← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 168

Sashe 88

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad ko dake tambayar me ya faru Hajia ta masa shiru, à haukace ya nuna Fati da yatsa yace "Akan wannan ce ko? To bana so, bana son ta Hajia ku kai kasuwa idan ta rasa miji ne, amma ku sani ba ku kyauta min ba, ko me zaku mata ku mata ba sa'ilin da ni na gayyace ta gidan nan ba, amma hakan da kuka yi, ya sake nuna min nan ɗin ƙaramin gida ne."

A fusace ya juya zuwa ga Fati dake tsaye ta rasa abun yi, kamar zai cije ta yace" Ki fita a sabgata, ni bana son ki."

Ƙasa da sama ya kalle ta a hassale ya fita a gidan shima, Fati m'a da taji zafin maganar nan da gudu ta juya zuwa ɗakin Hajia da ta bar jakar ta a can dan ta bar musu gidan su, dan sai yanzu ne ta gano dalilin zuwan ta gidan nan.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*41*

Tana fita kamar wani tsari ta ci karo da taxi, dan haka ko da Fahad ya bi bayan ta bai gan ta ba, kuka take kamar ranta zai fita, kuka ne da ita dai a sanin da ta ma rayuwar ta bata taɓa yin irin shi ba, amma sai gashi yau tana yi dalilin wulaƙantata da aka yi, tsaf taxi ya kai hôtel ɗin ta ta sauka ta biya shi, har za ta shiga ciki sai ta tuna tabbas Fahad zai zo nan, ita kuma bata son sake haɗuwa da shi, dan haka da azamar ta kama wata hanyar daban duk da bata san ina za ta kai ta ba ga kuma magrib da aka fara kira.

A cikin tafiyar ta ta haɗu da wurin siyar da magani, cikin kukan nan har muryar ta ta shaƙe ta siyi magani na ruwa na tari har da na ciwon kai, garin neman canji da mutumin ke yi Nabila ta ɗauke kwalin sigari guda dan tana buƙata, kuma ta san tana cewa ya bata za'a dinga mata wani kallo, dan haka ta ce ya bata ashana guda ɗaya kafin ya bata canjin.

Tana tafiya daga nan duhu ya sake yi, a wani fili ta zauna bakin bishiya ba tare da tunanin komai ba ta buÉ—e kwalbar maganin nan ta kifa kan ta, saida ta shanye tas ta dafe kan ta saboda juya mata da yake yi, ba ta sha maganin ciwon kan ba sai sigari da ta sake bankawa wuta.

Komai dake faruwa a rayuwar mu da ma mafari gare shi, dalilin abun nan da ya faru Nabila bata iya tashi daga nan ba saboda ta bugu sosai har bacci ya ɗauke ta tamkar wacce aka zarewa rai. Inda Fahad ke can y a neman ta tare da kiran wayar ta da ke ƙara sannu sannu ba yadda za ta damu mutum ba. Matasan gari ne suka ga Nabila a wurin, daga post ɗin ta, zuwa ƴan kunnen ta na zibare da Fahad ya siya mata, har kan sarƙar ƙafar Ummu dake ƙafar ta da agogo, har takalmin ta da ranar sakawa na biyu ta musu masu kyau da tsada ne, haka suka yaye ta suka bar ta nan yashe ba ta san me ke faruwa ba.

*Dama* tunda Sabeer yayi aure Alhaji ya sa aka buɗa mishi ƙofar da za ta shigo da Sabeer ɗin ɓangaren su kai tsaye, da wannan ne kowace asuba Alhaji ya kan je ya tashi Sabeer, duk da mafi yawan lokutta yana samun su a farke, amma dake ya sba sai ya je ya tashe shi sai su je masallaci tare. Tun da safe jiya da abinda ya faru ya farun nan bai sake fita ko masallaci ba, hakan ya sa ma saida limamin masallacin ya leƙo da magrib dan duba ko lafiya, wanda ka saba gani yau kuma shiru ba labari, ya fita suka jima suna hira har isha'i kafin ya dawo, kuma lafiya lau suka kwanta da shi da fatan ganin safiya lafiya.

Sai dai komai mafari gare shi, Hajia ta gigice yadda ta kasa aiwatar da komai bayan ta fahimci da gawar Alhaji take kwance, jikin shi sanyi ƙalau yadda ta kasa bambamce tun da suka kwanta ne rai yayi halinsa? Ko kuma dai bayan dre ya raba ne ko kuma ma yanzu kusan asubar? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Kawai take maimaitawa a bakin ta, ta ƙi yin kuka kuma ta ƙi tashi daga nan kan gadon da take bare ta nemi ɗauki.

