Sashe 76
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ya kalli Uzeifatu dake zaune tana ta turo baki yace" Ke kuma ki ji da kyau, tunda ita ba zata saka ki aiki ba ni daga yau na É—ora miki sharar gidan nan da wanke wanke, kika bari na sake tarar da ke zaune da waya a hannun ki alhalin mahaifiyar ki na aiki, to sai na rarraba ki gida biyu."
A fusace ya fito daga farfajiyar ya iso soro, Jabir ya samu tsaye ya juya bayan shi kan shi na kallon ƙasa kamar wanda ya faɗa duniyar tunani, duk da bai gane wanene ba, dan haka ya rage saurin da yake yana kallon ƙeyar mutumin da mamakin wa ye har cikin tsakiyar soron gidan shi? Jabir da ya ji abinda ke faruwa, ya kuma fahimci inda matsalar take da kuma yadda za'ayi ma ayi maganin matsalar, jin tako a bayan shi ya kuma tabbatar na mahaifin sa ne yasa shi juyowa da sauri, suka kallon kallo ya tabbatar da mahaifin shi, inda shi ma Baban nashi ya shaida shi ne tun bai faɗa masa shi bane ta fuskar kama da ya gani da margayiya mahaifiyar Jabir ɗin, sai dai bai sani ba zama ne a cikin jajayen mutane yasa ya ma fi ta kyau nesa ba kusa ba? Wangale baki yayi har kunne irin ka ga abinda kake mararin ganin nan, da wani irin sauri ya tunkaro Jabir da shima yake sakin murmushi mai cike da bege da kewar mahaifi ya fara takawa, cikin zaƙuwa mahaifin nasa ke faɗin "Jabir, kai ne? Shine ka zo baka kirani ba?"
Rumgume juna sukayi ƙam ƙam, duk rashin tsayi irin na Jabir irin tsarin nan zololo sai gashi kai da kai da shi da mahaifin shi, dan shi ma ba mutumin tsayi bane sosai ɗin nan. Hawaye masu zafi ne suka sauka a kafaɗar mahaifin Jabir, hakan ya tabbatar masa da kuka yake yi, dan haka ya ɗago shi yana murmushi tamkar gonar audiga yace "Jabir, kuka kuma? Kai share hawaye mana, me yasa kake kuka yanzu? Ni ba ka ga dariya nake yi ba? Yi murmushi ka ji Jabir ɗina."
Tafin hannun shi ya sa ya share hawayen sannan ya kalli fuskar mahaifin shi, yana nan har yanzu da ƙarkon shi kamar ba shi ya haife shi, jikin shi a murɗe haka kuma kan shi ɗan tsili tsilin farin gashin kaɗan ido ke iya hangowa, irin wanda za'a ƙidaya din nan a kan mutum, riƙe hannayen juna suka yi gam inda a tausashe cikin muryar kuka da rauni Jabir yace "Aba, ka yafe min? Na wahalar da kai wajen nema na ko?"
Murmushi yayi yana jijjiga hannayen Jabir ɗin yace "Karka damu fa, tun ranar ai na gaya maka ni ban riƙe ka ba Jabir, idan da mai laifi ai ni ne, ni na takura na dinga azabtar da kai har saida ka bar gida, ka ga kenan ni zan baka..."
Da sauri ya girgiza mishi kan shi dake kallon ƙasa saboda ya fahimci haƙuri zai bashi yace "Shikenan Aba, nagode da ka yafe min..." Sai kuma ya ɗaga kai ya sake kallon fuskar shi sosai cikin nutsuwa yace "Aba kana lafiya?"
Murmushi ya sake mishi yace "Lafiya lau nake Jabir, kai ma haka?"
Jinjina kai yayi alamar e tare da sadda kan shi, shiru ne ya gifta na sakan biyu, a hankali Aba ya zare hannun shi na hagu daga cikin na Jabir, cikin nutsuwa ya tallabo haɓar shi yana kallon shi da so da ƙauna, a hankali kamar da wasa yake zagaya sajen da ya zagaye kumatu har zuwa kunnuwan Jabir, da wani kwantaccen gashi dake ƙasan bakin shi kaɗan, zuwa wanda ke zagaye da bakin shi na sama, da fara'a yake yin haka yna jin daɗi yana kuma kallon fuskar ta shi yace "Jabir ka girma, kamar ba kai ne ka gudu daga gare ni kana shekara sha huɗu ba."
Faffaɗan murmushi Jabir yayi ya sunkuyar da kai cike da kunya yace "Hakane Aba, yanzu ɗan ka shekarar shi ashirin da bakwai, sannan ya zama alaramma da zai iya ja wa kowane babban malami baƙi, sannan ya ƙara gogewa a fannin neman na halak ɗin shi, Aba..."
