki kawai, shikenan fa."

Da farin ciki Ummu tace" E, kuma fa Mama kin kawo shawara."

Murmushi Maman tayi tana girgiza kai tace" Ummu kenan, ke dai ba'a rabaki da son jigida, idan ban yi ɓatan lissafi ba ina ga ɗaurin jigida goma sha uku ke a ƙugun ki, wai ke ko isar ki ma bata yi?"

Dariya Ummu tayi tana sunkuyar da kai dan Alhaji kullum shafa ƙugun ta yake yace tana birge shi abar nan, da sauri mama tace" Ba wannan ba, ya gidan naku? Komai dai lafiya ko?"

Ajiyar zuciya Ummu ta sauke ta kalle ta tace" Mama, gidan mu babu daɗi ta wata kusurwar, Alhaji mutumin kirki ne sosai, ba ruwan shi da damuwar duniya, yana min duk abinda nake so, kuma ya na maida kanshi ƙaramin yaro a gabana, hasalima Mama ya zama kamar abokin wasa a gare ni, sai dai mutanen gidan shi..."

Iska ta feso daga bakin ta sannan ta É—ora da" Hajia babba ita ce ke da hali irin na Alhaji, ba ta da matsala sannan tana da kirki, amma sauran matan da Æ´aÆ´ansu mata masu aure, duk tayasu kishi suke saboda wai na auri uban su, amma f Mama hatta babban É—anshi wanda yake da aure har da É—iya budurwa, wallahi kar ki so kiga yadda yake girmama ni ko da gaishe ni zaiyi, Æ´an mazan ba ruwan su su amma matan, Zeinab kaÉ—ai ke gaishe ni da girmamawa kuma har muke hira da ita, ko ma dai yaya ne Mama ni dai ina farin ciki da zamana da shi, bai tauye ni ta ko ina ba, dan haka ma bana shiga harkar su bayan gaisuwar mutumci."

Jinjina kai Mama tayi cike da tausayawa rayuwar Ummu, ita gaba ta fi hango mata wallahi, ta sani a shekarun ta yanzu da kuma na Alhaji dole wata rana za ta tawaya, to amma ta ga ita sam bata hango haka, hasalima yarinta ta sa bata wannan tunanin, dan haka ita ma bata so ta dinga mata irin wannan hirar, cike da rarrashi tace "Ki ci gaba da haƙuri kinji, kowace rayuwa dama da kika gani akwai ƙalubale a tare da ita, amma idan kika yi haƙuri komai zai zo ya zama tarihi."

Yadda Mama ta faɗa mata kuwa haka aka yi, dan tun a hanyar su ta komawa ta cika shi da shagwaɓa sai ya tsaya ta siyi duwatsu, tun yana dariya da cewa ta bari ta zo gobe ta siya har dai ya ga da gaske take, dole ya tsaya ta siya sannan suka wuce gida.

*******************

Kasancewar an shiga watan ruwa da babu ƙaƙƙautawa yasa tun jiya da safe ke ta ruwa kuma har yanzu da yamma tayi ana ta yayyafi, sanyin da gari ya ɗauka sosai yasa ciwon ƙafafun Hajia kakar ya tashi, ganin dai ba sauƙi kuma maganin ta y ƙare, dole Sa'ad ya fita tare da Aisha dan siyo mata maganin, a hanyar su ta dawowa bakin hanya inda babu nisa da gida ya tsaya wajen wankin mota yayi magana da ɗaya daga cikin yaran wurin kan zai kawo motar yanzu a wanke mishi, amma a jira ya kai Aisha gida, kallon shi tayi tace "Abbu, ka bayar mana yanzu, sai mu taka a ƙafa ai."

Kallonta yayi ta ƙasan idanu yace "Idan fa kika jiƙe d ruwa?"

Sadda kanta tayi tace "Babu komai ai, kuma ma yayyafi ne kaÉ—an."

Da wani irin narkakken kallo ya kalle ta yace "Kin tabbata?"

Ba tare data kalle shi ba ta jinjina kai alamar e, dan haka suka fita ya bar motar dan yana son fita anjima, a hankali suke tafe yayyafin nan na sauka jikin su, yanayin yayi kyau sosai inda sama tayi kalar shuɗi gwanin sha'awa, ledar maganin na hannun ta tana wasa da ita inda kanta ke ƙasa bata kallon ko ina sai ƙafafun ta, Sa'ad kuma dake satar Kallonta jefi-jefi ne yace "Kin taɓa riƙe waya taki?"

Ba tare data kalle shi ta girgiza kai cike da kunya tace "A'a."

Jinjina kai yayi ya kalli gabanshi yace "To saurayi fa?"

Da sauri ta kalle shi, yana juyowa ya kalle ta sai kunya ta sake rufeta ta rufe fuska da hijabi tana murmushi, wani basaraken murmushi ya saki yana girgiza kai yace "Ba zaki gaya ma Abbunki ba? Ko baki so muyi surukun taka ne?"

Cikin kukan shagwaɓa ta dinga bubbuga ƙafafu kamar zata tashi sama tana cewa "Abbu ka daina, ni bana da wani saurayi, ba ruwana da su."

Ajiyar zuciya ya sauke yana Kallonta yace "Saboda me? Naga ai kin isa aure ko?"

Kallon shi tayi tare da turo baki tace "To ai Mother bata barin mu kula maza kuma ba'a barin mu fita sakaka, ko waÉ—anda sukayi aure ma a gidan marayun duk mafi aksarin su auren haÉ—i ne ko kuma idan anyi katari ka fita wani muhimmin abu sai saurayin ya ganka ya kuma biyo ka."

Kallonta yayi yace" Da kyau, kenan ke baki taɓa irin fitar katarin ba da zata haɗaki da saurayi?"

Girgiza kai tayi a tausashe tace" Um um." Shiru sukayi na wasu daƙiƙu suka ci gaba da tafiya, suna daf da gida ya sake kallon ta yace" Me yafi miki daɗi?"

Kallon shi tayi da mamakin wannan tambayar, sai kawai ta kalli sama tana sauke numfashi tace" Kallon sama bayan É—auke ruwa, yanayi mai daÉ—in gaske."

Shiru suka sake yi, hakan yasa ta kalle shi ita ma tace" Kai kuma fa? Me ya fi birgeka?"

Saida ya ɗan cije leɓe yana jin kamar ya faɗi abinda ke ran shi, sai kawai yace" A da dai akwai abubuwa dayawa, a yanzu kuma *zama tare dake* ya fi min komai daɗi."

Cak! Ta tsaya tare da zuba mishi idanu tana kallo, kallon da take mishi ya ankarar da shi abinda ya faÉ—a, da sauri ya shiga gaba yana tafiya da cewa" Ba abinda kike tunani bane."

Ba Ta iya ɗaga ƙafafun ta ba har saida ya kusa shigewa gida sannan ta bi bayan shi jikin ta na sake yin sanyi da kuma tunanin abinda ya faɗa ɗin.

A zabure ta tsaya tana waigawa inda saurin ya fito, ganin shi tare da baƙo yasa ta tausasa murya tace "Ina kwana?"
Chapter 36 · 0% Book details