Sabeer na ta duba lokaci ya ga lokacin da Alhaji ke zuwa ya wuce bai zo ba, gashi ana daf da tayar da sallah, sai kawai shi ya fito ya kuma zo dan duba ko lafiya? Ya ƙwanƙwasa amma shiru Hajia ta kasa mishi magana, dan haka ya ji hankalin shi bai kwanta ba, to iyayen su biyu a ce ba wanda ya amsa idan lafiya? Turo ƙofar yayi a hankali yana ɗan zuro kai, Hajia da ya gani a yanayin da bai taɓa ganin ta ba ya sa ya kutso kai cikin ɗakin.

*Sun* tsinci kan su a tashin hankalin da ba su saka mishi rana ba, sun yi jimami da ƙoƙarin kwantarwa da mahaifiyarsu hankali wacce suka ga ta fi su shiga ɗimuwa. Suna wannan yanayin Fahad da bi kwana gidan ba ya shigo a hargitse, niyyar sa ita ce ya buɗe wuta kan abinda aka ma Nabila dan bai gan ta ba tun jiya, yarinyar mutane ta zo saboda shi, amma ya neme ta ya rasa? Sai dai ba wannan ba, mahaifin da ya haife shi ma ya shi duniyar ya bar musu baki ɗaya, ga dai shi kwance cikin farin yadin da ake lulluɓe tsoho da yaro, mace da namiji, mai kuɗi da kuma talaka, tunano abubuwan da suka faru tsakanin shi da mahaifin na shi, da yadda yake masa magana, da yadda ya bijire masa, irin ɓacin ran da ya dinga saka shi, sai ganin Fahad sukayi ƙasa ya suma saboda bala'in zafi da nauyi da kan shi ya ɗauka.

*Rigar kowa* (mutuwa), ta su Alhaji ta ƙare daga nan, mai kyau aka aikata ko akasin haka, wannan dukiyar da gida na alfarma, da Soyayyar nan ta iyali duk ya bar su a nan gidan duniya, inda aka ɗauke shi da aikin shi izuwa gida na haƙiƙa, iko, dukiya, taƙama da isa duk an bar wa *magada*. Allah ka sa mu cika da imani.

*******************

Halin da ta samu kan ta bayan farkawar ta daga baccin da bai da maraba da suma ya matuƙar sake ɗaga hankalin ta da dawo mata da damuwar ta sabuwa fil a leda, ba komai na jikin ta face doguwar rigar, dan kallabin ta ma iska ne ya fara kaɗashi har mai buƙata ya yi gaa da shi, ba komai, ba komai a tare da ita, ba kuɗin komawa gida, ba mana taxi bare ta kai ga komawa gida, kuma ba abun siyarwa. Ba wannan ne ya fi ɗaga mata hankali ba, yanzu da ace wanda suka yasheta ba kayan jikin ta kaɗai suka ɗauka ba, in da fa har da fyaɗe suka mata? A halin da take ba za ta iya hana su ba, da shikenan an ci banza kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wannan shi ya fi ɗaga mata hankali har ta durƙushe tana faɗin "Tirrr! Tirrr ! Nabila ba ki wa kanki adalci ba, wannan wace irin rayuwa ce? Shaye-shaye bai yi ba, Nabila kin cuci kan ki."

Sai kuma ta zabura ta tashi kamar mahaukaciya ta kama hanyar zuwa hôtel ɗin ta ɗauki ko da kayan ta ta kama hanyar komawa mahaifar ta.

Da ƙyar suka bar ta ta shiga dake sun san ta, amma yadda suka ga bata da ko takalmi sun ɗauka sabuwar kamu ce, haka ta tattaro kayan ta sannan ta canza kaya ta bar hôtel ɗin, dake safiya ce sosai ɗaya daga cikin ma'aikatan ya bata aron waya ta kira uwa maba da mama, uwar ta mai share kukan ta wato Ummu...

Ummu dake ta kai da kawo a tsakar ɗaki ta kasa zaune ta kasa tsaye tun jiya da ta sha abun da ya fi ƙarfin ta da ƙudirin ta samu kan Alhaji, amma ƙiri-ƙiri ya nuna mata ba fa kwanan ta bane, shi kuma ba zai yarda mata su kai shi wuta ba, har saida ta kai tana roƙon ya mata ko da wasa ne amma ya ce baya so su wuce gona da iri, haka ya fita ya bar ta ba tausayi bare tunanin halin da za ta shiga.
Chapter 88 · 0% Book details