Ya kira sunan shi suna kallon juna, É—orawa yayi da "Zan iya neman kuÉ—i a duk inda suke, Aba ina bin kowace hanya dan neman na kaina, amma ban da haramtacciyar hanya, sannan kuma Aba bana raina samu ko ya yake, ba dan komai ba saboda bana so na ji yunwa, sannan na ga na taimaki mai neman taimako kamar yadda Abba ya taimake ni lokacin da nake kusa da faÉ—awa garari."
Cikin farin cikin jin haka Aba ya sake jawo Jabir jikin shi ya rumgume yana daddaɓa bayan shi tare da cewa" Ka kyauta Jabir, Allah ya maka albarka, Allah ƙara maka buɗi na alkairi, Allah baka ikon neman halak ɗin ka a duk inda take, Allah kuma ya sauƙaƙa maka neman ta."
Ƙwarai! Yanzu ne ya fahimci ya jima yana rayuwa cikin kuskure, duk abinda mahaifin shi yayi bai kamata yayi watsi da shi ba, tunda dai shi ya haife shi, wasu ma Allah azurtar su yake da iyayen da basa bautawa Allah, ko kuma masu yin shirka gare shi, amma su yi haƙuri su zauna da su, gashi yanzu daga yi masa addu'a ɗaya ya ji wani irin yaƙinin na cewa wannan addu'a karɓaɓɓiya ce kuma tafi tasiri fiye da ta Abba Kabir, dan kuwa da bambamci ai tsakanin su, wannan shi ya kawo shi duniyar, sannan ya wahala da shi tun yana jariri har ya kai ɗan sha huɗu. Yayin da daga nan Abba kuma ya ɗora har zuwa yanzu da ya zama cikakken mutum mai aƙida da riƙo da shari'a ta gari, kowanen su ya bada gudummawa a cikin rayuwar shi, dan haka iyayen sa ne dukansu.
Da sauri Jabir ya janye jikin shi saboda tunawa da su Aliyu yace "Aba, tare da su Aliyu muke?"
Da mamaki ya kalle shi yace "Kua ka baro su waje? Ba shine ka bani muka gaisa daren shekaran jiya ba da ka sake kirana?"
Murmushi yayi a tausashe yace "Shine Aba, na shigo ne dan na tabbatar ko nan É—in ne."
Da sauri Aban ya fita yana cewa "Bari na shigo da su sai ku wuce."
Yana fita ya same su suna ta hira, rusunawa sosai sukayi suka gaishe shi sannan ya musu iso, suna shigowa Jabir ya yi murmushi saboda harara da Aliyu ya mako mishi yana faÉ—in "Shikenan sai ka manta da mu, kamar Aban naka ne kai kaÉ—ai?"
Rusunawa Jabir yayi yace "Kayi haƙuri *babban Yaya*."
Murmushi kawai Aliyu yayi dan ya fahimci me yasa ya bashi haƙuri, ba ya so su yi rigima ne har ya ɓata mishi rai a yanzu, haka suka rankaya da sallama a bakunansu.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*37*
Bara'atu na yankar albarka na abincin dare da za ta ɗora wanda na daga cikin abinda ya kwo rigimar nan, dan saida ta yi abincin da ya ce ta yi na tarban Jabir, ganin la'asar tayi ba su zo ba ta ce ko ba sai tayi girki ba kawai dan dama ta gaji? Daga cewa ta sa Uzei tayi girkin daren mana take faɗin Uzei ce z ta iya aikin nan? Ina ba za ta saka ta ba, amsa sallamar tayi tana tsare masu shigowa da idanu, ya dai ce mata Jabir kawai zai zo, ta yi duk iya tunanin da za ta yi wajen gano daga ina zai zo? Da wane kalar rashin mutumci? Da wace kalar shigar? A ganin ta Uzeifatu ma da ake kulawa take gaban iyayen ta ta zama yadda ta zame musu, ina ga Jabir da ba mai kwaɓa? Ba uwa ba uba sai Allah (tunda kin yarda yana da Allah ai ya gama komai), so take ta ga wani da ƙananan kaya yayi irin asdown ɗin nan, da irin askin nan na gogaggun marasa tarbiyya, idan ma abun yayi daɗi har ta ga ɗan kunnai a kunnen shi da huje a hanci, a taƙaice dai ta ga Jabir a mummunan yanayi da shiga wacce ko a ƙasar waje sai fetsararru na ƙarshe ne ke irin ta.
Amma sai taga duka cikin su kowa shiga ce ta kamala, ba wai Jabir da Aliyu da suke cikin dogayen riguna ba, Khamis ma manyan kaya ne jikin shi, ɗinkin shadda ce da kuma hular shi a kai, tun daga nan ta ji zuciyar ta ta sake baƙan ta, ranta ya sosu ta ji ba daɗin da har saida ta taɓe baki ta ci gaba da aikin ta.